2Sar 12
12
1A shekara ta bakwai ta sarautar Yehu, Yowash ya ci sarautar. Ya yi shekara arba'in yana sarauta a Urushalima. Sunan tsohuwarsa Zibiya ta Biyer-sheba. 2Yowash kuwa ya yi abin da yake daidai ga Ubangiji dukan kwanakinsa, domin Yehoyaka, firist, ya koya masa. 3Duk da haka ba a kawar da wuraren yin tsafi a tuddai ba, mutane suka ci gaba da miƙa hadayu da ƙona turare a kan tuddan.
4 #
Fit 30.11-16
Yowash ya ce wa firistoci, “Dukan kuɗin tsarkakan abubuwa da ake kawowa a Haikalin ubangiji, da kuɗin da aka tsara wa kowane mutum, da kuɗin da aka bayar da yardar rai, da ake kawowa a Haikali, 5sai ku karɓa daga junanku, don a gyara duk inda ake bukatar gyara a Haikalin.”
6Amma har a shekara ta ashirin da uku ta sarautar sarki Yowash, firistocin ba su yi wani gyara a Haikalin ba. 7Saboda haka Yowash ya kirawo Yehoyada, firist, da sauran firistoci, ya ce musu, “Me ya sa ba ku gyara Haikalin? Daga yanzu kada ku karɓi kuɗi daga wurin abokanku, sai in za ku ba da shi domin gyaran Haikalin.” 8Firistocin kuwa suka yarda, ba za su karɓi kuɗi daga wurin jama'a ba, ba su kuwa gyara Haikalin ba.
9Sa'an nan Yehoyada, firist, ya ɗauki akwati, ya huda rami a murfin, sa'an nan ya ajiye shi kusa da bagade a sashin dama na shiga Haikalin Ubangiji. Firistocin da suke tsaron ƙofar suka saka dukan kuɗin da aka kawo a Haikalin Ubangiji. 10Sa'ad da suka gani akwai kuɗi da yawa a cikin akwatin, sai magatakardan sarki, da babban firist suka zo, suka ƙirga kuɗin da yake a Haikalin Ubangiji suka ƙunsa shi a babbar jaka. 11Sa'an nan suka ba da kuɗin da aka ƙirga a hannun waɗanda suke lura da aikin Haikalin Ubangiji, domin su biya masassaƙan katakai, da masu haɗawa da suke aikin Haikalin Ubangiji, 12da masu gini, da masu sassaƙa duwatsu, a kuma sayi katako da sassaƙaƙƙun duwatsu don gyaran Haikalin Ubangiji, da kowane irin abu da ake bukata domin gyaran Haikalin. 13Amma ba a mori kuɗin da aka kawo a Haikalin Ubangiji domin yin kwanonin azurfa, da abin katse fitila, da tasoshi, da ƙahoni, da kwanonin zinariya ko na azurfa ba. 14Gama an ba da kuɗin ga ma'aikatan da suke gyaran Haikalin ubangiji. 15#2Sar 22.7 Ba a nemi lissafin kuɗin a wurin mutanen da aka ba su kuɗin don su biya ma'aikatan ba, gama su amintattu ne. 16#L.Fir 7.7 Ba a kawo kuɗi na hadaya don laifi da hadaya don zunubi a cikin Haikalin Ubangiji ba, ya zama na firistoci.
17Hazayel Sarkin Suriya kuwa ya tafi ya yi yaƙi da Gat har ya cinye ta, ya kuma shirya zai yi yaƙi da Urushalima. 18Sai Yowash Sarkin Yahuza ya kwashe dukan kyautai na yardar rai waɗanda Yehoshafat, da Yoram, da Ahaziya, kakanninsa, sarakunan Yahuza suka keɓe, ya kuma kwashe kyauta ta yardar rai ta kansa, da dukan zinariya da aka samu a baitulmalin Haikalin Ubangiji da baitulmalin gidan sarki, ya aika wa Hazayel, Sarkin Suriya. Sa'an nan Hazayel ya tashi ya bar Urushalima.
19Sauran ayyukan Yowash da dukan abin da ya yi, an rubuta su a littafin tarihin sarakunan Yahuza.
20Fādawansa suka ƙulla maƙarƙashiya, suka kashe shi a gidan da yake Millo, a kan hanyar da ta nufi Silla. 21Yozakar ɗan Shimeyat, da Yehozabad ɗan Shemer su ne fādawansa da suka kashe shi. Aka binne shi a makabartar kakanninsa cikin birnin Dawuda. Amaziya ɗansa ya gāji sarautarsa.
Currently Selected:
2Sar 12: HAU
Highlight
Share
Compare
Copy
Want to have your highlights saved across all your devices? Sign up or sign in
@Bible Society of Nigeria 1979