YouVersion Logo
Search Icon

Gal 5

5
Ku Dāge a Cikin 'Yanci
1Almasihu ya 'yanta mu, 'yantawar gaske. Don haka sai ku dāge, kada ku sāke sarƙafewa a cikin ƙangin bauta.
2To, ni Bulus, ina gaya muku, in kuna yarda a yi muku kaciya, Almasihu ba zai amfane ku kome ba ke nan. 3Ina sāke tabbatar wa duk wanda ya yarda a yi masa kaciya, cewa wajibi ne ya bi dukkan Shari'a. 4Ku da kuke neman kuɓuta ga Allah ta wurin bin Shari'a, kun katse daga Almasihu ke nan, kun noƙe daga alherin Allah. 5Gama mu, ta wurin ikon Ruhu, muke ɗokin cikar begen nan namu na samun adalcin Allah saboda bangaskiya. 6In muna a cikin Almasihu Yesu, kaciya da rashin kaciya ba a bakin kome suke ba. Bangaskiya mai aikata ƙauna ita ce wani abu.
7Dā, ai, kuna ci gaba sosai. Wane ne ya hana ku bin gaskiya? 8Wannan rarrashin da ake muku ba daga wanda ya kira ku ba ne. 9#1Kor 5.6 Ai, ɗan yisti kaɗan, yake game dukkan curin gurasa. 10Na dai amince da ku a cikin Ubangiji, ba za ku bi wani ra'ayi dabam da nawa ba. Wannan da yake ta da hankalinku kuwa zai sha hukunci, ko shi wane ne. 11Amma 'yan'uwa, in da har yanzu wa'azin yin kaciya nake yi, to, don me har yanzu ake tsananta mini? In da haka ne, ashe, an kawar da hamayyar da gicciyen Almasihu yake sawa ke nan! 12Da ma a ce masu ta da hankalinku ɗin nan su mai da kansu babanni!
13Ya ku 'yan'uwa, don 'yanci musamman aka kira ku, amma kada ku mai da 'yancin nan naku hujjar biye wa halin mutuntaka, sai dai ku bauta wa juna da ƙauna. 14#L.Fir 19.18 Don duk Shari'a an ƙunshe ta ne a kalma guda, wato, “Ka ƙaunaci maƙwabcinka kamar kanka.” 15Amma in kuna cin naman juna, ku mai da hankali fa, hanyar hallaka juna ke nan.
Albarkar Ruhu da Halin Mutuntaka
16Maganata ita ce, ku yi zaman Ruhu, ba kuwa za ku biye wa halin mutuntaka ba. 17#Rom 7.15-23 Don halin mutuntaka gāba yake yi da Ruhu, Ruhu kuma yana gāba da halin mutuntaka. Waɗannan biyu gāba suke yi da juna, har ba kwa iya yin abin da kuke so. 18In Ruhu ne yake bi da ku, ashe, Shari'a ba ta da iko da ku, ke nan.
19Aikin halin mutuntaka a fili yake, wato, fasikanci, da aikin lalata, da fajirci, 20da bautar gumaka, da sihiri, da gāba, da jayayya, da kishi, da fushi, da sonkai, da tsaguwa, da hamayya, 21da hassada, da buguwa, da shashanci, da kuma sauran irinsu. Ina faɗakar da ku kamar yadda na faɗakar da ku a dā, cewa masu yin irin waɗannan abubuwa, ba za su sami gādo a Mulkin Allah ba.
22Albarkar Ruhu kuwa ita ce ƙauna, da farin ciki, da salama, da haƙuri, da kirki, da nagarta, da aminci, 23da tawali'u da kuma kamunkai. Masu yin irin waɗannan abubuwa, ba dama shari'a ta kama su. 24Waɗanda kuwa suke su na Almasihu Yesu ne, sun gicciye halin mutuntaka da mugayen sha'awace-sha'awace iri iri.
25In dai rayuwar tamu ta Ruhu ce, to, sai mu tafiyar da al'amuranmu ta wurin ikon Ruhu. 26Kada mu zama masu homa, muna tsokanar juna, muna yi wa juna hassada.

Currently Selected:

Gal 5: HAU

Highlight

Share

Copy

None

Want to have your highlights saved across all your devices? Sign up or sign in