Eze 24
24
Misali a kan Tukunyar da Take Tafasa
1A kan rana ta goma ga watan goma, a shekara ta tara, sai Ubangiji ya yi magana da ni, ya ce, 2#2Sar 25.1; Irm 52.4 “Ɗan mutum, ka rubuta sunan wannan rana. Ranar ke nan da Sarkin Babila ya kewaye Urushalima da yaƙi. 3Ka yi wa 'yan tawayen nan magana da misali, ka faɗa musu cewa, ni Ubangiji na ce,
“ ‘Ka ɗora tukunya, ka ɗora ta a wuta,
Ka cika ta da ruwa.
4Ka zuba gunduwoyin nama a ciki,
Dukan gunduwoyi masu kyau, wato cinya da kafaɗa,
Ka cika ta da tantakwashi.
5Ka kama mafi kyau daga cikin garken,
Ka sa sauran ƙasusuwa a ƙarƙashinsa,
Ka tafasa gunduwoyin,
Ka kuma tafasa tantakwashin.’
6“Ni Ubangiji Allah na ce,
‘Domin haka kaiton birnin nan mai zubar da jini,
Da tukunya wadda take da tsatsa,
Wadda tsatsarta ba ta fita cikinta ba!
Ka sa sauran ƙasusuwa a ƙarƙashinsa,
Kada ka yi zaɓe.
7Gama jinin da ta zubar yana tsakiyarta,
Ta zubar da shi a kan dutse,
Ba ta zubar da shi a ƙasa inda za ta rufe shi da ƙura ba.
8Don a tsokani fushina har in yi sakayya,
Na zuba jinin da ta zubar a kan dutse,
Don kada a rufe shi.’
9“Saboda haka, ni Ubangiji Allah na ce,
‘Kaitonka, ya birni, mai zubar da jini!
Ni kuma zan tsiba itace da yawa.
10Ka tula gumagumai, ka kunna wuta,
Ka tafasa naman sosai,
Ka zuba kayan yaji a ciki,
Ka bar ƙasusuwan su ƙone.
11Ka ɗora tukunyar da ba kome cikinta a bisa garwashi
Domin ta yi zafi, tagullarta ta yi ja wur,
Domin dauɗarta ta narke a ciki,
Tsatsarta kuma ta ƙone.
12Ta gajiyar da ni a banza,
Wutar ba ta fitar da yawan tsatsarta ba.
13Ya Urushalima, tsatsarki ita ce ƙazantar lalatarki.
Da yake na tsabtace ki, ba ki tsabtatu ba,
To, ba za ki ƙara yin tsabta ba,
Har lokacin da na fashe fushina a kanki.’
14Ni, Ubangiji na faɗa, zai tabbata gama zan aikata, ba zan fasa ba, ba kuwa zan ƙyale ba, ba kuma zan bari ba. Zan hukunta ki saboda hanyoyinki da ayyukanki, ni Ubangiji Allah na faɗa.”
Rasuwar Matar Ezekiyel
15Ubangiji kuma ya yi magana da ni, ya ce, 16“Ya ɗan mutum, ga shi, ina gab da ɗauke maka ƙaunatacciyarka farat ɗaya, amma fa, kada ka yi makoki, ko kuka, ko ka zubar da hawaye. 17Ka yi ajiyar zuciya a hankali, kada ka yi makoki saboda matacciyar. Ka naɗa rawaninka, ka sa takalmanka, kada ka ja amawali, kada kuma ka ci abincin masu makoki.”
18Sai na yi magana da mutane da safe, da maraice kuwa matata ta rasu. Kashegari da safe, sai na yi kamar yadda aka umarce ni. 19Mutane kuwa suka tambaye ni dalilin da ya sa nake yin haka.
20Sai na ce musu, “Ubangiji ya yi magana da ni, ya ce, 21in faɗa wa mutanen Isra'ila, cewa Ubangiji Allah ya ce, ‘Zan ƙazantar da Haikalina, abin fariyarku, da abin da idanunku suke jin daɗin ganinsa, da abin faranta zuciyarku. 'Ya'yanku maza waɗanda kuka bari a baya, za a kashe su da takobi. 22Za ku kuwa yi kamar yadda na yi, wato ba za ku ja amawali ba, ba kuwa za ku ci abincin masu makoki ba. 23Za ku naɗa rawunanku, ku sa takalmanku, ba za ku kuma yi makoki ko kuka ba, amma za ku lalace cikin zunubanku. Za ku yi ta nishi. 24Da haka Ezekiyel zai zama muku alama. Za ku yi kamar yadda ya yi duka. Sa'ad da wannan ya faru, za ku sani nine Ubangiji Allah.’
25“Kai ɗan mutum, a ranar da zan ɗauke musu madogararsu, da murnarsu, da darajarsu, da abin da idanunsu suka ji daɗin gani, da abin da yake faranta zuciyarsu, da 'ya'yansu mata da maza, 26a wannan rana wanda ya tsere zai kawo maka labarin. 27A ranar bakinka zai buɗe, za ka yi magana da wanda ya tsere, ba kuma za ka zama bebe ba. Da haka za ka zama alama gare su, za su kuwa sani ni ne Ubangiji.”
Currently Selected:
Eze 24: HAU
Highlight
Share
Compare
Copy
Want to have your highlights saved across all your devices? Sign up or sign in
@Bible Society of Nigeria 1979