YouVersion Logo
Search Icon

2Sar 13

13
Sarki Yehowahaz na Isra'ila
1A shekara ta ashirin da uku ta sarautar Yowash ɗan Ahaziya Sarkin Yahuza, Yehowahaz ɗan Yehu ya ci sarautar Isra'ila a Samariya. Ya yi mulki shekara goma sha bakwai. 2Ya aikata mugunta a gaban Ubangiji, gama ya aikata irin zunuban Yerobowam ɗan Nebat, wanda ya sa Isra'ilawa su yi zunubi. Bai rabu da zunuban Yerobowam ba. 3Ubangiji kuwa ya husata da jama'ar Isra'ila, sai ya dinga ba da su a hannun Hazayel Sarkin Suriya, da hannun Ben-hadad ɗan Hazayel. 4Sai Yehowahaz ya roƙi Ubangiji, Ubangiji kuwa ya ji shi, gama ya ga wahalar da Isra'ilawa suke ciki, wato yadda Sarkin Suriya yake musguna musu. 5Saboda haka Ubangiji ya ba jama'ar Isra'ila maceci, suka kuwa kuɓuta daga ƙangin Suriyawa, suka zauna a gidajensu lafiya kamar dā. 6Duk da haka ba su rabu da zunuban gidan Yerobowam ba, wanda ya sa mutanen Isra'ila su yi zunubi. Sun aikata irin zunuban Yerobowam. Gunkiyan nan mai suna Ashtoret tana nan a Samariya.
7Rundunar Yehowahaz kuwa ba ta fi mahaya hamsin, da karusai goma, da dakarai dubu goma (10,000) ba, gama Sarkin Suriya ya hallaka rundunar, ya yi kaca kaca da ita kamar ƙura a masussuka.
8Sauran ayyukan Yehowahaz da dukan abin da ya yi, da ƙarfinsa, an rubuta su a littafin tarihin sarakunan Isra'ila. 9Yehowahaz kuwa ya rasu, aka binne shi a Samariya. Yehowash ɗansa ya gāji sarautarsa.
Sarki Yehowash na Isra'ila
10A shekara ta talatin da bakwai ta sarautar Yowash Sarkin Yahuza, Yehowash ɗan Yehowahaz ya ci sarautar Isra'ila a Samariya. Ya yi shekara goma sha shida yana sarauta. 11Ya aikata mugunta a gaban Ubangiji. Bai rabu da dukan zunubin Yerobowam ɗan Nebat ba, wanda ya sa jama'ar Isra'ila su yi zunubi. Ya bi halin Yerobowam ɗan Nebat. 12Sauran ayyukan Yehowash da dukan abin da ya yi, da irin ƙarfin da ya yi yaƙi da Amaziya Sarkin Yahuza, an rubuta su a littafin tarihin sarakunan Isra'ila.2Sar 14.15; 1Sar 15.31 13Yehowash kuwa ya mutu, aka binne shi a Samariya, inda ake binne sarakunan Isra'ila, sai Yerobowam na biyu ya gāji gadon sarautarsa.
Annabi Elisha Ya Rasu
14 # 2Sar 2.12 Da Elisha ya kamu da ciwon ajali, sai Yehowash Sarkin Isra'ila ya tafi wurinsa, ya yi kuka a gabansa, yana cewa, “Ubana, Ubana, karusar Isra'ila da mahayan dawakanta!”
15Elisha kuwa ya ce masa, “Ka ɗauki baka da kibau.” Shi kuwa ya ɗauka. 16-17Sa'an nan ya ce, “Ka buɗe tagar da take wajen gabas.” Sai ya buɗe. Elisha ya kuma ce masa, “Ka ja bakan.” Ya kuwa ja. Sai Elisha ya ɗora hannuwansa a bisa hannuwan sarki. Sa'an nan Elisha ya ce, “Harba.” Sai ya harba. Elisha kuwa ya ce, “Kibiyar Ubangiji ta nasara, kibiyar nasara a kan Suriya. Gama za ka yi yaƙi da Suriyawa a Afek har ka ci su.”
18Sa'an nan ya ce, “Ka ɗauki kibau.” Shi kuwa ya ɗauka. Sai ya ce wa Sarkin Isra'ila, “Ka caki ƙasa da su.” Sai ya caka har sau uku, sa'an nan ya tsaya. 19Elisha kuwa ya husata, ya ce, “Da ma ka caka sau biyar ko shida da za ka yi nasara a kan Suriyawa har ka ci su sarai, amma yanzu za ka yi nasara da su sau uku kawai.”
20Elisha kuwa ya rasu, aka binne shi.
Maharan Mowabawa sukan kawo yaƙi a ƙasar da bazara. 21Wata rana ana binne gawa, sai aka ga mahara, aka jefar da gawar a cikin kabarin Elisha. Da gawar ta taɓi ƙasusuwan Elisha, sai ya farko ya tashi ya miƙe tsaye.
Yaƙi tsakanin Isra'ila da Suriya
22Hazayel Sarkin Suriya kuwa ya musguna wa jama'ar Isra'ila a dukan zamanin Yehowahaz. 23Amma Ubangiji ya nuna musu alheri, ya ji tausayinsu, bai ba su baya ba saboda alkawarinsa da Ibrahim, da Ishaku, da Yakubu. Bai yarda ya hallaka su ba, bai kuma yi watsi da su ba har wa yau.
24Da Hazayel Sarkin Suriya ya rasu, sai Ben-hadad ɗansa ya gāji sarautarsa. 25Sai Yehowash ɗan Yehowahaz ya ƙwace daga hannun Ben-hadad, ɗan Hazayel, biranen da Ben-hadad ya ci da yaƙi daga hannun Yehowahaz, tsohonsa. Sau uku Yehowash ya ci shi da yaƙi, sa'an nan ya karɓe biranen Isra'ila.

Currently Selected:

2Sar 13: HAU

Highlight

Share

Compare

Copy

None

Want to have your highlights saved across all your devices? Sign up or sign in