YouVersion Logo
Search Icon

2Tim 3

3
Halin Ƙarshen Zamani
1Amma ka fahimta, a zamanin ƙarshe za a sha wuya ƙwarai. 2Mutane za su zama masu sonkai, da masu son kuɗi, da masu ruba, da masu girmankai, da masu zagezage, da marasa bin iyayensu, da masu butulci, da marasa tsarkaka, 3da marasa ƙauna, da masu riƙo a zuci, da masu yanke, da fajirai, da maƙetata, da maƙiyan nagarta, 4da maciya amana, da masu taurinkai, da masu homa, da masu son annashuwa fiye da son Allah, 5suna riƙe da siffofin ibada, amma suna sāɓa wa ikonta. Ka yi nesa da irin waɗannan mutane. 6A cikinsu kuwa akwai masu saɗaɗawa su shiga gidajen mutane, suna rinjayar mata marasa wayo, waɗanda zunubi ya sha kansu, muguwar sha'awa iri iri kuma ta ɗauke musu hankali, 7kullum suna koyo, amma kullum sai su kāsa kaiwa ga sanin gaskiya. 8#Fit 7.11 Kamar yadda Yanisu da Yambirisu suka tayar wa Musa, haka mutanen nan kuma suke tayar wa gaskiya, mutane ne masu ɓataccen hankali ƙwarai, bangaskiyarsu kuwa ta banza ce. 9Amma ba za su yi nisa ba, don rashin hankalinsu zai bayyana ga kowa, kamar na mutanen nan biyu.
Gargaɗin Bulus ga Timoti na Ƙarshe
10Kai kam, ka riga ka kiyaye koyarwata, da halina, da niyyata, da bangaskiyata, da haƙurina, da ƙaunata, da jimirina, 11#A.M 13.14-52; A.M 14.1-7; A.M 14.8-20 da kuma yawan tsanani, da wuyar da na sha, da suka same ni a Antakiya, da Ikoniya, da Listira, wato irin tsanance-tsanancen da na jure. Amma Ubangiji ya kuɓutar da ni daga cikinsu duka. 12Labudda, duk masu niyyar zaman tsarkaka, suna ga Almasihu Yesu, za su sha tsanani. 13Mugayen mutane da masu ruɗi kuwa, ƙara muni za su riƙa yi, suna yaudara, ana kuma yaudararsu. 14Amma kai kuwa, ka zauna a kan abin da ka koya, ka kuma haƙƙaƙe, gama ka san wurin waɗanda ka koye su, 15da kuma yadda tun kana ɗan ƙaramin yaro ka san Littattafai masu tsarki, waɗanda suke koya maka hanyar samun ceto ta dalilin bangaskiya ga Almasihu Yesu. 16Kowane Nassi hurarre na Allah ne, mai amfani ne kuma wajen koyarwa, da tsawatarwa, da gyaran hali, da kuma tarbiyyar aikin adalci, 17domin bawan Allah yă zama cikakke, shiryayye sosai ga kowane kyakkyawan aiki.

Currently Selected:

2Tim 3: HAU

Highlight

Share

Copy

None

Want to have your highlights saved across all your devices? Sign up or sign in