YouVersion Logo
Search Icon

2Yah 1

1
Gaisuwa
1Daga dattijon nan na ikkilisiya zuwa ga uwargida zaɓaɓɓiya, da 'ya'yanta waɗanda nake ƙauna da gaske, ba kuwa ni kaɗai ba, har ma dukan waɗanda suka san gaskiya, 2wato, muna ƙaunarku saboda gaskiyar da take a dawwame a cikinmu, za ta kuwa kasance tare da mu har abada.
3Alheri, da jinƙai, da salama na Allah Uban, da kuma na Yesu Almasihu Ɗan Uban, za su tabbata a gare mu, da gaskiya da ƙauna.
Ku Zauna Cikin Koyarwar Almasihu
4Na yi farin ciki ƙwarai da samun waɗansu 'ya'yanki suna bin gaskiya, kamar yadda Uba ya ba mu umarni. 5#Yah 13.34; 15.12,17 Yanzu kuma ina roƙonki, uwargida, ba cewa wani sabon umarni nake rubuto miki ba, sai dai wanda muke da shi tun farko ne, cewa mu ƙaunaci juna. 6Ƙauna kuwa ita ce mu bi umarninsa. Umarnin kuwa, shi ne kamar yadda kuka ji tun farko, cewa ku yi zaman ƙauna. 7Gama masu ruɗi da yawa sun fito duniya, waɗanda ba sa bayyana yarda, cewa Yesu Almasihu ya bayyana da jiki, irin wannan shi ne mai ruɗi, magabcin Almasihu. 8Ku kula da kanku don kada ku yar da aikin da muka yi, amma dai ku sami cikakken sakamako. 9Kowa ya yi ƙari, bai tsaya a kan koyarwar Almasihu ba, Allah ba ya tare da shi ke nan. Wanda kuwa ya tsaya a kan koyarwar nan, yana da uba da Ɗan. 10Kowa ya zo gare ku, bai kuwa zo da wannan koyarwa ba, kada ku karɓe shi a gidanku, ko maraba ma kada ku yi masa. 11Don duk wanda ya yi masa maraba, mugun aikinsa, sai yă shafe shi.
Gaisuwa
12Ko da yake ina da abin da zan faɗa muku da yawa, na gwammace ba a wasiƙa ba, amma na sa zuciya in ziyarce ku, mu yi magana baka da baka. don farin cikinmu ya zama cikakke.
13'Ya'yan 'yar'uwarki zaɓaɓɓiya suna gaishe ki.

Currently Selected:

2Yah 1: HAU

Highlight

Share

Copy

None

Want to have your highlights saved across all your devices? Sign up or sign in

YouVersion uses cookies to personalize your experience. By using our website, you accept our use of cookies as described in our Privacy Policy