YouVersion Logo
Search Icon

Ish 7

7
Jawabi zuwa ga Sarki Ahaz
1 # 2Sar 16.5; 2Tar 28.5,6 Sa'ad da sarki Ahaz, ɗan Yotam, wato jikan Azariya yake mulkin Yahuza, sai yaƙi ya ɓarke. Rezin, Sarkin Suriya, da Feka ɗan Remaliya, Sarkin Isra'ila, suka fāɗa wa Urushalima da yaƙi, amma ba su iya cinta ba.
2Labari ya kai gun Sarkin Yahuza, cewa sojojin Suriya sun shiga ƙasar Isra'ila. Sai shi da dukan jama'arsa suka firgita ƙwarai, suna ta kaɗuwa kamar itatuwan da iska take kaɗawa.
3Ubangiji ya ce wa Ishaya, “Ka ɗauki ɗanka Sheyar-yashub ka je ka sami sarki Ahaz. Za ka same shi a hanya inda masu wankin tufafi suke aiki, a wajen ƙarshen wuriyar da yake kawo ruwa daga kududdufin da yake sama da ita. 4Faɗa masa ya zauna da shiri, ya natsu, kada ya ji tsoro ko ya damu. Fushin sarki Rezin da Suriyawansa da na sarki Feka ba wani abu mai hatsari ba ne, bai fi hayaƙin 'yan ƙirare biyu da suke cin wuta ba. 5Suriya tare da Isra'ila da sarkinta sun ƙulla maƙarƙashiya. 6Nufinsu su kai wa ƙasar Yahuza yaƙi, su tsoratar da jama'a, don su haɗa kai da su, sa'an nan su naɗa ɗan Tabeyel.
7“Amma ni Ubangiji na hurta, faufau wannan ba zai faru ba. 8Don me? Saboda Dimashƙu ita ce ƙarfin Suriya, sarki Rezin kuwa shi ne ƙarfin Dimashƙu. Isra'ila kuwa a shekara sittin da biyar masu zuwa za ta karkasu, har ba za ta iya rayuwa ta zama al'umma ba. 9Samariya ita ce ƙarfin Isra'ila, sarki Feka kuma shi ne ƙarfin Samariya.
“Idan bangaskiyarku ba ta da ƙarfi, to, ba za ku dawwama ba.”
Immanuwel
10Ubangiji ya aika wa Ahaz da wani jawabi, ya ce, 11“Ka roƙi Ubangiji Allahnka ya ba ka alama. Yana yiwuwa daga can zurfin lahira ne, ko kuma daga can cikin sama ne.”
12Ahaz ya amsa, ya ce, “Ba zan nemi wata alama ba. Ba zan jarraba Ubangiji ba.”
13Ga amsar da Ishaya ya ba Ahaz, “Kasa kunne yanzu, kai zuriyar sarki Dawuda. Ba abin kirki kuke yi ba, da kuka ƙure haƙurin jama'a, haƙurin Allah kuma kuke so ku ƙure? 14#Mat 1.23 Yanzu fa, Ubangiji kansa zai ba ku alama. Wata budurwa wadda take da ciki, za ta haifi ɗa, za a raɗa masa suna Immanuwel. 15In ya yi girma har ya isa yanke shawara don kansa, madara da zuma ne abincinsa. 16Kafin lokacin ya yi, ƙasashen sarakunan nan biyu waɗanda suka firgita ku za su zama kango.
17“Ubangiji zai aukar maka da kwanakin wahala, kai da jama'arka, da dukan iyalin gidan sarauta, waɗanda suka fi muni tun lokacin da aka raba mulkin Isra'ila daga na Yahuza. Zai kawo Sarkin Assuriya!
18“A lokacin nan, Ubangiji zai yi feɗuwa ya kirawo Masarawa su zo kamar ƙudaje daga manisantan mazaunan Kogin Nilu, ya kuma kirawo Assuriyawa su zo daga ƙasarsu kamar ƙudajen zuma. 19Za su zo jingim su mamaye kwazazzabai da kogwanni cikin duwatsu, za su rufe kowane fili mai ƙayayuwa da kowace makiyaya.
20“A lokacin nan, Ubangiji zai yi ijara da wanzami daga wancan hayi na Yufiretis, wato Sarkin Assuriya! Zai aske gyammanku, da gashin kawunanku, da na jikunanku.
21“A lokacin nan, ko da karsana ɗaya da awaki biyu kaɗai manomi yake da su, 22za su ba da isasshiyar madarar da za ta biya dukan bukatarsa. Hakika dukan waɗanda suka ragu a ƙasar za su sami yawan albarka su ƙoshi.
23“A lokacin nan, waɗannan kyawawan gonakin inabi waɗanda suke da kurangar inabi dubu, kuɗin kowace gonar inabi azurfa dubu guda ne, gonakin za su cika da ƙayayuwa da sarƙaƙƙiya. 24Ba wanda yake da ƙarfin hali da zai iya tafiya can, sai ko wanda yake da kwari da baka. Hakika ƙasar duka za ta cika da sarƙaƙƙiya da ƙayayuwa. 25Dukan tuddai inda dā akan shuka amfanin gona, za su cika da ƙayayuwa, har da ba mai iya zuwa wurin. Zai zama wurin kiwon shanu da tumaki.”

Currently Selected:

Ish 7: HAU

Highlight

Share

Copy

None

Want to have your highlights saved across all your devices? Sign up or sign in