Ish 25
25
Waƙar Yabo saboda Alherin Ubangiji
1Ya Ubangiji, kai ne Allahna, Zan ɗaukaka ka, in yabi sunanka.
Ka aikata al'amura masu banmamaki,
Ka tafiyar da su da aminci,
Wato bisa ga shirin da ka yi tuntuni.
2Ka mai da birane kufai
Ka lalatar da kagaransu,
Wuraren da maƙiya suka gina kuwa,
An shafe su har abada.
3Jama'ar al'ummai masu iko za su yabe ka,
Za a ji tsoronka a biranen mugayen al'ummai.
4Matalauta da 'yan ƙaƙa naka yi sun sheƙa zuwa wurinka,
Sun sami zaman lafiya a lokatan wahala.
Ka ba su mafaka daga hadura,
Ka inuwantar da su daga matsanancin zafi.
Mugaye sukan tasar musu kamar hadirin ƙanƙara,
5Kamar fari a ƙeƙasasshiyar ƙasa.
Amma kai, ya Ubangiji, ka rufe bakin abokan gābanmu,
Ka sa hayaniyar mugaye ta yi tsit,
Kamar yadda girgije yake sanyaya zafin rana.
Allah Ya Shirya Biki
6A kan Dutsen Sihiyona Ubangiji Mai Runduna zai shirya wa dukan sauran al'umman duniya biki da abinci irin na adaras da ruwan inabi mafi kyau. 7A can ne zai kawar da baƙin cikin da ya lulluɓe dukan sauran al'umma. 8#1Kor 15.54; W.Yah 7.17; 21.4 Ubangiji zai hallaka mutuwa har abada! Zai share hawaye daga idanun kowane mutum, ya kawar da kunyar da jama'arsa suke sha a duniya duka. Ubangiji ne da kansa ya faɗa!
9Sa'ad da wannan ya faru, kowa zai ce, “Shi Allahnmu ne! Mun dogara gare shi, ya kuwa cece mu. Shi ne Ubangiji. Mun dogara gare shi, yanzu kuwa muna da farin ciki domin ya cece mu!”
10 #
Ish 15.1—16.14; Irm 48.1-47; Eze 25.8-11; Amos 2.1-3; Zaf 2.8-11 Ubangiji zai kiyaye Dutsen Sihiyona, amma za a tattake jama'ar Mowab a ƙasa, kamar yadda ake tattake tattaka cikin taki. 11Za su miƙa hannuwansu kamar suna ƙoƙarin yin ninƙaya, amma girmankansu zai jā hannuwansu ƙasa a duk sa'ad da suka ɗaga. 12Allah zai lalatar da kagaran Mowab da dogayen garukansu, ya rushe su ƙasa su zama ƙura.
Currently Selected:
Ish 25: HAU
Highlight
Share
Copy
Want to have your highlights saved across all your devices? Sign up or sign in
@Bible Society of Nigeria 1979