YouVersion Logo
Search Icon

Ish 27

27
Ceton Isra'ila da Tarawarta
1 # Ayu 41.1; Zab 74.14; 104.26 A wannan rana Ubangiji zai yi amfani da takobinsa mai ƙarfi, mai muguwar ɓarna, don ya hukunta dodon ruwan nan mai kanannaɗewa, mai murɗewa, ya kashe dodon da yake cikin teku.
2A wannan rana Ubangiji zai yi magana a kan kyakkyawar gonar inabinsa, 3ya ce, “Ina tsaronta ina yi mata banruwa kowane lokaci, ina tsaronta dare da rana, don kada a yi mata ɓarna. 4Ba zan ƙara yin fushi da gonar inabin ba. Da ma a ce akwai ƙayayuwa da sarƙaƙƙiya in yi faɗa da su, da na ƙone su ƙurmus. 5Amma idan maƙiyan jama'ata suna so in cece su, sai su yi sulhu da ni, i, bari su yi sulhu da ni.”
6A wannan rana jama'ar Isra'ila, zuriyar Yakubu, za su yi saiwa kamar itace, za su yi toho, su yi fure. 'Ya'yan da suka yi za su cika duniya.
7Ubangiji bai hukunta Isra'ila da tsanani kamar yadda ya yi wa maƙiyanta ba, ba za su yi hasarar mutane da yawa ba. 8Ubangiji ya hukunta jama'arsa da ya sa aka kai su baƙuwar ƙasa. Ya sa iskar gabas mai ƙarfin gaske ta tafi da su. 9Ba za a gafarta zunuban Isra'ila ba, sai an niƙe duwatsun bagadan arna su zama kamar alli, har kuma ba sauran keɓaɓɓun ginshiƙai ko bagadan ƙona turare.
10Birni mai garu ya zama kufai. An bar shi kamar jejin da ba kowa ciki. Ya zama wurin kiwon shanu, inda za su huta su yi kiwo. 11Rassan itatuwa sun bushe sun kakkarye, mata kuwa sun tattara, don su riƙa hura wuta da su. Da yake jama'a ba su gane kome ba, Allah Mahaliccinsu ba zai ji tausayinsu ba, ba zai nuna musu jinƙai ba.
12A wannan rana Ubangiji kansa zai hukunta jama'arsa, Isra'ila, daga wannan iyakar ƙasa zuwa waccan, tun daga Yufiretis har zuwa iyakar Masar. Zai raba tsakanin nagari da mugu.
13A wannan rana za a busa ƙaho don a kirawo Isra'ilawan da suke zaman baƙunci a Assuriya da Masar. Za su zo su yi wa Ubangiji sujada a Urushalima a tsattsarkan dutsensa.

Currently Selected:

Ish 27: HAU

Highlight

Share

Copy

None

Want to have your highlights saved across all your devices? Sign up or sign in