YouVersion Logo
Search Icon

3Yah 1

1
Gaisuwa
1 # A.M 19.29; Rom 16.23; 1Kor 1.14 Daga dattijon nan na ikkilisiya zuwa ga Gayus, ƙaunatacce, wanda nake ƙauna da gaske.
2Ya ƙaunataccena, ina addu'a kă sami zaman lafiya ta kowace hanya da kuma lafiya jiki, kamar yadda ruhunka yake a zaune lafiya. 3Na yi farin ciki ƙwarai sa'ad da waɗansu 'yan'uwa suka zo suka shaida gaskiyarka, yadda hakika kake bin gaskiya. 4Ba abin da ya fi faranta mini rai kamar in ji 'ya'yana suna bin gaskiya.
Yaba Kirkin Gayus
5Ya ƙaunataccena, duk abin da kake yi wa 'yan'uwa, aikin bangaskiya kake yi, tun ba ma ga baƙi ba. 6Su ne suka shaida ƙaunarka a gaban ikkilisiya. Zai kyautu ka raka su a guzuri, kamar yadda ya cancanci bautar Allah, 7domin saboda sunan nan ne suka fito, ba sa kuma karɓar kome daga al'ummai. 8Domin haka ya kamata mu karɓi irin mutanen nan, mu ɗau nauyinsu, domin mu zama abokan aiki da su a kan gaskiya.
Diyotarifis Mai Ƙin Bin Magana
9Na yi wa ikkilisiya 'yar wasiƙa, amma shi Diyotarifis wanda yake so ya fi kowa a cikinsu, ya ƙi bin maganarmu. 10Saboda haka, in na zo zan tabbatar masa da abin da yake yi, yana surutu game da mu, yana ɓaɓɓata mu. Wannan ma bai ishe shi ba, har ya ƙi yi wa 'yan'uwa maraba, yana kuma hana masu so su marabce su, yana fitar da su daga ikkilisiya.
Kyakkyawar Shaida kan Dimitiriyas
11Ya ƙaunataccena, kada ka kwaikwayi mugun aiki, sai dai nagari. Kowa da yake aikin nagari na Allah ne. Mai mugun aiki kuwa bai san Allah ba sam. 12Dimitiriyas yana da kyakkyawar shaida a gun kowa, har gaskiya kanta ma tana yi masa shaida. Mu ma mun shaide shi, ka kuwa san shaidarmu tabbatacciya ce.
Gaisuwa
13Dā kam, ina da abin da zan rubuto maka da yawa, amma yanzu na gwammace kada in rubuto a wasiƙa. 14Ina sa zuciya mu sadu ba da daɗewa ba, sa'an nan ma yi magana baka da baka.
15Salama tă tabbata gare ku. Aminanmu suna gaishe ka. Ka gai da aminanmu kowa da kowa.

Currently Selected:

3Yah 1: HAU

Highlight

Share

Copy

None

Want to have your highlights saved across all your devices? Sign up or sign in

YouVersion uses cookies to personalize your experience. By using our website, you accept our use of cookies as described in our Privacy Policy