2Tar 30
30
Yin Idin Ƙetarewa
1 #
L.Ƙid 9.9-11
Sai Hezekiya ya aika zuwa ga dukan Isra'ila da Yahuza, ya kuma rubuta wasiƙu zuwa ga Ifraimu, da Manassa, cewa sai su zo Haikalin Ubangiji a Urushalima, domin su yi Idin Ƙetarewa na Ubangiji Allah na Isra'ila. 2Gama sarki da sarakunansa da dukan majalisar da take a Urushalima sun tsai da shawara a yi Idin Ƙetarewa a wata na biyu, 3gama ba su iya yinsa a lokacinsa ba, saboda yawan firistocin da suka tsarkake kansu bai isa ba, mutane kuma ba su taru a Urushalima ba. 4A ganin sarki da na jama'a duka, shirin ya yi daidai. 5Sai suka ba da umarni a yi shela a Isra'ila duka, tun daga Biyer-sheba, har zuwa Dan, cewa sai mutane su zo Idin Ƙetarewa na Ubangiji Allah na Isra'ila a Urushalima, gama jama'a mai yawan gaske ba su zo wurin yin idin kamar yadda aka umarta ba. 6Sai mazanni suka tafi ko'ina da ina a dukan ƙasar Isra'ila da ta Yahuza da wasiƙu daga wurin sarki da sarakunansa, yadda sarki ya umarta.
“Ya ku jama'ar Isra'ila, ku komo wurin Ubangiji Allah na Ibrahim, da Ishaku, da Isra'ila domin ya sāke juyowa zuwa ga sauranku, waɗanda kuka kuɓuta daga hannun sarakunan Assuriya. 7Kada fa ku zama kamar kakanninku ko 'yan'uwanku, marasa bangaskiya ga Ubangiji Allah na kakanninsu, saboda haka ya maishe su kufai kamar yadda kuka gani. 8Kada ku yi taurin kai kamar yadda kakanninku suka yi, amma ku miƙa kanku ga Ubangiji, ku zo Wuri Mai Tsarki, wanda ya tsarkake har abada, ku bauta wa Ubangiji Allahnku, domin ya huce daga zafin fushin da yake yi da ku. 9Gama idan kun juyo zuwa ga Ubangiji, 'yan'uwanku da 'ya'yanku za su sami rahamar waɗanda suka kama su, su komo wannan ƙasa. Gama Ubangiji Allahnku mai alheri ne, mai jinƙai, ba zai kawar da fuskarsa daga gare ku ba, idan kun komo gare shi.”
10Manzannin fa suka tafi gari gari a ƙasar Ifraimu, da ta Manassa, har zuwa Zabaluna, amma suka yi musu dariyar raini, suka yi musu ba'a. 11Sai mutane kaɗan na Ashiru, da na Manassa, da na Zabaluna suka yi tawali'u, suka zo Urushalima. 12Ikon Allah kuma yana kan Yahuza, ya ba su zuciya ɗaya ta su yi abin da sarki da sarakunansa suka umarta bisa ga maganar Ubangiji.
13Mutane da yawa kuwa suka zo Urushalima don su yi idin abinci marar yisti a wata na biyu, aka yi babban taro. 14Sai suka kama aiki, suka kawar da bagadan da suke cikin Urushalima, da dukan bagadan ƙona turare suka kwashe suka zubar a kwarin Kidron. 15Suka yanka ɗan rago na Idin Ƙetarewa a rana ta sha huɗu ga wata na biyu. Suka sa firistoci da Lawiyawa su sha kunya, saboda haka sai suka tsarkake kansu, suka kawo hadayu na ƙonawa a Haikalin Ubangiji. 16Sai suka ɗauki matsayinsu wanda aka ayyana bisa ga dokar Musa, mutumin Allah, firistocin suka yarfa jinin da suka karɓa daga hannun Lawiyawa. 17Gama akwai waɗansu da yawa daga cikin taron waɗanda ba su tsarkake kansu ba, saboda haka ya zama tilas Lawiyawa su yanka ɗan rago na Idin Ƙetarewa saboda dukan wanda ba shi da tsarki, domin a tsarkake shi ga Ubangiji. 18Gama akwai jama'a jingim, da yawa kuwa mutanen Ifraimu ne, da na Manassa, da na Issaka, da na Zabaluna, da ba su tsarkake kansu ba, duk da haka sun ci Idin Ƙetarewa ba yadda aka ƙayyade ba. Sai Hezekiya ya yi addu'a dominsu, yana cewa, “Ya Ubangiji mai alheri, ka gafarta wa ko wanne 19wanda ya sa zuciyarsa ga neman Allah, Ubangiji Allah na kakanninsa, ko bai yi bisa kan dokar tsarkakewa na Wuri Mai Tsarki ba.” 20Ubangiji kuwa ya ji Hezekiya, ya warkar da jama'ar. 21Jama'ar Isra'ila waɗanda suke a Urushalima kuwa sun yi idin abinci marar yisti da murna mai yawa, har kwana bakwai. Lawiyawa kuma da firistoci suka yabi Ubangiji kowace rana, suna raira waƙa da iyakar ƙarfinsu ga Ubangiji. 22Hezekiya kuwa ya yi magana ta ƙarfafawa ga dukan Lawiyawa waɗanda suka nuna fasaha a hidimar Ubangiji.
An Ƙara Yin Idin
Mutane fa suka ci abincin idin har kwana bakwai, suna miƙa hadayu na salama, suna ta yin godiya ga Ubangiji Allah na kakanninsu. 23Sai dukan taron suka yarda su ci gaba da yin idin har waɗansu kwana bakwai ɗin kuma, sai suka ci gaba da yin idin har kwana bakwai da murna. 24Gama Hezekiya, Sarkin Yahuza, ya ba taron bijimai dubu (1,000) da tumaki dubu bakwai (7,000), don yin hadayu, sarakuna kuma sun ba taron bijimai dubu (1,000) da tumaki dubu goma (10,000). Firistoci da yawa suka tsarkake kansu. 25Dukan taron Yahuza, da firistoci, da Lawiyawa, da dukan taron jama'a da suka zo daga Isra'ila, da baƙi waɗanda suka zo daga ƙasar Isra'ila, da baƙin da suka zauna a Yahuza, suka yi murna. 26Saboda haka an yi babban farin ciki a Urushalima, gama tun daga zamanin Sulemanu ɗan Dawuda, Sarkin Isra'ila, ba a yi wani abu kamar haka a Urushalima ba. 27Sai firistoci da Lawiyawa suka tashi suka sa wa jama'a albarka, aka kuwa ji muryarsu, addu'arsu kuma ta kai wurin zamansa a Sama.
Currently Selected:
2Tar 30: HAU
Highlight
Share
Compare
Copy
Want to have your highlights saved across all your devices? Sign up or sign in
@Bible Society of Nigeria 1979