M.Sh 32
32
1“Ku saurara, ya ku sammai, gama zan yi magana,
Bari duniya ta ji maganar bakina.
2Bari koyarwata ta zubo kamar ruwan sama,
Maganata ta faɗo kamar raɓa,
Kamar yayyafi a bisa ɗanyar ciyawa,
Kamar ɗiɗɗigar ruwa a bisa ganyaye.
3Gama zan yi shelar sunan Ubangiji,
In yabi girman Allahnmu!
4“Shi Dutse ne, aikinsa kuma cikakke ne,
Gama dukan hanyoyinsa masu adalci ne.
Allah mai aminci ne, babu rashin gaskiya a gare shi,
Shi mai adalci ne, nagari ne kuma.
5Sun aikata mugunta a gabansa,
Su ba 'ya'yansa ba ne saboda lalacewarsu,
Su muguwar tsara ce, karkatacciya,
6Haka za ku sāka wa Ubangiji,
Ya ku wawaye, mutane marasa hikima?
Ba shi ne Ubanku, Mahaliccinku ba,
Wanda ya yi ku, ya kuma kafa ku?
7“Ku fa tuna da kwanakin dā,
Ku yi tunani a kan shekarun tsararraki,
Ku tambayi mahaifanku, su za su faɗa muku,
Ku tambayi dattawanku, su kuma za su faɗa muku,
8 #
A.M 17.26
Sa'ad da Maɗaukaki ya ba al'ummai gādonsu,
Sa'ad da ya raba 'yan adam,
Ya yanka wa mutane wurin zama bisa ga yawan Isra'ilawa.
9Gama rabon Ubangiji shi ne jama'arsa,
Yakubu shi ne rabon gādonsa.
10“Ya same shi daga cikin hamada,
A jeji marar amfani, inda namomi suke kuka.
Ya kewaye shi, ya lura da shi,
Ya kiyaye shi kamar ƙwayar idonsa.
11Kamar gaggafar da take kaɗa fikafikanta a kan sheƙarta,
Tana rufe da 'yan tsakinta,
Ta buɗe fikafikanta, ta kama su,
Ta ɗauke su a bisa kafaɗunta.
12Ubangiji ne kaɗai ya bishe shi,
Ba wani baƙon allah tare da shi.
13“Ya sa shi ya hau kan tuddai,
Ya ci amfanin ƙasa,
Ya sa shi ya sha zuma daga dutse,
Ya ba shi mai daga dutsen ƙanƙara.
14Ya sami kindirmo daga shanu,
Da madara daga garken tumaki da na awaki,
Da kitse daga 'yan raguna, da raguna,
Da bijimai, da bunsurai daga Bashan,
Da alkama mafi kyau.
Ka sha ruwan inabi jaja wur, mai kyau.
15“Yeshurun ya yi ƙiba, yana harbin iska,
Ka yi ƙiba, ka yi kauri, ka yi sumul.
Ya rabu da Allahn da ya yi shi,
Ya raina Dutsen Cetonsa.
16Suka sa shi kishi, saboda gumaka,
Suka tsokani fushinsa da abubuwan banƙyama.
17 #
1Kor 10.20
Suka miƙa hadayu ga aljannun da ba Allah ba,
Ga gumakan da ba su sani ba,
Sababbin allolin da aka shigo da su daga baya,
Waɗanda kakanninku ba su ji tsoronsu ba.
18Kun ƙi kula da Dutsen da ya haife ku,
Kun manta da Allahn da ya ba ku rai.
19“Ubangiji ya gani, ya raina su,
Saboda tsokanar da 'ya'yansa mata da maza suka yi masa.
20Ya ce, ‘Zan ɓoye musu fuskata,
Zan ga yadda ƙarshensu zai zama.
Gama su muguwar tsara ce,
'Ya'ya ne marasa aminci.
21 #
1Kor 10.22;
Rom 10.19
Suka sa ni kishi da abin da ba Allah ba,
Suka tsokani fushina da gumakansu,
Ni kuma zan sa su su yi kishi da waɗanda suke ba mutane ba.
Zan tsokane su da wawanyar al'umma.
22Gama fushina ya kama wuta,
Tana ci har ƙurewar zurfin lahira.
Za ta cinye duniya da dukan amfaninta,
Za ta kama tussan duwatsu.
23“ ‘Zan tula musu masifu,
Zan ƙare kibauna a kansu,
24Za su lalace saboda yunwa,
Zazzaɓi mai zafi, da muguwar annoba za su cinye su.
Zan aika da haƙoran namomi a kansu,
Da dafin abubuwa masu jan ciki.
25Waɗanda suke a waje, takobi zai kashe su,
A cikin ɗakuna kuma tsoro,
Zai hallaka saurayi da budurwa,
Da mai shan mama da mai furfura.
26Na ce, zan watsar da su,
in sa a manta da su cikin mutane.
