1
Ish 51:12
Littafi Mai Tsarki
HAU
Ubangiji ya ce, “Ni ne wanda yake ƙarfafa ku. Don me za ku ji tsoron mutum mai mutuwa, Wanda bai fi ciyawa tsawon rai ba?
Compare
Explore Ish 51:12
2
Ish 51:16
Na shimfiɗa sammai, Na kafa harsashin ginin duniya, Na ce wa Sihiyona, ‘Ku jama'ata ne! Na ba ku koyarwata, Na kuwa kiyaye ku da ikona.’ ”
Explore Ish 51:16
3
Ish 51:7
“Ku kasa kunne gare ni, ku da kuka san abin da yake daidai, Ku da kuke riƙe da koyarwata a zuciyarku. Kada ku ji tsoro sa'ad da mutane suke yi muku ba'a da zagi.
Explore Ish 51:7
4
Ish 51:3
“Zan ji juyayi a kan Sihiyona, Da dukan masu zama a kufanta. Ko da yake ƙasarta hamada ce, zan sa ta zama lambu, Kamar lambun da na dasa a Aidan. Murna da farin ciki za su kasance a can, Da waƙoƙi na yabo da godiya zuwa gare ni.
Explore Ish 51:3
5
Ish 51:11
Su waɗanda ka fansa Za su kai Urushalima da farin ciki, Da waƙa, da sowa ta murna. Za su yi ta murna har abada, Ba sauran baƙin ciki ko ɓacin zuciya har abada.
Explore Ish 51:11
Home
Bible
Plans
Videos