Ezra 2
2
Yawan Kamammu da suka Komo.
(Neh 7.4-73)
1Waɗannan su ne mutanen da suka bar lardin Babila suka komo Urushalima da Yahuza daga bautar talala da Nebukadnezzar, Sarkin Babila, ya kai su Babila. Kowa ya koma garinsu. 2Sun komo tare da Zarubabel, da Yeshuwa, da Nehemiya, da Seriya, da Re'elaya, da Mordekai, da Bilshan, Misfar, da Bigwai, da Rehun, da Ba'ana.
Ga jerin iyalan Isra'ila, da yawan waɗanda suka komo na kowane iyali daga zaman talala.
3-20Zuriyar Farosh, mutum dubu biyu da ɗari da saba'in da biyu (2,172)
Zuriyar Shefatiya, mutum ɗari uku da saba'in da biyu
Zuriyar Ara, mutum ɗari bakwai da saba'in da biyar
Zuriyar Fahat-mowab na zuriyar Yeshuwa da Yowab, mutum dubu biyu da ɗari takwas da goma sha biyu (2,812)
Zuriyar Elam, mutum dubu da ɗari biyu da hamsin da huɗu (1,254)
Zuriyar Zattu, mutum ɗari tara da arba'in da biyar
Zuriyar Zakkai, mutum ɗari bakwai da sittin
Zuriyar Bani, mutum ɗari shida da arba'in da biyu
Zuriyar Bebai, mutum ɗari shida da ashirin da uku
Zuriyar Azgad, mutum dubu da ɗari biyu da ashirin da biyu (1,222)
Zuriyar Adonikam, mutum ɗari shida da sittin da shida
Zuriyar Bigwai, mutum dubu biyu da hamsin da shida (2,056)
Zuriyar Adin, mutum ɗari huɗu da hamsin da huɗu
Zuriyar Ater na Hezekiya, mutum tasa'in da takwas
Zuriyar Bezai, mutum ɗari uku da ashirin da uku
Zuriyar Yora, mutum ɗari da goma sha biyu
Zuriyar Hashum, mutum ɗari biyu da ashirin da uku
Zuriyar Gibeyon, mutum tasa'in da biyar.
21-35Mutanen da suke a garuruwan nan, su ma suka komo.
Mutanen Baitalami, mutum ɗari da ashirin da uku
Mutanen Netofa, mutum hamsin da shida
Mutanen Anatot, mutum ɗari da ashirin da takwas
Zuriyar Azmawet, mutum arba'in da biyu
Zuriyar Kiriyat-yeyarim, da Kefira, da Biyerot, mutum ɗari bakwai da arba'in da uku
Zuriyar Rama da Geba, mutum ɗari shida da ashirin da ɗaya
Mutanen Mikmash, mutum ɗari da ashirin da biyu
Mutanen Betel da Ai, mutum ɗari biyu da ashirin da uku
Zuriyar Nebo, mutum hamsin da biyu
Zuriyar Magbish, mutum ɗari da hamsin da shida
Zuriyar wancan Elam, mutum dubu da ɗari biyu da hamsin da huɗu (1,254)
Zuriyar Harim, mutum ɗari uku da ashirin
Zuriyar Lod, da Hadid, da Ono, mutum ɗari bakwai da ashirin da biyar
Mutanen Yariko, mutum ɗari uku da arba'in da biyar
Zuriyar Senaya, mutum dubu uku da ɗari shida da talatin (3,630).
36-39Ga kuma lissafin iyalan firistocin da suka komo,
Zuriyar Yedaiya na gidan Yeshuwa, mutum ɗari da saba'in da uku
Zuriyar Immer, mutum dubu da hamsin da biyu (1,052)
Zuriyar Fashur, mutum dubu da ɗari biyu da arba'in da bakwai (1,247).
Zuriyar Harim, mutum dubu da goma sha bakwai (1,017).
40Lawiyawa na zuriyar Yeshuwa da Kadmiyel na Hodawiya mutum saba'in da huɗu.
41Mawaƙa na zuriyar Asaf, mutum ɗari da ashirin da takwas.
42Zuriyar Shallum, da ta Ater, da ta Talmon, da ta Akkub, da ta Hatita, da ta Shobai, su ne zuriyar matsaran ƙofa, yawan mutanensu duka ɗari da talatin da tara.
