YouVersion Logo
Search Icon

Eze 6

6
Annabci Gāba da Duwatsun Isra'ila
1Ubangiji ya yi magana da ni ya ce, 2“Ya ɗan mutum, ka zuba ido wajen duwatsun Isra'ila, sa'an nan ka yi annabci a kansu. 3Ka ce musu, ‘Ya ku duwatsun Isra'ila, ku ji maganar Ubangiji Allah! Haka Ubangiji Allah ya ce a kan duwatsu, da tuddai, da kwazazzabai, da kwaruruka. Ga shi, ni kaina, zan kawo takobi a kanku, zan hallaka wuraren tsafinku. 4Bagadanku za su zama kango, za a farfasa bagadanku na ƙona turare, zan sa kisassunku su faɗi a gaban gumakansu, 5zan sa gawawwakin Isra'ilawa a gaban gumakansu, zan warwatsa ƙasusuwanku kewaye da bagadanku. 6A duk inda kuke zaune, biranenku za su zama kango, wuraren tsafinku da bagadanku za su lalace, gumakanku da bagadanku na ƙona turare za a farfashe su. Za a shafe dukan abin da kuka yi. 7Za a kashe waɗansu daga cikinku sa'an nan za ku sani ni ne Ubangiji.
8“‘Duk da haka zan bar waɗansunku da rai, gama waɗansu daga cikinku za su tsere wa takobi, amma zan watsa su cikin sauran al'umma. 9Waɗansunku da suka tsere za su tuna da ni cikin al'ummai inda aka kai su bautar talala yadda raina ya ɓaci saboda zuciyarsu ta rashin imani wadda ta rabu da ni, da idanunsu masu zina da suke bin gumaka. Za su kuwa ji ƙyamar kansu saboda mugayen abubuwa da suka aikata. 10Za su kuma sani, ni Ubangiji, ba a banza na ce zan kawo musu wannan masifa ba’ ”
11Ubangiji Allah ya ce, “Ka tafa hannunka, ka ɗage ƙafarka, sa'an nan ka ce, ‘Kaito, kaito, saboda dukan mugayen abubuwan ƙyama da mutanen Isra'ila suka yi, gama takobi, da yunwa, da annoba za su kashe su. 12Annoba za ta kashe wanda yake nesa, wanda yake kusa kuwa takobi zai kashe shi. Yunwa kuma za ta kashe wanda yaƙi ya kewaye shi. Ta haka zan aukar da fushina a kansu. 13Za ku kuwa sani ni ne Ubangiji, sa'ad da gawawwakinsu sun kwanta tare da gumakansu kewaye da bagadansu a kan kowane tudu, da kan tsaunuka, da ƙarƙashin kowane itace mai duhuwa, da ƙarƙashin itacen oak mai ganye, duk inda suka miƙa turare mai ƙanshi ga dukan gumakansu. 14Zan nuna ikona a dukan ƙasar, in mai da ita da wuraren zamansu duka hamada. Ƙasarsu za ta zama hamada har zuwa Dibla. Kowa zai sani ni ne Ubangiji’ ”

Currently Selected:

Eze 6: HAU

Highlight

Share

Copy

None

Want to have your highlights saved across all your devices? Sign up or sign in