27Amma saboda gudun tsokanar maƙiyi,
Kada abokan gābansu su zaci su ne suka ci nasara.
Ai, ni ne na yi wannan.’
28“Gama su al'umma ce wadda ba ta yin shawara,
Ba su da ganewa.
29Da suna da hikima, da sun gane wannan,
Da za su gane da yadda ƙarshensu zai zama!
30Ƙaƙa mutum ɗaya zai runtumi dubu,
Mutum biyu kuma su kori zambar goma,
Sai dai Dutsensu ya sayar da su,
Ubangiji kuma ya bashe su?
31Gama dutsensu ba kamar Dutsenmu ba ne,
Ko abokan gabanmu ma sun san haka.
32Kurangar inabinsu daga kurangar inabin Saduma ne
Da gonakin Gwamrata.
'Ya'yan inabinsu dafi ne,
Nonnansu masu ɗaci ne.
33Ruwan inabinsu dafin macizai ne.
Da mugun dafin kumurci.
34“ ‘Wannan ba a jibge suke a rumbunana ba,
A ƙulle kuma a taskokina?
35 #
Rom 12.19; Ibr 10.30 Sakayya da ɗaukar fansa nawa ne,
A lokacin ƙafarsu za ta zame,
Gama ranar masifarsu ta kusa,
Hallakarsu za ta zo da sauri.’
36 #
Zab 135.14
Ubangiji zai ɗauka wa jama'arsa fansa,
Zai ji ƙan bayinsa,
Sa'ad da ya ga ƙarfinsu ya kāsa,
Ba kuma wanda ya ragu, bawa ko ɗa.
37Sa'an nan zai ce, ‘Ina gumakansu,
Dutse wanda suka nemi mafaka gare shi,
38Waɗanda suka ci kitsen hadayunsu,
Suka sha ruwan inabin hadayarsu ta sha?
Bari su tashi su taimake ku,
Bari su zama mafaka!
39“ ‘Ku duba fa, ni ne shi,
Ba wani Allah, banda ni,
Nakan kashe, in rayar,
Nakan sa rauni, nakan kuma warkar,
Ba wanda zai cece su daga hannuna.
40Na ɗaga hannuna sama,
Na rantse da madawwamin raina,
41Sa'ad da na wasa takobina mai walƙiya,
Na riƙe shi da hannuna don yin hukunci,
Zan ɗauki fansa a kan magabtana
Zan sāka wa maƙiyana.
42Zan sa kibauna su bugu da jini,
Takobina zai ci nama,
Da jinin kisassu da na kamammu,
Da ƙoƙon kan shugabannin maƙiya.’
43 #
Rom 15.10; W.Yah 19.2 “Ya ku al'ummai, ku yabi jama'arsa,
Gama zai rama wa bayinsa saboda jininsu,
Zai ɗauki fansa a kan magabtansa,
Zai tsarkake ƙasar jama'arsa.”
Gargaɗin Musa na Ƙarshe
44Sai Musa da Joshuwa ɗan Nun suka zo, suka hurta dukan kalmomin wannan waƙa a kunnen jama'a.
45Sa'ad da Musa ya gama hurta waɗannan kalmomi ga Isra'ila, 46ya ce musu, “Ku riƙe dukan waɗannan kalmomi a zuciyarku, waɗanda nake yi muku kashedi da su a yau don ku umarci 'ya'yanku su kiyaye dukan maganar dokokin nan sosai. 47Wannan ba magana kurum ba ce, amma ranku ne. Ta wurin wannan magana ce za ku yi tsawon rai a ƙasar da za ku haye Urdun zuwa ciki don ku mallake ta.”
An Yarda wa Musa Ya Hangi Ƙasar Kan'ana
48 #
L.Ƙid 27.12-14; M.Sh 3.23-27 A wannan rana ce Ubangiji ya ce wa Musa, 49“Ka hau duwatsun Abarim, wato Dutsen Nebo wanda yake a ƙasar Mowab, daura da Yariko, ka duba ƙasar Kan'ana wadda zan ba Isra'ilawa su mallaka. 50Za ka rasu a kan dutsen da za ka hau, za a kai ka wurin mutanen da suka riga ka gidan gaskiya, kamar yadda ɗan'uwanka, Haruna, ya rasu a Dutsen Hor, aka kai shi wurin mutanensa waɗanda suka riga shi gidan gaskiya. 51Gama ba ku amince da ni ba a gaban mutanen Isra'ila a wurin ruwan Meriba ta Kadesh a jejin Zin a wannan lokaci, domin ba ku nuna tsarkina a gaban jama'ar Isra'ila ba. 52Za ka ga ƙasar da nake ba jama'ar Isra'ila, amma ba za ka shiga cikinta ba.”
Currently Selected:
M.Sh 32: HAU
Highlight
Copy
Compare
Share
Want to have your highlights saved across all your devices? Sign up or sign in
@Bible Society of Nigeria 1979