Ish 51
51
Maganar Ta'aziyya ga Sihiyona
1Ubangiji ya ce,
“Ku kasa kunne gare ni, ku da kuke so a cece ku,
Ku da kuka zo gare ni neman taimako.
Ku yi tunanin dutse inda kuka fito,
Da mahaƙar duwatsu inda kuka fito.
2Ku yi tunani a kan kakanku Ibrahim,
Da Saratu, wadda kuke zuriyarta.
Sa'ad da na kira Ibrahim ba shi da ɗa,
Amma na sa masa albarka, na ba shi 'ya'ya,
Na sa zuriyarsa suka yi yawa.
3“Zan ji juyayi a kan Sihiyona,
Da dukan masu zama a kufanta.
Ko da yake ƙasarta hamada ce, zan sa ta zama lambu,
Kamar lambun da na dasa a Aidan.
Murna da farin ciki za su kasance a can,
Da waƙoƙi na yabo da godiya zuwa gare ni.
4“Ku kasa kunne gare ni, ku mutanena,
Ku saurara ga abin da nake faɗa,
Na ba da koyarwata ga al'ummai,
Dokokina za su kawo musu haske.
5Zan zo da sauri in cece su,
Lokacina na nasara ya yi kusa.
Ni kaina zan yi mulki a kan al'ummai.
Manisantan ƙasashe za su jira ni in zo,
Za su jira da sa zuciya, ni in cece su.
6Ku duba sammai, ku duba duniya!
Sammai za su shuɗe kamar hayaƙi,
Duniya kuwa za ta yage kamar tsohuwar tufa,
Dukan mutanenta kuma za su mutu.
Amma ceton da zan kawo zai dawwama har abada,
Nasarata, ita ce za ta zama ta har abada.
7“Ku kasa kunne gare ni, ku da kuka san abin da yake daidai,
Ku da kuke riƙe da koyarwata a zuciyarku.
Kada ku ji tsoro sa'ad da mutane suke yi muku ba'a da zagi.
8Irin waɗannan mutane za su shuɗe kamar tufar da asu ya cinye!
Amma ceton da zan kawo zai dawwama har abada,
Nasarata za ta kasance har abada abadin.”
9Ya Ubangiji, ka tashi, ka taimake mu!
Ka nuna ikonka, ka cece mu,
Ka nuna ikonka kamar yadda ka yi a dā.
Kai ne ka daddatse dodon ruwa, wato Rahab.
10Kai ne ka sa teku ta ƙafe,
Ka kuma shirya hanya ta ruwa,
Domin waɗanda kake cetonsu su haye.
11Su waɗanda ka fansa
Za su kai Urushalima da farin ciki,
Da waƙa, da sowa ta murna.
Za su yi ta murna har abada,
Ba sauran baƙin ciki ko ɓacin zuciya har abada.
12Ubangiji ya ce,
“Ni ne wanda yake ƙarfafa ku.
Don me za ku ji tsoron mutum mai mutuwa,
Wanda bai fi ciyawa tsawon rai ba?
13Kuna mantawa da Ubangiji wanda ya halicce ku,
Wanda ya shimfiɗa sammai,
Ya kuma kafa harsashin ginin duniya?
Don me za ku yi ta jin tsoron fushin waɗanda suke zaluntarku,
Da waɗanda suke shiri su hallaka ku?
Fushinsu ba zai taɓa yi muku kome ba!
14'Yan sarƙa za su fita ba da jimawa ba
Za su yi tsawon rai,
Su kuma sami dukan abincin da suke bukata.
15“Ni ne Ubangiji Allahnku,
Na dama teku
Na sa raƙumanta suka yi ruri.
Sunana Ubangiji Mai Iko Dukka!
16Na shimfiɗa sammai,
Na kafa harsashin ginin duniya,
Na ce wa Sihiyona, ‘Ku jama'ata ne!
Na ba ku koyarwata,
Na kuwa kiyaye ku da ikona.’ ”
Ƙarshen Wahalar Urushalima
17 #
W.Yah 14.10; 16.19 Ya Urushalima, ki farka!
Ki tashi da kanki, ki miƙe!
Kika sha ƙoƙon hukunci wanda Ubangiji, cikin fushinsa, ya ba ki ki sha,
Kika shanye shi, ya kuwa sa ki yi tangaɗi!
18Ba wanda zai yi miki jagora,
Ba wani daga cikin mutanenki
Da zai kama hannunki.
19Masifa riɓi biyu ta auko miki,
Yaƙi ya lalatar da ƙasarki,
Mutanenki suka tagayyara da yunwa.
20A kan kusurwar kowane titi
Mutanenki sun rafke saboda rashin ƙarfi,
Sun zama kamar barewa da tarkon maharbi ya kama.
Suka ji ƙarfin fushin Allah.
21Ku mutanen Urushalima, masu shan wahala,
Ku da kuke tangaɗi kamar waɗanda suka bugu,
22Ubangiji Allahnku ya kāre ku ya ce,
“Ina ɗauke ƙoƙon da na ba ku cikin fushina.
Ba za ku ƙara shan ruwan inabin da zai sa ku yi tangaɗi ba.
23Zan ba da shi ga waɗanda suke zaluntarku,
Su waɗanda suka sa kuka kwanta a tituna
Suka tattake ku, sai ka ce kun zama ƙura.”
Currently Selected:
Ish 51: HAU
Highlight
Share
Copy
Want to have your highlights saved across all your devices? Sign up or sign in
@Bible Society of Nigeria 1979