YouVersion Logo
Search Icon

Ish 61

61
Albishirin Ceto ga Sihiyona
1 # Mat 11.5; Luk 7.22 # Luk 4.18,19 Ubangiji ya saukar mini da ikonsa.
Ya zaɓe ni, ya aike ni
Domin in kawo albishir mai daɗi ga talakawa,
In warkar da waɗanda suka karai a zuci,
In yi shelar kwance ɗaurarru,
Da kuma 'yanci ga waɗanda suke cikin kurkuku.
2 # Mat 5.4 Ya aike ni in yi shela,
Cewa lokaci ya yi
Da Ubangiji zai ceci mutanensa,
Ya kuma ci nasara a kan abokan gābansu.
Ya aike ni domin in ta'azantar da masu makoki,
3Domin in kawo wa masu makoki a Sihiyona
Farin ciki da murna maimakon baƙin ciki,
Waƙar yabo maimakon ɓacin rai.
Ubangiji kansa zai lura da su,
Za su ji daɗi kamar itace mai duhuwa.
Kowa da kowa zai aikata abin da yake daidai,
Za a yi yabon Allah saboda abin da ya yi.
4Za su sāke gina biranen da suke a rurrushe tun da daɗewa.
5Ya Urushalima, baƙi za su bauta miki,
Za su lura da garkunanki,
Za su nome gonakinki, su gyara gonakinki na inabi.
6Amma za a sani, ku firistoci ne na Ubangiji,
Za ku mori dukiyar al'ummai,
Za ku yi fāriya da cewa, taku ce.
7Kunyarku da shan wulakancinku za su ƙare.
Za ku zauna a ƙasarku,
Za a riɓanya dukiyarku,
Za ku yi ta farin ciki har abada.
8Ubangiji ya ce,
“Ina ƙaunar aikin gaskiya,
Amma ina ƙin zalunci da aikata laifi.
Da aminci zan ba mutanena lada,
In yi madawwamin alkawari, da su.
9Za su yi suna a cikin al'ummai,
Dukan wanda ya gan su zai sani,
Su ne mutanen da na sa wa albarka.”
10 # W.Yah 21.2 Urushalima tana murna saboda abin da Ubangiji ya yi.
Tana kama da amaryar da ta sha ado a ranar aurenta.
Allah ya suturce ta da ceto da nasara.
11Ba shakka, Ubangiji zai ceci jama'arsa,
Kamar yadda iri yakan tsiro ya yi girma.
Dukan al'ummai kuwa za su yi yabonsa.

Currently Selected:

Ish 61: HAU

Highlight

Share

Copy

None

Want to have your highlights saved across all your devices? Sign up or sign in