YouVersion Logo
Search Icon

2Tar 14

14
Sarki Asa na Yahuza
(1Sar 15.9-12)
1Sarki Abaija kuwa ya rasu, suka binne shi tare da kakanninsa a birnin Dawuda. Ɗansa Asa shi ya gāji gadon sarautarsa. Ƙasar ta sami sakewa har shekara goma a zamaninsa. 2Asa ya aikata abin da yake daidai a gaban Ubangiji Allahnsa. 3Ya kawar da baƙin bagadai da masujadai, ya rurrushe ginshiƙai, ya kuma tumɓuke Ashtarot. 4Ya umarci Yahuza su nemi Ubangiji Allah na kakanninsu, su kiyaye doka, da umarni. 5Daga cikin dukan biranen Yahuza, ya kawar da masujadai da bagadan ƙona turare. A zamaninsa an sami zaman lafiya a mulkinsa. 6Ya giggina birane masu kagara a Yahuza, gama ƙasar tana zaman lafiya. A waɗannan shekaru bai yi yaƙi da kowa ba, saboda Ubangiji ya kawo masa salama. 7Sai ya ce wa mutanen Yahuza, “Bari mu giggina waɗannan birane, mu kewaye su da garu, da hasumiya, da ƙofofi masu ƙyamare. Ƙasar tamu ce har yanzu, saboda mun nemi Ubangiji Allahnmu. Mun neme shi, ya kuwa ba mu salama a kowace fuska.” Suka yi ta gini, suka kuwa arzuta. 8Sarki Asa kuwa yana da soja dubu ɗari uku (300,000) a Yahuza, ko wanne yana da kutufani da māshi, yana da soja dubu ɗari biyu da dubu tamanin (280,000) daga Biliyaminu, 'yan baka ko wanne da garkuwarsa. Dukansu manyan jarumawa ne.
9Sai Zera mutumin Habasha ya zo da soja zambar dubu (1,000,000) da karusa ɗari uku har Maresha, don ya yi yaƙi da su. 10Don haka sai Asa ya fito ya gamu da shi, suka kuwa jā dāga a kwarin Zefata a Maresha. 11Asa kuwa ya yi kuka ga Ubangiji Allahnsa, ya ce, “Ya Ubangiji, ba wani mai taimako kamarka, wanda zai yi taimako sa'ad da mai ƙarfi zai kara da marar ƙarfi, ka taimake mu, ya Ubangiji Allahnmu, gama a gare ka muke dogara, da sunanka kuma muka zo don mu yi yaƙi da wannan babbar runduna. Ya Ubangiji, kai ne Allahnmu, kada ka bar mutum ya rinjayi jama'arka.”
12Ubangiji kuwa ya fatattaki Habashawa a gaban Asa da Yahuza, Habashawa kuwa suka gudu. 13Sai Asa da jama'ar da suke tare da shi, suka runtume su har zuwa Gerar. Habashawa suka fāɗi duka, ko ɗaya, ba wanda ya ragu da rai, gama an ragargaza su a gaban Ubangiji da gaban sojojin. Mutane suka kwashe ganima mai yawa gaske. 14Suka hallaka dukan birane da suke kewaye da Gerar, gama tsoron Ubangiji ya kama su. Suka washe dukan biranen, gama biranen suna cike da ganima. 15Suka kware alfarwan masu kiwon dabbobi, suka kora tumaki, da raƙuma masu yawan gaske. Sa'an nan suka komo Urushalima.

Currently Selected:

2Tar 14: HAU

Highlight

Share

Compare

Copy

None

Want to have your highlights saved across all your devices? Sign up or sign in