YouVersion Logo
Search Icon

Eze 18

18
Hakkin Kowa
1Ubangiji kuma ya yi magana da ni, ya ce, 2#Irm 31.29 “Me kuke nufi da faɗar wannan karin magana a kan ƙasar Isra'ila cewa,
“ ‘Ubanni sun ci 'ya'yan inabi masu tsami,
Hakoran 'ya'ya kuwa sun mutu’?
3“Ni Ubangiji Allah na ce, hakika, ba za a ƙara faɗar wannan karin magana a Isra'ila ba. 4Ga shi, dukan rayuka nawa ne, da ran uban da na ɗan, duka nawa ne. Wanda ya yi zunubi shi zai mutu.
5“Ga irin mutumin da zai rayu, mutumin da yake adali, yana bin shari'a, yana kuma aikata abin da yake daidai, 6idan ba ya cin abinci a ɗakin tsafi, bai bauta wa gumakan mutanen Isra'ila ba, bai kwana da matar maƙwabcinsa ba, ba yakan kwana da mace a lokacin hailarta ba, 7wanda ba ya cin zalin kowa, wanda yakan mayar wa wanda ya ba shi jingina abin da ya jinginar masa, wanda ba ya ƙwace, amma yakan ba mayunwanci abinci, wanda yakan ba huntu tufa, 8wanda ba ya ba da bashi da ruwa, ko tare da wani ƙari, wanda yake hana hannunsa yin mugunta, amma yana goyon bayan gaskiya tsakanin masu gardama, 9#L.Fir 18.5 wanda yake bin dokokina, yana kuma kiyaye ka'idodina da aminci, shi adali ne. Hakika zai rayu, ni Ubangiji na faɗa.
10“Amma idan ya haifi ɗa wanda ya zama ɗan fashi, mai kisankai, yana yi wa ɗan'uwansa ɗaya daga cikin abubuwan nan, ko shi kansa, 11bai yi irin waɗannan abubuwa ba, wato yana cin abinci a ɗakin tsafi, yana kwana da matar maƙwabcinsa, 12yana kuma cin zalin matalauta masu fatara, yana yin ƙwace, ba ya mayar da abin da aka jinginar masa, yana bauta wa gumaka, yana kuma aikata abubuwa masu banƙyama, 13yana ba da bashi da ruwa da ƙari, wannan ba zai rayu ba, gama ya aikata dukan abubuwan nan masu banƙyama. Zai mutu lalle, alhakin jininsa kuwa yana a kansa.
14“Amma idan wannan mutum ya haifi ɗa wanda ya ga dukan laifofin da mahaifinsa ya yi, sa'an nan ya ji tsoro, bai kuwa yi haka ba, 15bai ci abinci a ɗakin tsafi ba, bai bauta wa gumakan mutanen gidan Isra'ila ba, bai kwana da matar maƙwabcinsa ba, 16bai ci zalin kowa ba, bai karɓi jingina ba, bai yi ƙwace ba, amma yana ba mayunwaci abinci, yana ba huntu tufa, 17yana hana hannunsa aikata mugunta, bai ba da bashi da ruwa ko wani ƙari ba, yana kiyaye ka'idodina, yana kuma bin dokokina, ba zai mutu saboda laifin mahaifinsa ba, amma zai rayu. 18Amma mahaifinsa, da yake ya yi zalunci, ya yi wa ɗan'uwansa ƙwace ya aikata mugun abu a cikin mutanensa, zai mutu saboda muguntarsa.
19“Za ku yi tambaya cewa, ‘Me ya sa ɗa ba zai ɗauki hakkin laifin mahaifinsa ba?’ Sa'ad da ɗan ya bi shari'a, ya yi abin da yake daidai, ya kiyaye dokokina sosai, lalle zai rayu. 20#M.Sh 24.16 Wanda ya yi zunubi shi zai mutu. Ɗa ba zai ɗauki hakkin laifin mahaifinsa ba, mahaifi kuma ba zai ɗauki hakkin laifin ɗansa ba. Adalcin adali nasa ne, muguntar mugu kuma tasa ce.
Ayyukan Allah Daidai Ne
(Eze 33.10-20)
21“Amma idan mugu ya bar dukan muguntarsa da ya aikata, ya kiyaye dokokina, ya bi shari'a, ya yi abin da yake daidai, zai rayu, ba zai mutu ba. 22Ba za a bi hakkin laifin da ya aikata ba. Zai rayu saboda adalcin da ya yi. 23Ni Ubangiji Allah, na ce, ina jin daɗin mutuwar mugu ne? Ban fi so ya bar mugun halinsa ya rayu ba?
24“Amma idan adali ya bar yin adalci, ya aikata mugunta, ya yi abubuwa masu banƙyama waɗanda mugu yake aikatawa, zai rayu? Ayyukansa na adalci waɗanda ya aikata, ba za a tuna da su ba, faufau. Zai mutu saboda rashin amincin da ya yi da laifin da ya aikata.
25“Amma kun ce, ‘Hanyar Ubangiji ba daidai ba ce.’ Ku ji ya ku mutanen Isra'ila, hanyata ba daidai ba ce? Ashe, ba hanyarku ce ba daidai ba? 26Sa'ad da adali ya bar adalcinsa, ya kuwa aikata mugunta zai mutu saboda muguntarsa. 27Idan kuma mugu ya bar muguntarsa da yake yi, ya kuwa bi shari'a, ya yi abin da yake daidai, zai rayu. 28Domin ya yi tunani, ya bar laifofin da ya aikata, zai rayu, ba zai mutu ba. 29Amma mutanen Isra'ila suna cewa hanyar Ubangiji ba daidai ba ce. Ya mutanen Isra'ila, hanyata ba daidai ba ce? Ashe, ba hanyarku ce ba daidai ba?
30“Domin haka ni Ubangiji Allah zan hukunta ku, ku mutanen Isra'ila, kowa gwargwadon ayyukansa. Ku tuba, ku bar laifofinku domin kada su zama muku dalilin halaka. 31Ku rabu da laifofin da kuka yi mini, sa'an nan ku samo wa kanku sabuwar zuciya da sabon hali. Don me za ku mutu, ya ku jama'ar Isra'ila? 32Ni Ubangiji Allah na ce ba na murna da mutuwar kowa, saboda haka sai ku tuba domin ku rayu.”

Currently Selected:

Eze 18: HAU

Highlight

Share

Copy

None

Want to have your highlights saved across all your devices? Sign up or sign in