Eze 7
7
MatuÆa ta Yi
1Ubangiji ya yi magana da ni, ya ce, 2âYa kai, Éan mutum, ni Ubangiji Allah, na ce wa Æasar Isra'ila, matuÆa ta yi a kan kusurwa huÉu na Æasar!
3âYanzu matuÆarki ta yi. Zan fashe fushina a kanki, zan kuma shara'anta ki bisa ga ayyukanki, in hukunta ki saboda dukan Æazantarki. 4Ba zan yafe miki ba, ba kuwa zan ji tausayinki ba, amma zan hukunta ki saboda ayyukanki sa'ad da kike tsakiyar aikata Æazantarki. Sa'an nan za ki sani ni ne Ubangiji.â
5Ubangiji Allah ya ce, âMasifa a kan masifa, ga shi, tana zuwa! 6MatuÆa ta yi, ta farka a kanki, ga shi, ta yi! 7Æaddararku ta auko muku, ya ku mazaunan Æasar. Lokaci ya yi, rana ta gabato, ranar tunzuri, ba ta murna da ta sowa a kan duwatsu ba.
8âYanzu, ba da jimawa ba, zan fashe hasalata a kanku, in aukar da fushina a kanku, in hukunta ku bisa ga ayyukanku. Zan hukunta ku saboda dukan Æazantarku. 9Ba zan yafe ba, ba kuwa zan ji tausayi ba, amma zan hukunta ku bisa ga ayyukanku sa'ad da kuke tsakiyar aikata Æazantarku, sa'an nan za ku sani ni ne Ubangiji wanda yake hukunta ku.
10âGa rana ta zo. Æaddararku ta zo, rashin gaskiya ta yi fure, girmankai kuma ya yi toho. 11Hargitsi ya habaka, ya zama sandan mugunta. Ba wanda zai ragu cikinsu, ko yawaitarsu, ko dukiyarsu, ko wani muhimmi a cikinsu.
12âLokaci ya yi, ranar ta gabato, kada mai saye ya yi farin ciki, kada kuma mai sayarwa ya yi baÆin ciki, gama fushina yana kan taron jama'a duka. 13Mai sayarwa ba zai ta da ciniki ba sa'ad da suke da rai, gama fushina yana bisa kan dukan taron jama'arsu, ba zai fasa ba. Ba wanda yake zamansa cikin zunubi da zai iya shiryar da kansa.â
Hukunci a kan Zunuban Isra'ila
14âSun busa Æaho, sun gama shiri duka, amma ba wanda ya tafi yaÆi, gama fushina yana kan dukan taron jama'a. 15Takobi yana zare a waje, annoba da yunwa suna ciki. Wanda yake waje takobi zai kashe shi, wanda kuma yake ciki annoba da yunwa za su kashe shi. 16Idan akwai waÉanda suka tsere, za a same su a kan duwatsu kamar kurciyoyin kwaruruka, suna baÆin ciki dukansu, kowa yana baÆin ciki saboda laifinsa. 17Dukan hannuwa sun raunana, dukan gwiyoyi kuma sun zama marasa Æarfi kamar ruwa. 18Sun sa tufafin makoki, razana ta kama su, fuskokinsu kuma suna cike da kunya, akwai sanÆo a kawunansu. 19Sun watsar da azurfarsu a titi, zinariyarsu kuma ta zama kamar Æazantacciyar aba. Azurfarsu da zinariyarsu ba za su iya cetonsu ba, a ranar fushin Ubangiji. Ba za su iya Æosar da su ba, gama su ne sanadin tuntuÉensu. 20Suna fariyar banza da kyawawan kayan adonsu, na zinariya da azurfa. Da su suka yi siffofi masu banÆyama, da Æazantattun abubuwa. Domin haka zan maishe su Æazantattun abubuwa a gare su.
21âZan ba da su ganima ga baÆi, da kwaso ga mugayen mutanen Æasar. Za su lalatar da su. 22Zan kuwa juya daga gare su. Zan bar su su Æazantar da Haikalina. Mafasa za su shiga su Æazantar da shi.
23âSai ka Æera surÆa, gama Æasar tana cike da alhakin jini, birnin kuma yana cike da hargitsi. 24Zan kawo al'ummai masu muguntar gaske su mallaki gidajensu. Zan sa fariyar masu Æarfi ta Æare. Za a Æazantar da masujadansu. 25Sa'ad da wahala ta zo, za su nemi salama, amma ba za su same ta ba. 26Masifa a kan masifa, jita-jita a kan jita-jita. Suna neman wahayi daga wurin annabi, amma doka ta lalace a wurin firist, shawara kuma ta lalace a wurin dattawa. 27Sarki yana makoki, yarima kuma zai fid da zuciya. Hannuwan mutanen Æasar sun shanye saboda razana. Zan sÄka musu bisa ga ayyukansu, zan kuma hukunta su kamar yadda suka hukunta waÉansu. Za su kuwa sani ni ne Ubangiji.â
Currently Selected:
Eze 7: HAU
Highlight
Share
Copy
Want to have your highlights saved across all your devices? Sign up or sign in
@Bible Society of Nigeria 1979