1
Fit 20:2-3
Littafi Mai Tsarki
HAU
“Ni ne Ubangiji Allahnka wanda ya fisshe ka daga ƙasar Masar, daga gidan bauta. “Kada ka kasance da waɗansu alloli sai ni.
Compare
Explore Fit 20:2-3
2
Fit 20:4-5
“Kada ka yi wa kanka wani gunki ko kuwa wata siffa ta wani abu a sama a bisa, ko a duniya a ƙasa, ko kuma a ruwa a ƙarƙarshin ƙasa. Kada ka rusuna musu, kada kuwa ka bauta musu, gama ni Ubangiji Allahnka, mai kishi ne. Nakan hukunta 'ya'ya har tsara ta uku da ta huɗu na waɗanda suke ƙina.
Explore Fit 20:4-5
3
Fit 20:12
“Ka girmama mahaifinka da mahaifiyarka, domin ka yi tsawon rai a ƙasar da Ubangiji Allahnka yake ba ka.
Explore Fit 20:12
4
Fit 20:8
“Tuna da rana Asabar, ka kiyaye ta da tsarki.
Explore Fit 20:8
5
Fit 20:7
“Kada ka kama sunan Ubangiji Allahnka a banza, gama zan hukunta duk wanda ya kama sunana a banza.
Explore Fit 20:7
6
Fit 20:9-10
Za ku yi dukan ayyukanku cikin kwana shida, amma rana ta bakwai keɓaɓɓiya ce ga Ubangiji Allahnka. A ranar ba za ka yi kowane irin aiki ba, ko kai, ko 'ya'yanka, ko barorinka, ko dabbobinka, ko kuwa baƙon da yake zaune tare da ku.
Explore Fit 20:9-10
7
Fit 20:17
“Kada ka yi ƙyashin gidan maƙwabcinka. Kada kuma ka yi ƙyashin matar maƙwabcinka, ko barorinsa mata da maza, ko sansa, ko jakinsa, ko kowane abin da yake nasa.”
Explore Fit 20:17
8
Fit 20:16
“Kada ka ɓāta sunan maƙwabcinka.
Explore Fit 20:16
9
Fit 20:14
“Kada ka yi zina.
Explore Fit 20:14
10
Fit 20:13
“Kada ka yi kisankai.
Explore Fit 20:13
11
Fit 20:15
“Kada ka yi sata.
Explore Fit 20:15