YouVersion Logo
Search Icon

Ish 12

12
Waƙar Godiya
1Rana tana zuwa sa'ad da jama'a za su raira waƙa, su ce,
“Ina yabonka ya Ubangiji! A dā ka yi fushi da ni,
Amma yanzu kana yi mini ta'aziyya, ba za ka ƙara yin fushi da ni ba.
2 # Fit 15.2; Zab 118.14 Allah ne Mai Cetona,
Zan dogara gare shi, ba zan ji tsoro ba.
Ubangiji ne yake ba ni iko da ƙarfi,
Shi ne Mai Cetona.”
3Kamar yadda ruwan daɗi yake sa mai jin ƙishirwa farin ciki,
Haka nan jama'ar Allah suke farin ciki sa'ad da ya cece su.
4A wannan rana jama'a za su raira waƙa, su ce,
“Ku yi wa Ubangiji godiya! Ku nemi taimako a gare shi!
Ku faɗa wa dukan sauran al'umma abin da ya aikata!
Ku faɗa musu irin girman da yake da shi!
5Ku raira waƙa ga Ubangiji, saboda manyan ayyuka da ya aikata.
Bari dukan duniya ta ji labarin.
6Bari dukan waɗanda suke zaune a Sihiyona su yi sowa su raira waƙa!
Gama Mai Tsarki, Allah na Isra'ila, mai girma ne,
Yana zaune tare da mutanensa.”

Currently Selected:

Ish 12: HAU

Highlight

Share

Copy

None

Want to have your highlights saved across all your devices? Sign up or sign in