2Tim 4
4
1Na gama ka da Allah, da kuma Almasihu Yesu, wanɗa zai yi wa rayayyu da matattu shari'a, na kuma gargaɗe ka saboda bayyanarsa da kuma mulkinsa, 2ka yi wa'azin Maganar Allah, ka dimanta a kai ko da yaushe, kana shawo kan mutane, kana tsawatarwa, kana ƙarfafa zukata, a game da matuƙar haƙuri da kuma koyarwa. 3Don lokaci zai zo da mutane ba za su jure sahihiyar koyarwa ba, amma saboda kunnensu yana ƙaiƙayi, sai su taro masu koyarwa da za su biya musu muradinsu. 4Za su toshe kunnensu ga jin tatsuniyoyi. 5Kai kuwa, sai ka natsu a cikin kowane hali, ka jure wa shan wuya, kana aikin mai bishara, ka cika hidimarka.
6Ni fa tsiyaye ni ake yi kamar hadaya, lokacin ƙauracewata kuma ya gabato. 7Na sha fama, famar gaske, na gama tseren, na riƙe bangaskiya. 8Saura kuwa, sai sakamakon nan na aikin adalci, da aka tanadar mini, wanda Ubangiji, mahukunci mai adalci, zai ba ni a ranar nan, ba kuwa ni kaɗai ba, har da duk waɗanda suke ɗokin ganin bayyanarsa.
Waɗansu Umarnai
9Ka yi matuƙar ƙoƙari ka zo wurina da hanzari, 10#Kol 4.14; Fil 1.24; 2Kor 8.23; Gal 2.3; Tit 1.4 domin Dimas, saboda ƙaunar duniyar nan, ya yashe ni, ya tafi Tasalonika. Karaska ya tafi ƙasar Galatiya, Titus kuma ya tafi ƙasar Dalmatiya. 11#Kol 4.14; Fil 1.24; A.M 12.12,25; 13.13; 15.37-39; Kol 4.10; Fil 1.24 Luka ne kaɗai yake tare da ni. Ka ɗauko Markus ku zo tare, gama yana da amfani a gare ni a wajen yi mini hidima. 12#A.M 20.4; Afi 6.21,22; Kol 4.7,8 Tikikus kuwa na aike shi Afisa. 13#A.M 20.6Sa'ad da za ka taho, ka zo da alkyabbar nan da na bari a wurin Karbus a Taruwasa, da kuma littattafan nan, tun ba ma fatun nan masu rubutu ba. 14#1Tim 1.20; Zab 62.12; Rom 2.6 Iskandari maƙerin farfarun nan ya yi mini mugunta ƙwarai, Ubangiji zai yi masa sakayyar aikinsa. 15Kai ma, ka mai da hankali da shi, gama ya hauri maganarmu, mummunan hauri. 16A lokacin da na ba da hanzarina na farko, ba wanda ya goyi bayana, sai duk suka yashe ni. Ina fata ba za a lasafta wannan laifi a kansu ba. 17Amma Ubangiji ya tsaya tare da ni, ya ba ni ƙarfin sanar da bishara sosai da sosai, domin duk al'ummai su ji, aka kuwa cece ni daga bakin zaki. 18Ubangiji zai cece ni daga kowane mugun abu, ya kuma kiyaye ni, ya kai ni ga Mulkinsa na Sama. Ɗaukaka tă tabbata a gare shi har abada abadin. Amin! Amin!
Gaisuwa
19 #
A.M 18.2;
2Tim 1.16,17 Ka gayar mini da Bilkisu da Akila, da mutanen gidan Onisifaras. 20#A.M 19.22; Rom 16.23; A.M 20.4; 21.29 Aratas ya dakata a Koranti. Tarofimas kuwa na bar shi a Militas, ba shi da lafiya. 21Ka yi matuƙar ƙoƙari ka zo kafin damuna. Aubulus yana gaishe ka, da Budis, da Linas, da Kalaudiya, da kuma dukkan 'yan'uwa.
22Ubangiji yă kasance a zuciyarka. alheri yă tabbata a gare ku.
Currently Selected:
2Tim 4: HAU
Highlight
Share
Copy
Want to have your highlights saved across all your devices? Sign up or sign in
@Bible Society of Nigeria 1979