YouVersion Logo
Search Icon

Fit 20

20
Dokoki Goma
1Allah ya faɗi dukan waɗannan zantuttuka, ya ce, 2“Ni ne Ubangiji Allahnka wanda ya fisshe ka daga ƙasar Masar, daga gidan bauta.
3“Kada ka kasance da waɗansu alloli sai ni.
4 # Fit 34.17; L.Fir 19.4; 26.1; M.Sh 4.15-18; 27.15 “Kada ka yi wa kanka wani gunki ko kuwa wata siffa ta wani abu a sama a bisa, ko a duniya a ƙasa, ko kuma a ruwa a ƙarƙarshin ƙasa. 5#Fit 34.6,7; L.Ƙid 14.18; M.Sh 7.9,10 Kada ka rusuna musu, kada kuwa ka bauta musu, gama ni Ubangiji Allahnka, mai kishi ne. Nakan hukunta 'ya'ya har tsara ta uku da ta huɗu na waɗanda suke ƙina. 6Amma nakan gwada madawwamiyar ƙaunata ga dubban tsararrakin da suke ƙaunata, masu kiyaye dokokina.
7 # L.Fir 19.12 “Kada ka kama sunan Ubangiji Allahnka a banza, gama zan hukunta duk wanda ya kama sunana a banza.
8 # Fit 16.23-30; 31.12-14 “Tuna da rana Asabar, ka kiyaye ta da tsarki. 9#Fit 23.12; 31.15; 34.21; 35.2; L.Fir 23.3 Za ku yi dukan ayyukanku cikin kwana shida, 10amma rana ta bakwai keɓaɓɓiya ce ga Ubangiji Allahnka. A ranar ba za ka yi kowane irin aiki ba, ko kai, ko 'ya'yanka, ko barorinka, ko dabbobinka, ko kuwa baƙon da yake zaune tare da ku. 11#Far 2.1-3; Fit 31.17 Gama cikin kwana shida Ubangiji ya yi sama, da duniya, da teku, da dukan abin da yake cikinsu, amma a rana ta bakwai ya huta. Soboda haka Ubangiji ya keɓe ranar Asabar, ya tsarkake ta.
12 # M.Sh 27.16; Mat 15.4; 19.19; Mar 7.10; 10.19; Luk 18.20; Afi 6.2; Afi 6.3 “Ka girmama mahaifinka da mahaifiyarka, domin ka yi tsawon rai a ƙasar da Ubangiji Allahnka yake ba ka.
13 # Far 9.6; L.Fir 24.17; Mat 5.21; 19.18; Mar 10.19; Luk 18.20; Rom 13.9; Yak 2.11 “Kada ka yi kisankai.
14 # L.Fir 20.10; Mat 5.27; 19.18; Mar 10.19; Luk 18.20; Rom 13.9; Yak 2.11 “Kada ka yi zina.
15 # L.Fir 19.11; Mat 19.18; Mar 10.19; Luk 18.20; Rom 13.9 “Kada ka yi sata.
16 # Fit 23.1; Mat 19.18; Mar 10.19; Luk 18.20 “Kada ka ɓāta sunan maƙwabcinka.
17 # Rom 7.7; 13.9 “Kada ka yi ƙyashin gidan maƙwabcinka. Kada kuma ka yi ƙyashin matar maƙwabcinka, ko barorinsa mata da maza, ko sansa, ko jakinsa, ko kowane abin da yake nasa.”
Jama'a suka Tsorata
18 # Ibr 12.18,19 Da jama'a suka ji tsawar hadiri, da ƙarar ƙaho mai tsanani suka kuma ga walƙiya, da dutsen yana hayaƙi, sai suka ji tsoro suka yi rawar jiki, suka tsaya nesa. 19Suka ce wa Musa, “Kai, ka yi magana da mu, za mu ji, amma kada Allah ya yi magana da mu don kada mu mutu.”
20Musa kuwa ya ce wa jama'a, “Kada ku ji tsoro, gama Allah ya zo ne don ya jarraba ku, don ku riƙa girmama shi, don kuma kada ku yi zunubi.” 21Sai jama'a suka tsattsaya nesa, Musa kuwa ya matsa kusa da girgije mai duhu inda Allah yake.
Dokoki a kan Bagadai
22Ubangiji ya ce wa Musa, “Haka za ka faɗa wa Isra'ilawa, ‘Ku da kanku kun ji na yi magana da ku daga sama. 23Banda ni, kada ku yi wa kanku allolin azurfa da na zinariya. 24Za ku gina mini bagade na ƙasa. A kansa za ku miƙa mini hadayu na ƙonawa da na salama, da tumakinku da shanunku. A duk inda na sa a tuna da sunana zan zo wurinku in sa muku albarka. 25#M.Sh 27.5-7; Josh 8.31 Idan kuwa za ku gina mini bagade na dutse, kada ku gina mini da sassaƙaƙƙun duwatsu, gama idan guduma ta taɓa duwatsun sun haramtu. 26Kada ku yi wa bagadena matakai domin kada tsiraicinku ya bayyana a bisansu sa'ad da kuke hawansu’ ”

Currently Selected:

Fit 20: HAU

Highlight

Copy

Compare

Share

None

Want to have your highlights saved across all your devices? Sign up or sign in