YouVersion Logo
Search Icon

2Tar 4

4
1 # Fit 27.1,2 Ya yi bagade na tagulla, tsawonsa kamu ashirin ne, fāɗinsa kuma kamu ashirin, tsayinsa kuwa kamu goma. 2Ya yi kwatarniya kewayayyiya ta zubi, kamu goma daga gāɓa zuwa gāɓa, tsayinsa kuwa kamu biyar ne, da'irarsa kuwa kamu talatin. 3A ƙashiyar kwatarniya akwai siffofin bijimai kamu goma kewaye da ita har jeji biyu. Gaba ɗaya aka yi zubinsu da na kwatarniya. 4Kwatarniya tana bisa bijimai goma sha biyu, uku suna fuskantar gabas, uku suna fuskantar yamma, uku suna fuskantar kudu, uku kuma suna fuskantar arewa. Kwatarniya tana bisa bijiman, gindin kowannensu yana daga ciki. 5Kaurin kwatarniya taƙi guda ne, bakinsa kamar bakin finjali ne, kamar kuma siffar furen bi-rana. Kwatarniya kuwa tana iya ɗaukar fiye da garwa dubu uku na ruwa. 6#Fit 30.17-21 Ya kuma yi daro goma na wanki, ya ajiye biyar a wajen kudu, biyar kuma a wajen arewa, don a riƙa ɗauraye abubuwan da ake hadayar ƙonawa da su. Amma kwatarniya don firistoci su riƙa wanka a ciki ne.
7 # Fit 25.31-40 # Fit 25.23-30 Sa'an nan ya yi alkuki goma na zinariya kamar yadda aka tsara. Ya sa su cikin Haikali, biyar a sashen dama, biyar kuma a hagu. 8Ya kuma yi tebur goma, ya ajiye a cikin Haikalin, biyar a dama, biyar kuma a hagu. Ya kuma yi kwanonin zinariya guda ɗari.
9Sa'an nan ya yi wani shirayi domin firistoci, ya kuma yi wani babban shirayi, ya yi ƙofofi domin shirayun. Ya dalaye ƙyamaren ƙofofin da tagulla. 10Ya girka kwatarniya a kusurwar kudu maso gabas daura da Haikalin.
11-16Huram kuma ya yi tukwanen ƙarfe, da manyan cokula, da daruna. Huram kuwa ya gama dukan aikin da ya alkawarta wa sarki Sulemanu a Haikalin Allah:
ginshiƙi biyu
dajiya biyu a kan ginshiƙi biyu
siffar tukakkiyar sarƙa a kan kowane ginshiƙi
Siffar rumman guda ɗari huɗu domin raga don rufe dajiyar ginshiƙan
dakali goma
daro goma
kwatarniya.
Bijimi goma sha biyu da suke ɗauke da kwatarniya kwanoni, manyan cokula masu yatsotsi, wato ya yi dukan kayan nan da tagulla domin Haikalin Ubangiji.
17Sarki ya yi zubinsu a filin Urdun tsakanin Sukkot da Zaretan a wuri mai yumɓu. 18Haka Sulemanu ya yi kayayyakin nan da yawa ƙwarai, har ba a iya lissafin yawan nauyin tagullar da aka yi amfani da ita ba.
19-22Haka kuwa Sulemanu ya yi dukan kayayyakin nan da suke cikin Haikalin Allah, duk da zinariya tsantsa aka yi su.
bagade na zinariya
tebur don ajiye gurasar ajiyewa
alkukai tare da fitilunsu na zinariya tsantsa, domin a kunna su a gaban Wuri Mafi Tsarki na ciki kamar yadda aka tsara
furanni
fitilu
arautaki
hantsuka
daruna
cokula
farantan wuta
ƙofofi na can ciki
ƙofofi na waje.

Currently Selected:

2Tar 4: HAU

Highlight

Share

Compare

Copy

None

Want to have your highlights saved across all your devices? Sign up or sign in