2Tar 3
3
Sulemanu Ya Gina Ɗakin Sujada domin Ubangiji
(1Sar 6.1-38)
1 #
Far 22.22
Sulemanu kuwa ya fara ginin Haikalin Ubangiji a Urushalima a kan Dutsen Moriya, inda Ubangiji ya taɓa bayyana ga tsohonsa Dawuda, inda kuma Dawuda ya riga ya shirya a daidai masussukar Arauna Bayebuse. 2Ya fara ginin a ran biyu ga watan biyu a shekara ta huɗu ta sarautarsa. 3Ga awon harsashin da Sulemanu ya kafa domin ginin Haikalin Ubangiji. Tsawonsa bisa ga tsohon magwajin, kamu sittin ne, fāɗin kuwa kamu ashirin. 4Tsawon shirayi daga gaban Haikalin ya yi daidai da fāɗin Haikalin, wato kamu ashirin, sa'an nan tsayinsa kamu ɗari da ashirin. Aka shafe ciki da zinariya tsantsa. 5Ya jera itatuwan fir a cikin babban ɗakin, sa'an nan ya shafe su da zinariya tsantsa, ya kuma zana siffofin itatuwan dabino da na sarƙoƙi. 6Banda wannan kuma ya ƙawata Haikalin da duwatsu masu daraja da zinariya irin ta Farwayim. 7Ya kuma shafe Haikalin duk da ginshiƙansa, da bakin ƙofofinsa, da bangayensa, da ƙyamarensa da zinariya, ya kuma zana siffofin kerubobi a jikin bangaye. 8#Fit 26.33,34 Sai ya gina Wuri Mafi Tsarki. Tsawonsa daidai da fāɗin Haikalin, wato kamu ashirin, fāɗinsa kuma kamu ashirin. Ya shafe shi da zinariya tsantsa, wadda jimillar nauyinta ta yi talanti ɗari shida. 9Nauyin ƙusoshin ya kai shekel hamsin na zinariya. Ya kuma shafe benaye da zinariya tsantsa.
10 #
Fit 25.18-20
Ya sassaƙa siffofin kerubobi biyu na itace, a Wuri Mafi Tsarki, ya shafe su da Zinariya. 11Tsawon fikafikan kerubobin duka kamu ashirin ne, fiffike ɗaya, kamu biyar, ya taɓo bangon ɗakin, ɗaya fiffiken kuma wanda shi ma kamu biyar ne, ya taɓo fiffiken kerub ɗaya ɗin. 12Guda kerub ɗin kuma, fiffikensa guda ya taɓo bangon ɗakin, ɗaya fiffiken shi ma ya taɓo fiffiken kerub na farko. 13Tsawon fikafikan kerubobin ya kai kamu ashirin. Su kerubobin a tsaye suke, suna fuskantar babban ɗakin. 14#Fit 26.31 Sai ya yi labule mai launin shuɗi, da shunayya, da garura, da lilin mai kyau, sa'an nan ya zana siffofin kerubobin a jikin labulen.
Kayan Haikali
(1Sar 7.15-51)
15Ya kuma yi ginshiƙai biyu domin ƙofar Haikalin, tsayinsu kamu talatin da biyar ne, ya yi wa ginshiƙan dajiya, tsayin kowace dajiya kamu biyar ne. 16Ya yi sarƙoƙi, ya rataya wa ginshiƙan, ya kuma yi siffofin rumman guda ɗari, ya maƙala wa sarƙoƙin. 17Sai ya kafa ginshiƙin a ƙofar Haikali, ɗaya a wajen kudu, ɗaya kuma a wajen arewa. Ya sa wa na wajen kudu suna Yakin, na wajen arewa kuwa Bo'aza.
Currently Selected:
2Tar 3: HAU
Highlight
Share
Compare
Copy
Want to have your highlights saved across all your devices? Sign up or sign in
@Bible Society of Nigeria 1979