1
Ish 12:2
Littafi Mai Tsarki
HAU
Allah ne Mai Cetona, Zan dogara gare shi, ba zan ji tsoro ba. Ubangiji ne yake ba ni iko da ƙarfi, Shi ne Mai Cetona.”
Compare
Explore Ish 12:2
2
Ish 12:3
Kamar yadda ruwan daɗi yake sa mai jin ƙishirwa farin ciki, Haka nan jama'ar Allah suke farin ciki sa'ad da ya cece su.
Explore Ish 12:3
3
Ish 12:5
Ku raira waƙa ga Ubangiji, saboda manyan ayyuka da ya aikata. Bari dukan duniya ta ji labarin.
Explore Ish 12:5
4
Ish 12:4
A wannan rana jama'a za su raira waƙa, su ce, “Ku yi wa Ubangiji godiya! Ku nemi taimako a gare shi! Ku faɗa wa dukan sauran al'umma abin da ya aikata! Ku faɗa musu irin girman da yake da shi!
Explore Ish 12:4
5
Ish 12:1
Rana tana zuwa sa'ad da jama'a za su raira waƙa, su ce, “Ina yabonka ya Ubangiji! A dā ka yi fushi da ni, Amma yanzu kana yi mini ta'aziyya, ba za ka ƙara yin fushi da ni ba.
Explore Ish 12:1
6
Ish 12:6
Bari dukan waɗanda suke zaune a Sihiyona su yi sowa su raira waƙa! Gama Mai Tsarki, Allah na Isra'ila, mai girma ne, Yana zaune tare da mutanensa.”
Explore Ish 12:6
Home
Bible
Plans
Videos