YouVersion Logo
Search Icon

Eze 25

25
Annabci a kan Ammonawa
1 # Irm 49.1-6; Eze 21.28-32; Amos 1.13-15; Zaf 2.8-11 Ubangiji kuma ya yi magana da ni, ya ce, 2“Ɗan mutum, ka fuskanci wajen Ammonawa, ka yi annabci a kansu. 3Ka faɗa musu su ji maganar Ubangiji Allah.” Ubangiji Allah ya ce, “Da yake kun ce, ‘Madalla,’ a lokacin da aka ƙazantar da Haikalina, da lokacin da ƙasar Isra'ila ta zama kufai, da lokacin da aka kai mutanen Yahuza bautar talala, 4domin haka zan bashe ku abin mallaka ga mutanen gabas. Za su kafa alfarwansu a cikinku, su zauna tare da ku. Za su ci amfanin gonakinku, su sha madararku. 5Zan mai da Rabba makiyayar raƙuma, in mai da biranen Ammonawa garken awaki da tumaki. Sa'an nan ku sani ni ne Ubangiji Allah.”
6Gama Ubangiji Allah ya ce, “Da yake kun tafa hannuwanku, kun buga ƙafafunku, kuka yi murna don nuna dukan ƙiyayyarku da ƙasar Isra'ila, 7domin haka zan miƙa hannuna gāba da ku, zan bashe ku, ku lalace a ƙasashe, zan hallaka ku. Sa'an nan za ku sani ni ne Ubangiji.”
Annabci a kan Mowab
8 # Ish 15.1—16.14; 25.10-12; Irm 48.1-47; Amos 2.1-3; Zaf 2.8-11 Ubangiji Allah ya ce, “Da yake Mowab da Seyir sun ce mutanen Yahuza sun zama kamar al'ummai, 9saboda haka zan buɗe ƙofar shiga Mowab daga garuruwan da suke kan iyaka, waɗanda su ne darajarta, wato Bet-yeshimot, da Ba'al-meyon, da Kiriyatayim. 10Zan bashe ta duk da Ammonawa su zama abin mallakar mutanen gabas, don kada um'ƙara tunawa da su a cikin al'ummai. 11Zan hukunta Mowab, sa'an nan za ta sani ni ne Ubangiji.”
Annabci a kan Edom
12 # Ish 34.5-17; 63.1-6; Irm 49.7-22; Eze 35.1-15; Amos 1.11,12; Oba 1.1-14; Mal 1.2-5 Ubangiji Allah ya ce, “Da yake Edom ta ɗaukar wa kanta fansa a kan mutanen Yahuza, ta yi babban laifi da ta ɗaukar wa kanta fansa, 13domin haka ni Ubangiji Allah zan hukunta Edom. Zan kashe mutanenta da dabbobinta, zan maishe ta kufai. Za a kashe su da takobi, tun daga Teman har zuwa Dedan. 14Mutanen Isra'la za su ɗaukar mini fansa a kan Edom. Za su aukar da fushina da hasalata a kan Edom, sa'an nan Edom za ta san sakayyata, ni Ubangiji Allah na faɗa.”
Annabci a kan Filistiyawa
15 # Ish 14.29-31; Irm 47.1-7; Yow 3.4-8; Amos 1.6-8; Zaf 2.4-7; Zak 9.5-7 Ubangiji Allah ya ce, “Tun da yake Filistiyawa sun yi sakayya, sun ɗauki fansa da muguwar zuciya da ƙiyayya marar ƙarewa, don su hallakar, 16domin haka ni Ubangiji Allah zan hukunta Filistiyawa. Zan kashe Keretiyawa, in hallaka sauran mazaunan gāɓar teku. 17Zan yi musu babbar sakayya da hukunci mai tsanani. Sa'an nan za su sani ni ne Ubangiji, sa'ad da na ɗauki fansa a kansu.”

Currently Selected:

Eze 25: HAU

Highlight

Share

Compare

Copy

None

Want to have your highlights saved across all your devices? Sign up or sign in