YouVersion Logo
Search Icon

2Tar 13

13
Sarki Abaija na Yahuza
(1Sar 15.1-8)
1A shekara ta goma sha takwas ta mulkin sarki Yerobowam, sai Abaija ya ci sarautar Yahuza. 2Ya yi mulki shekara uku a Urushalima, sunan tsohuwarsa Ma'aka, 'yar Uriyel na Gibeya.
Sai yaƙi ya ɓarke a tsakanin Abaija da Yerobowam. 3Abaija ya tafi da rundunar jarumawansa, dubu ɗari huɗu (400,000) zaɓaɓɓun mutane. Yerobowam shi kuma ya jā dāgar yaƙi don ya kara da Abaija, yana da mutum dubu ɗari takwas (800,000), zaɓaɓɓun mayaƙa ƙarfafa.
4Sai Abaija ya hau kan Dutsen Zemarayim, wanda yake a ƙasar Ifraimu mai tuddai, ya ce, “Ku kasa kunne gare ni, ya Yerobowam da dukanku Isra'ilawa. 5Ashe, ba ku sani ba, Ubangiji Allah na Isra'ila, ya ba da sarautar Isra'ila ga Dawuda, da 'ya'yansa maza har abada, ta wurin alkawarin gishiri? 6Duk da haka Yerobowam ɗan Nebat, baran Sulemanu ɗan Dawuda, ya tashi, ya yi wa ɗan ubangidansa tawaye, 7waɗansu marasa amfani, 'yan iska, suka taru suka goyi bayansa, suka raina Rehobowam ɗan Sulemanu, saboda a lokacin shi yaro ne, ba shi da ƙarfin zuciya, bai iya tsayayya da su ba. 8Yanzu kuma, so kuke ku ƙi mulkin Ubangiji wanda yake hannun 'ya'yan Dawuda, maza, saboda yawan da kuke da shi, da gumakan maruƙan zinariya da kuke da su, waɗanda Yerobowam ya yi muku. 9Ashe, ba ku kori firistocin Ubangiji, 'ya'yan Haruna, maza, da Lawiyawa ba, kuka yi wa kanku firistoci kamar na al'umman sauran ƙasashe? Duk wanda ya zo ya miƙa ɗan bijimi da raguna bakwai don ya tsarkake kansa, ya zama firist na gumaka ke nan, ba na Allah ba.
10“Amma a gare mu, Ubangiji shi ne Allahnmu, ba mu kuwa rabu da shi ba. Muna da firistoci, 'ya'yan Haruna, maza, masu yi wa Ubangiji hidima, da Lawiyawa masu yi musu hidima. 11Safe da yamma suna miƙa wa Ubangiji hadayun ƙonawa, da turare mai daɗin ƙanshi, sukan ajiye gurasar ajiyewa a kan tebur ɗin zinariya tsantsa, sukan lura da alkukin zinariya, da kuma fitilunsa kowane maraice, gama muna riƙe da umarnin Ubangiji Allahnmu, amma ku kun rabu da shi. 12Ga shi kuwa, Allah yana tare da mu, shi ne shugabanmu, firistocinsa kuwa suna da ƙahon da akan busa lokacin yaƙi, don su busa kira na yin yaƙi. Ya ku Isra'ilawa, kada ku yi yaƙi da Ubangiji, Allah na kakanninku, gama ba za ku yi nasara ba.”
13Ashe, Yerobowam ya riga ya sa 'yan kwanto, su yi musu yankan baya. Ƙungiyar mayaƙan Isra'ila tana fuskantar ta Yahuza, 'yan kwanto kuma suna bayansu. 14Da Yahuza suka duba, sai ga yaƙi a gabansu da bayansu. Sai suka yi kuka ga Ubangiji, firistoci kuma suka busa ƙaho. 15Mutanen Yahuza suka yi kūwwar yaƙi. Da suka yi kuwwar yaƙin sai Ubangiji ya sa Yerobowam da dukan jama'ar Isra'ila su gudu a gaban Abaija da Yahuza. 16Mutanen Isra'ila kuwa suka gudu a gaban Yahuza, Allah ya bashe su a hannunsa. 17Abaija fa, da jama'arsa suka karkashe su, mugun kisa. Mutum dubu ɗari biyar (500,000) zaɓaɓɓu na Isra'ila, aka karkashe. 18Haka kuwa aka ci nasara a kan mutanen Isra'ila a wannan lokaci. Mutanen Yahuza sun yi rinjaye saboda sun dogara ga Ubangiji, Allah na kakanninsu.
19Abaija ya runtumi Yerobowam, ya ƙwace masa waɗansu birane, wato Betel tare da ƙauyukanta, da Yeshana tare da ƙauyukanta, da kuma Efron tare da ƙauyukanta. 20Mulkin Yerobowam bai ƙara farfaɗowa a zamanin Abaija ba. Ubangiji kuma ya bugi Yerobowam, ya mutu.
21Amma Abaija ya ƙasaita, ya auro mata goma sha huɗu, ya haifi 'ya'ya maza ashirin da biyu, da 'ya'ya mata goma sha shida. 22Sauran ayyukan Abaija, da al'amuransa, da jawabansa, an rubuta su a littafin tarihin annabi Iddo.

Currently Selected:

2Tar 13: HAU

Highlight

Share

Compare

Copy

None

Want to have your highlights saved across all your devices? Sign up or sign in