2Tar 29
29
Sarki Hezekiya na Yahuza
(2Sar 18.1-3)
1Hezekiya ya ci sarauta sa'ad da yake da shekara ashirin da biyar. Ya yi mulki shekara ashirin da tara a Urushalima. Sunan tsohuwarsa Abaija, 'yar Zakariya. 2Ya yi abin da yake daidai a gaban Ubangiji kamar yadda kakansa Dawuda ya yi duka.
Hezekiya Ya Tsabtace Haikali
3A shekara ta fari ta mulkinsa, a wata na farko, sai ya buɗe ƙofofin Haikalin Ubangiji ya gyaggyara su. 4Sai ya shigo da firistoci da Lawiyawa, ya tara su a filin da yake wajen gabas. 5Sai ya ce musu, “Ku ji ni, ya ku Lawiyawa. Ku tsarkake kanku yanzu, ku kuma tsarkake Haikalin Ubangiji Allah na kakanninku, ku kawar da ƙazantar da yake a Wuri Mai Tsarki. 6Gama kakanninmu sun yi rashin aminci, sun aikata mugunta a gaban Ubangiji Allahnmu, sun rabu da shi sun ba da baya ga mazaunin Ubangiji. 7Sun kuma rurrufe ƙofofin shirayi suka kashe fitilu, sun daina ƙona turare ko miƙa hadayun ƙonawa a Wuri Mai Tsarki ga Allah na Isra'ila. 8Don haka Ubangiji ya yi fushi da Yahuza da Urushalima, ya sa suka zauna da tsoro, abin banmamaki, abin ba'a kamar yadda kuke gani da idanunku. 9Saboda wannan an kashe kakanninmu da takobi, 'ya'yanmu mata, da 'ya'yanmu maza da matanmu, an kai su bauta.
10“Yanzu na yi niyya a zuciyata in yi alkawari da Ubangiji Allah na Isra'ila, domin ya huce daga zafin fushin da yake yi da mu. 11'Ya'yana, kada ku yi sakaci, gama Ubangiji ne ya zaɓe ku don ku tsaya a gabansa, ku yi masa hidima, ku ƙona masa turare.”
12-14Sa'an nan sai Lawiyawa suka tashi,
na Kohatawa, Mahat ɗan Amasai, da Yowel ɗan Azariya,
na Merari, Kish ɗan Abdi, da Azariya ɗan Yehallelel,
na Gershonawa, Yowa ɗan Zimma, da Eden ɗan Yowa,
na Elizafan, Shimri da Yehiyel,
na Asaf, Zakariya da Mattaniya,
na Heman, Yehiyel da Shimai,
na Yedutun, Shemaiya da Uzziyel.
15Sai suka tattara 'yan'uwansu maza, suka tsarkake kansu, suka shiga bisa ga umarnin sarki, bisa ga maganar Ubangiji domin su tsabtace Haikalin Ubangiji. 16Firistoci fa, suka shiga can cikin Haikalin Ubangiji domin su tsabtace shi. Suka kwaso dukan ƙazantar da yake a Haikalin Ubangiji, suka zuba ta a farfajiyar Haikalin Ubangiji. Sai Lawiyawa suka kwashe, suka zubar a rafin Kidron.
17A rana ta fari a watan ɗaya suka fara aikin tsarkakewar. A rana ta takwas ga watan suka kai shirayin Ubangiji da aikin, kwana takwas suka ɗauka domin tsabtace Haikalin Ubangiji, a ranar sha shida ga watan ɗaya suka gama.
An Sāke Keɓe Haikali
18Sai suka tafi wurin sarki Hezekiya suka ce, “Mun tsabtace Haikalin Ubangiji duka, da bagaden hadayar ƙonawa tare da dukan tasoshi, da tukwane, da teburin gurasar ajiyewa da kuma dukan kayayyakin da yake ciki. 19Dukan kayayyakin da sarki Ahaz ya lalatar a zamaninsa, sa'ad da ya zama marar aminci, mun shirya su mun tsarkake su, suna nan a gaban bagaden Ubangiji.”
