Waɗansu shugabannin gidajen kakanninsu, sa'ad da suka isa Haikalin Ubangiji a Urushalima, sai suka bayar da kyautai da yardar rai don a sāke gina Haikalin Ubangiji a wurin da yake dā. Gwargwadon arzikinsu suka ba da darik dubu sittin da dubu ɗaya (61,000) na zinariya, da maina dubu biyar (5,000) na azurfa, da tufafin firistoci guda ɗari.