YouVersion Logo
Search Icon

Gal 4

4
1Ana nufin, magaji, muddin yana yaro bai fi bawa ba, ko da yake yana da mallakar dukkan kome. 2A hannun iyayen goyo da wakilai yake har zuwa ranar da mahaifinsa ya sa. 3Haka yake a gare mu, wato sa'ad da muke kamar yara, a cikin ƙangin bautar al'adun duniya muke. 4Amma da lokaci ya yi sosai, sai Allah ya aiko Ɗansa, haifaffen mace, haifaffe kuma a ƙarƙashin Shari'a, 5#Rom 8.15-17 domin ya fanso waɗanda suke a ƙarƙashin Shari'a, a mai da mu a matsayin 'ya'yan Allah. 6Tun da yake ku 'ya'ya ne, sai Allah ya aiko da Ruhun Ɗansa a cikin zukatanmu, yana kira, “Ya Abba! Uba!” 7Don haka, kai ba bawa ba ne kuma, amma ɗa ne. Da yake ɗa ne kuma, to, magāji ne bisa ga ikon Allah.
Alhinin Bulus a kan Masu Bangaskiya
8Dā da ba ku san Allah ba, kuna bauta wa waɗansu gumaka, waɗanda ga ainihi ba a bakin kome suke ba. 9Amma a yanzu da kuka san Allah, ko ma dai a ce Allah ya san ku, ta yaya za ku sāke komawa a kan raunanan al'adu marasa biyan bukata, har kuna neman komawa ga bautarsu? 10Ga shi, al'adun ranaku, da na watanni, da na lokatai, da na shekaru ba sa wuce ku! 11Amma kun ba ni tsoro, kada ya zamana na yi wahala a kanku a banza!
12Ina roƙonku, ya ku 'yan'uwana, ku zama kamar yadda nake, domin ni ma in zama kamar yadda kuke. Ba ku taɓa yi mini wani laifi ba. 13Kun dai sani a dalilin rashin lafiyata ne na yi muku bishara a zuwana na fari. 14Ko da yake rashin lafiyata ta hana ku sukuni, duk da haka ba ku nuna mini raini ko ƙyama ba, sai dai kuka yi na'am da ni kamar wani mala'ikan Allah, ko ma Almasihu Yesu kansa. 15To, ina daɗin nan da kuka ji a game da ni? Don na shaide ku a kan lalle da mai yiwuwa ne da kun ƙwaƙule idanunku kun ba ni! 16Ashe, wato na zama abokin gābarku ne don na gaya muku gaskiya? 17Waɗannan suna habahaba da ku, amma ba da kyakkyawar niyya ba. Niyyarsu su raba ku da mu, don su ma ku yi habahaba da su. 18Ai, in da kyakkyawar niyya, abu ne mai kyau koyaushe a yi habahaba da mutum, ba sai ina tare da ku kaɗai ba. 19Ya ku 'ya'yana ƙanana, ina sāke shan wahalar naƙudarku, har Almasihu ya siffatu a zuciyarku! 20Da ma a ce ina tare da ku a yanzu in sauya muryata! Gama na ruɗe a kan sha'aninku.
Ishara da Hajaratu da Saratu
21Ku gaya mini, ku da kuke son Shari'a ta yi iko da ku, ba kwa sauraron Sharia ne? 22#Far 16.15; Far 21.2 Domin a rubuce yake, Ibrahim yana da 'ya'ya biyu maza, ɗaya ɗan kuyanga, ɗaya kuma ɗan 'ya. 23Ɗan kuyangar nan, an haife shi ne bisa ga ɗabi'a, ɗan 'yar kuwa ta cikar alkawarin ne. 24Wannan kuwa duk don ishara ne, wato matan nan a kan alkawari biyu suke. Ɗaya tushensa Dutsen Sina'i, mai haihuwar bayi, wato Hajaratu ke nan. 25To, ai, Hajaratu Dutsen Sina'i ce a ƙasar Larabawa. Ita ce kwatancin Urushalima ta yanzu, don ita da 'ya'yanta duk a bauta suke. 26Amma Urushalima ta sama, ai 'ya ce, ita ce kuma uwarmu. 27#Ish 54.1 Domin a rubuce yake cewa,
“ki yi farin ciki, ya ke bakarariya da ba kya haihuwa,
Ki ɗauki sowa, ke da ba kya naƙuda,
Don yasasshiya ta fi mai miji yawan 'ya'ya.”
28To, 'yan'uwa, mu ma 'ya'yan alkawari ne kamar Ishaku. 29#Far 21.9 Kamar yadda dā, shi da aka haifa bisa ga ɗabi'a ya tsananta wa wanda aka haifa bisa ga ikon Ruhun, haka a yanzu ma yake. 30#Far 21.10 Amma me Nassin ya ce? “Ka kori kuyangar da ɗanta, don ko kaɗan ɗan kuyangar ba zai ci gādo tare da ɗan 'ya ba.” 31Saboda haka 'yan'uwa, mu ba 'ya'yan kuyanga ba ne, na 'ya ne.

Currently Selected:

Gal 4: HAU

Highlight

Share

Copy

None

Want to have your highlights saved across all your devices? Sign up or sign in