20Sarki Hezekiya kuwa ya tashi da sassafe ya tattara manyan gari suka haura zuwa Haikalin Ubangiji. 21Suka kawo bijimai bakwai, da raguna bakwai, da 'yan raguna bakwai, da bunsurai bakwai, domin yin hadaya don zunubi saboda mulkin, da Wuri Mai Tsarki, da kuma Yahuza. Sai ya umarci firistoci, wato 'ya'yan Haruna, maza, su miƙa su a kan bagaden Ubangiji. 22Sai suka yanka bijiman, firistoci suka karɓi jinin, suka yayyafa a jikin bagaden. Suka kuma yanka ragunan suka yayyafa jinin a bagaden. Haka nan kuma suka yanka 'yan ragunan suka yayyafa jinin a bagaden. 23Sa'an nan suka kawo wa sarki da taron jama'a bunsuran yin hadaya domin zunubi, suka ɗora hannuwansu a kan bunsuran. 24Sai firistocin suka yanka su suka tsarkake bagaden da jinin bunsuran, don a yi kafara saboda dukan Isra'ila. Gama sarki ya umarta a yi hadaya ta ƙonawa da hadaya don zunubi saboda dukan Isra'ila.
25Sai ya zaunar da Lawiyawa a Haikalin Ubangiji, masu kuge, da molaye, da garayu, bisa ga umarnin Dawuda, da na Gad, maigani na sarki, da na annabi Natan. Gama umarnin daga wurin Ubangiji ya zo ta wurin annabawansa. 26Lawiyawa suka tsaya da kayan bushe-bushe da na kaɗe-kaɗe na Dawuda, firistoci kuwa suna riƙe da ƙahoni. 27Sai Hezekiya ya ba da umarni a miƙa hadaya ta ƙonawar a bisa bagaden. Sa'ad da aka fara miƙa hadaya ta ƙonawa, sai aka fara raira waƙa ga Ubangiji, aka busa ƙaho, sai sauran masu kayan kaɗe-kaɗe da na bushe-bushe na Dawuda, Sarkin Isra'ila, suka kama. 28Dukan taron suka yi sujada, mawaƙa suna ta raira waƙa, masu ƙahoni suka yi ta busa. Aka yi ta yin haka har lokacin da aka gama miƙa hadayar ƙonawa. 29Bayan da an gama yin hadaya ta ƙonawa, sai sarki, tare da dukan waɗanda suke tare da shi, suka sunkuya suka yi sujada. 30Sai sarki Hezekiya tare da sarakunansa, suka faɗa wa Lawiyawa su yi ta raira yabo ga Ubangiji da kalmomin Dawuda, da na Asaf maigani. Da murna suka raira yabo, suka sunkuya suka yi sujada.
31Hezekiya kuwa ya amsa ya ce, “Yanzu dai kun tsarkake kanku ga Ubangiji. Sai ku zo kusa ku kawo hadayu da sadakoki na godiya a Haikalin Ubangiji.” Sai taron suka kawo hadayu da sadakoki na godiya, dukan waɗanda suka yi niyya kuwa suka kawo hadayu na ƙonawa. 32Jimillar hadayu na ƙonawa waɗanda taron suka kawo, su ne bijimai saba'in, da raguna ɗari, da 'yan raguna ɗari biyu, waɗannan duka kuwa don hadaya ne ta ƙonawa ga Ubangiji. 33Abubuwan da aka keɓe kuwa bijimai ɗari shida ne, da tumaki dubu uku (3,000). 34Amma su firistoci kima ne, don haka sun kāsa fiɗa dukan dabbobin da za a miƙa su hadaya ta ƙonawa. Sai 'yan'uwansu Lawiyawa suka taimake su har aka gama aiki kafin sauran firistoci su sami damar tsarkake kansu. Gama Lawiyawa sun fi firistoci himma wajen tsarkakewar kansu. 35Banda hadayu masu yawa na ƙonawa da aka yi, akwai kuma kitse na hadaya ta salama, akwai kuma hadaya ta sha don kowace hadaya ta ƙonawa.
Da haka fa aka maido hidimar Haikalin Ubangiji. 36Hezekiya da dukan jama'a suka yi murna saboda abin da Allah ya yi wa jama'a, gama farat ɗaya abin ya faru.
Currently Selected:
2Tar 29: HAU
Highlight
Share
Compare
Copy
Want to have your highlights saved across all your devices? Sign up or sign in
@Bible Society of Nigeria 1979