Eze 17
17
Misalin Gaggafa da Kurangar Inabi
1Ubangiji kuma ya yi magana da ni, ya ce, 2“Ɗan mutum, ka faɗa wa mutanen Isra'ila ka-cici-ka-cici, da kuma misali. 3Ka ce, Ubangiji Allah ya ce, ‘Wata babbar gaggafa mai manyan fikafikai, da dogayen gasusuwan fikafikai da gasusuwa da yawa masu launi iri iri, ta zo Lebanon ta ciri kan itacen al'ul. 4Ta karya kan tohonsa mafi tsawo, ta kai shi a ƙasar ciniki, ta dasa shi a birnin 'yan kasuwa. 5Sai kuma ta ɗauki irin na ƙasar, ta dasa shi a wuri mai dausayi kusa da ruwa mai yawa. Ta dasa shi kamar itacen wardi. 6Ya yi toho, ya zama kuranga mai yaɗuwa. Rassanta suka tanƙwasa wajenta. Saiwoyinta suka kama ƙasa sosai. Haka ta zama kuranga, ta yi rassa da ganyaye.
7“ ‘Akwai kuma wata babbar gaggafa mai manyan fikafikai da gashi mai yawa. Sai wannan kuranga ta tanƙwasa saiwoyinta zuwa wajenta, ta kuma miƙe rassanta zuwa wajenta tun daga inda aka dasa ta, don gaggafar ta yi mata banruwa. 8An dasa ta a wuri mai dausayi inda akwai ruwa da yawa don ta yi ganyaye, ta kuma ba da 'ya'ya, ta zama kurangar inabi ta ƙwarai.’ 9Ka ce, Ubangiji Allah ya ce, ‘Ko wannan kurangar inabi za ta ci gaba? Ashe, gaggafa ta farko ba za ta tumɓuke saiwoyinta, ta sassare rassanta, don ganyayenta da suke tohuwa su bushe ba? Ba sai da hannu mai ƙarfi, ko kuwa da yawan mutane za a tumɓuke ta daga saiwoyinta ba. 10Idan aka sāke dasa ta kuma za ta yi amfani? Ba za ta bushe sarai sa'ad da iskar gabas ta hura ba? Lalle za ta bushe tun daga inda aka dasa ta ta yi girma.’ ”
Fassarar Misalin
11Ubangiji kuma ya yi magana da ni, ya ce, 12#2Sar 24.15-20; 2Tar 36.10-13 “Ka tambayi mutanen Isra'ila, 'yan tawayen nan cewa, ‘Ba ku san ma'anar waɗannan abubuwa ba?’ Ka faɗa musu, cewa Sarkin Babila ya zo Urushalima, ya tafi da sarkinta da shugabanninta zuwa Babila. 13Sai ya dauƙi wani daga zuriyar sarauta, ya yi alkawari da shi, ya kuma rantsar da shi. Ya kwashe mutanen ƙasa masu maƙami, 14don sarautar ƙasar ta raunana, ta kāsa ɗaga kanta, amma ta tsaya dai ta wurin cika alkawarinsa. 15Amma Sarkin Yahuza ya tayar masa, da ya aiki wakilai zuwa Masar don a ba shi dawakai da sojoji masu yawa. To, zai yi nasara? Wanda ya yi irin wannan abu zai tsira? Zai iya ta da alkawari sa'an nan ya tsere?
16“Ni Ubangiji Allah, na ce, hakika wannan sarki zai mutu a Babila, domin bai cika rantsuwarsa da alkawarin da ya yi wa Sarkin Babila, wanda ya naɗa shi ba. 17Fir'auna da yawan sojojinsa masu ƙarfi, ba za su taimake shi da yaƙin ba, sa'ad da Babilawa suka gina mahaurai da kagarai don su kashe mutane da yawa. 18Bai kuwa cika rantsuwarsa da alkawarinsa ba. Ya ƙulla alkawari, amma ga shi, ya aikata dukan waɗannan abubuwa, ba zai kuɓuta ba.
19“Domin haka ni Ubangiji Allah, na ce, hakika zan nemi hakkin rantsuwar da ya yi mini, da alkawarin da ya yi mini, waɗanda bai cika ba. 20Zan kafa masa tarko in kama shi, sa'an nan in kai shi Babila inda zan yi masa shari'a saboda ya tayar mini. 21Dukan sojojinsa zaɓaɓɓu za a kashe su da takobi, za a watsar da waɗanda suka ragu ko'ina. Za ku sani ni Ubangiji ne na faɗa.”
Alkawarin Sa Zuciya
22Ga abin da Ubangiji Allah ya ce,
“Ni kaina zan cire toho a kan itacen al'ul mai tsawo.
Daga cikin sababbin rassansa zan karya lingaɓu,
In dasa shi a tsauni mai tsayi.
23A ƙwanƙolin tsaunin Isra'ila zan dasa shi
Don ya fito da rassa, ya ba da 'ya'ya,
Ya zama itacen al'ul na gaske.
Tsuntsaye iri iri za su zauna a ƙarƙashinsa,
Za su yi sheƙuna a cikin inuwar rassansa.
24Dukan itatuwan jeji za su sani,
Ni Ubangiji nakan sa manyan itatuwa su zama ƙanana,
In sa ƙanana kuma su zama manya,
In sa ɗanyen itace ya bushe,
In sa busasshen itace kuma ya zama ɗanye, Ni Ubangiji na faɗa, zan kuwa aikata.”
Currently Selected:
Eze 17: HAU
Highlight
Share
Copy
Want to have your highlights saved across all your devices? Sign up or sign in
@Bible Society of Nigeria 1979