43-54Ga lissafin ma'aikatan Haikali da suka komo.
Zuriyar Ziha, da zuriyar Hasufa, da zuriyar Tabbawot
Zuriyar Keros, da zuriyar Siyaha, da zuriyar Fadon
Zuriyar Lebana, da zuriyar Hagaba, da zuriyar Akkub
Zuriyar Hagab, da zuriyar Shamlai, da zuriyar Hanan
Zuriyar Giddel, da zuriyar Gahar, da zuriyar Rewaiya
Zuriyar Rezin, da zuriyar Nekoda, da zuriyar Gazam
Zuriyar Ussa, da zuriyar Faseya, da zuriyar Besai
Zuriyar Asna, da Me'uniyawa, da Nefushiyawa
Zuriyar Bakbuk, da zuriyar Hakufa da zuriyar Harhur
Zuriyar Bazlut, da zuriyar Mehida, da zuriyar Harsha
Zuriyar Barkos, da zuriyar Sisera, da zuriyar Tema
Zuriyar Neziya, da zuriyar Hatifa.
55-57Zuriyar barorin Sulemanu, su ne
Zuriyar Sotai, da zuriyar Hassoferet, da zuriyar Feruda
Zuriyar Yawala, da zuriyar Darkon, da zuriyar Giddel
Zuriyar Shefatiya, da zuriyar Hattil, da zuriyar Fokeret-hazzebayim, da zuriyar Ami.
58Dukan zuriyar ma'aikatan Haikali da zuriyar barorin Sulemanu su ɗari uku da tasa'in da biyu ne.
59Waɗannan su ne waɗanda suka zo daga Tel-mela, da Tel-harsha, da Kerub, da Addan, da Immer, amma ba su iya tabbatar da gidajen kakanninsu da asalinsu ba, ko su na Isra'ila ne. 60Su ne zuriyar Delaiya, da zuriyar Tobiya, da zuriyar Nekoda. Su ɗari shida da hamsin da biyu ne.
61Sai kuma zuriyar firistoci, wato zuriyar Habaya, da zuriyar Hakkoz, da zuriyar Barzillai, wanda ya auri mata daga cikin 'ya'yan Barzillai, mata, mutumin Gileyad, aka kira shi da sunnansu, 62suka bincika littafin asalin kakanninsu, amma suka ga ba su a ciki. Don haka aka mai da su ƙazantattu, ba a yarda musu su yi aikin firist ba. 63#L.Ƙid 27.21 Sai mai mulki ya ce ba za su ci abinci mafi tsarki ba, sai firist ya shawarci Urim da Tummim tukuna, wato kamar kuri'a ke nan.
64-67Yawan taron jama'a su dubu arba'in da biyu da ɗari uku da sittin (42,360).
Barorinsu maza da mata, dubu bakwai da ɗari uku da talatin da bakwai (7,337)
Mawaƙa ɗari biyu mata da maza
Dawakansu ɗari bakwai da talatin da shida
Alfadaransu ɗari biyu da arba'in da biyar
Raƙumansu kuma ɗari huɗu da talatin da biyar ne
Jakunansu kuwa dubu shida da ɗari bakwai da ashirin (6,720).
68Waɗansu shugabannin gidajen kakanninsu, sa'ad da suka isa Haikalin Ubangiji a Urushalima, sai suka bayar da kyautai da yardar rai don a sāke gina Haikalin Ubangiji a wurin da yake dā. 69Gwargwadon arzikinsu suka ba da darik dubu sittin da dubu ɗaya (61,000) na zinariya, da maina dubu biyar (5,000) na azurfa, da tufafin firistoci guda ɗari.
70 #
1Tar 9.2; Neh 11.3 Firistoci, da Lawiyawa, da waɗansu mutanen da suke zaune a Urushalima da kewayenta, da mawaƙa, da masu tsaron ƙofofi, da ma'aikatan Haikalin, da dukan mutanen Isra'ila suka zauna a garuruwansu.
Currently Selected:
Ezra 2: HAU
Highlight
Share
Compare
Copy
Want to have your highlights saved across all your devices? Sign up or sign in
@Bible Society of Nigeria 1979