Fit 24
24
Tabbatar da Alkawari
1Ubangiji ya ce wa Musa, “Ku zo wurina, kai, da Haruna, da Nadab, da Abihu, da dattawa saba'in na Isra'ila. Ku yi sujada daga nesa kaɗan. 2Musa ne kaɗai zai kusaci Ubangiji. Amma sauran kada su zo kusa, kada kuma jama'a su hau tare da shi.”
3Musa ya tafi, ya faɗa wa jama'a dukan dokokin Ubangiji da ka'idodinsa, sai dukan jama'a suka amsa gaba ɗaya, suka ce, “Za mu kiyaye dukan dokokin da Ubangiji ya ba mu.” 4Musa kuwa ya rubuta dukan dokokin Ubangiji. Kashegari da sassafe ya gina bagade a gindin dutsen, da kuma ginshiƙai goma sha biyu bisa ga yawan kabilai goma sha biyu na Isra'ila. 5Ya kuma sa samarin Isra'ila su miƙa hadaya ta ƙonawa, da hadaya ta salama, da bijimai ga Ubangiji. 6Sai Musa ya zuba rabin jinin a tasa, sauran rabin jinin kuwa ya yayyafa a kan bagade. 7Ya kuma ɗauki Littafin Alkawari, ya karanta wa jama'a, sai suka ce, “Za mu yi dukan abin da Ubangiji ya faɗa, za mu yi biyayya.” 8#Mat 26.28; Mar 14.24; Luk 22.20; 1Kor 11.25; Ibr 10.29; Ibr 9.19,20 Musa kuwa ya ɗauki jinin ya watsa wa jama'ar. Sa'an nan ya ce, “Wannan shi ne jinin alkawarin da Ubangiji ya yi da ku, wanda yake cikin dokokin nan duka.”
9Musa ya haura tare da Haruna, da Nadab, da Abihu, da dattawan nan saba'in na Isra'ila. 10Suka ga Allah na Isra'ila. Wurin da yake ƙarƙashin tafin ƙafafunsa yana kama da daɓen da aka yi da dutsen yakutu, garau kamar sararin sama. 11Amma Ubangiji bai yi wa dattawan Isra'ila wani abu ba, ko da yake suka ga zatin Allah. Su kuma suka ci suka sha a gaban Allah.
Musa a bisa Dutsen Sina'i
12Ubangiji ya ce wa Musa, “Ka hawo zuwa wurina a bisa dutsen, ka zauna har in ba ka allunan dutse da yake da dokoki da farillan da na rubuta don a koya musu.” 13Sai Musa ya tashi, shi da baransa Joshuwa, suka tafi, suka hau dutsen Allah. 14Ya ce wa dattawan, “Ku dakata a nan har mu komo wurinku. Haruna da Hur suna tare da ku, in wani yana da wata damuwa, sai ya je wurinsu.” Sa'an nan Musa ya hau bisa dutsen.
15Da hawan Musa bisa dutsen, girgije ya rufe kan dutsen. 16Ɗaukakar Ubangiji kuma ta zauna bisa Dutsen Sina'i. Girgijen ya lulluɓe dutsen har kwana shida, a rana ta bakwai kuwa Ubangiji ya kira Musa daga cikin girgijen. 17Isra'ilawa suka ga ɗaukakar Ubangiji kamar wuta mai cinyewa a bisa ƙwanƙolin dutsen. 18#M.Sh 9.9 Sai Musa ya shiga girgijen, ya hau bisa dutsen. Ya zauna a kan dutsen yini arba'in da dare arba'in.
Currently Selected:
Fit 24: HAU
Highlight
Copy
Compare
Share
Want to have your highlights saved across all your devices? Sign up or sign in
@Bible Society of Nigeria 1979