Fit 25
25
Sadakoki domin Yin Wuri Mai Tsarki
(Fit 35.4-9)
1Ubangiji ya ce wa Musa, 2“Faɗa wa Isra'ilawa su karɓo mini kaya daga dukan wanda ya yi niyyar bayarwa. 3Ga irin sadakokin da za ku karɓa, zinariya, da azurfa, da tagulla, 4da ulu mai launin shuɗi, da mai launin shunayya, da mai launin ja, da lilin mai laushi, da gashin akuya, 5da jemammun fatun raguna, da fatun awaki, da itacen ƙirya, 6da mai domin fitila, da kayan yaji domin man keɓewa, da turaren ƙonawa, 7da onis, da duwatsun da za a mammanne a falmaran da ƙyallen maƙalawa a ƙirji. 8Za su yi tsattsarkan wuri domina, don in zauna tare da su. 9Za ku yi mazaunina da kayayyakinsa duka, bisa ga irin fasalin da zan nuna maka.”
Akwatin Alkawari
(Fit 37.1-9)
10“Sai ku yi akwatin alkawari da itacen maje, tsawonsa ya zama kamu biyu da rabi, fāɗinsa kuwa kamu ɗaya da rabi, tsayinsa ya zama kamu ɗaya da rabi. 11Ku dalaye shi da zinariya tsantsa ciki da waje. Ku yi wa gyaffansa ado da gurun zinariya. 12Za ku yi wa akwatin ƙawanya huɗu na zinariya ku liƙa a kowace kusurwar akwatin, wato ƙawanya biyu a kowane gefe na tsawon. 13Za ku kuma yi sanduna da itacen ƙirya, ku dalaye su da zinariya. 14Ku sa sandunan a kafar kowace ƙawanya da take gyaffan akwatin saboda ɗaukarsa. 15Za a bar sandunan cikin ƙawanen akwatin, kada a zare su. 16A kuma sa allunan da suke da dokokin da zan ba ka a cikin akwatin.
17 #
Ibr 9.5
“Za ku yi wa akwatin murfi da zinariya tsantsa, tsawonsa kamu biyu da rabi, fāɗinsa kuma kamu ɗaya da rabi. 18Za ku yi siffofin kerubobi biyu da ƙerarriyar zinariya, ku sa a gefen nan biyu na murfin. 19Siffar kerub ɗaya a kowane gefe. Ku yi su ta yadda za su zama ɗaya da murfin. 20Fikafikan kerubobin za su miƙe bisa domin su inuwantar da murfin, za su fuskanci juna, suna duba murfin. 21Za ku sa murfin bisa akwatin. A cikin akwatin kuwa za ku sa allunan da suke da dokokin da zan ba ka. 22A nan zan zo in sadu da kai, in yi magana da kai, wato tsakanin kerubobi biyu da suke bisa akwatin alkawari. Zan ba ka umarnaina duka don Isra'ilawa.”
Teburin Gurasar Ajiyewa ga Ubangiji
(Fit 37.10-16)
23“Ku yi tebur da itacen ƙirya, tsawonsa kamu biyu, fāɗinsa kamu ɗaya, tsayinsa kuma kamu ɗaya da rabi. 24Ku dalaye shi da zinariya tsantsa, ku kuma yi masa ado kewaye da gurun zinariya. 25Za ku yi wa tebur ɗin dajiya mai fāɗin tafin hannu, ku kuma yi wa dajiyar ado da gurun zinariya. 26Za ku yi ƙawanya huɗu da zinariya, ku sa a kusurwa huɗu na ƙafafun teburin. 27Ƙawanen za su kasance kusa da dajiyar don su riƙe sandunan ɗaukar teburin. 28Ku yi sanduna da itacen ƙirya, sa'an nan ku dalaye su da zinariya. Da su za a riƙa ɗaukar teburin. 29Da zinariya tsantsa kuma za ku yi farantansa, da kwanonin tuya, da butocinsa, da kwanoninsa domin yin hadayu na sha. 30#L.Fir 24.5-8 Kullum za ku riƙa ajiye gurasar da kuke kawo mini a bisa teburin.”
Alkuki
(Fit 37.17-24)
31“Ku kuma yi alkuki da zinariya tsantsa. Ku yi gindinsa da gorar jikinsa da ƙerarriyar zinariya. Ƙoƙuna, da mahaɗai, da furanninsa a haɗe da shi za ku yi su. 32Alkukin ya kasance da rassa shida, rassa uku a kowane gefe. 33A kowane reshe na alkuki za a yi ƙoƙuna uku masu kamar tohon almond. Ya kasance kuma da mahaɗai da furanni. 34Za a yi wa gorar alkukin ƙoƙuna huɗu masu kamar tohon almond, da mahaɗai da furanni. 35A gindin kowane reshe biyu za a yi mahaɗi ɗaya. 36Da mahaɗai da rassan za su kasance a haɗe da alkukin. Da ƙerarriyar zinariya za a yi su. 37Ku kuma yi fitilu bakwai, ku sa su a bisa alkukin ta yadda za su haskaka wajen da suka fuskanta. 38Ku kuma yi hantsuka da farantai da zinariya tsantsa. 39Da zinariya tsantsa na talanti ɗaya za ku yi alkukin da waɗannan abubuwa duka. 40#A.M 7.44; Ibr 8.5 Sai ku lura, ku yi waɗannan abubuwa duka bisa ga fasalin da aka nuna maka a bisa dutsen.”
Currently Selected:
Fit 25: HAU
Highlight
Copy
Compare
Share
Want to have your highlights saved across all your devices? Sign up or sign in
@Bible Society of Nigeria 1979