1Sam 31
31
Rasuwar Saul da 'Ya'yansa Maza
(1Tar 10.1-12)
1Filistiyawa suka yi yaƙi da Isra'ilawa. Isra'ilawa kuma suka yi gudun Filistiyawa, aka karkashe su a Dutsen Gilbowa. 2Filistiyawa suka ci Saul da 'ya'yansa maza. Suka kashe Jonatan, da Abinadab, da Malkishuwa, 'ya'yan Saul. 3Yaƙin ya matsa wa Saul. Maharba suka harbe shi, suka yi masa mummunan rauni. 4Sai ya ce wa mai ɗaukar masa makamai, “Ka zare takobinka ka sha zarata da shi domin kada marasa kaciyan nan su zo su sha zarata, su yi mini ba'a.” Amma mai ɗaukar masa makamai bai yarda ba, domin ya ji tsoro da yawa. Sai Saul ya zare takobinsa, ya faɗa a kansa. 5Da mai ɗaukar masa makamai ya ga Saul ya rasu, shi ma ya fāɗa a kan nasa takobi ya mutu tare da Saul. 6Haka Saul, da 'ya'yansa maza guda uku, da mai ɗaukar masa makamai, da dukan mutanen da suke tare da shi suka mutu a rana ɗaya. 7Sa'ad da Isra'ilawan da suke a wancan hayi na kwarin da waɗanda suke a wancan hayin Urdun suka ga mayaƙan Isra'ila sun gudu, Saul kuma da 'ya'yansa sun mutu, sai suka bar garuruwansu, suka gudu. Filistiyawa kuwa suka zo suka zauna a cikinsu.
8Da Filistiyawa suka zo kashegari don su washe kayan kisassun, sai suka tarar da gawar Saul da gawawwakin 'ya'yansa uku a kan Dutsen Gilbowa. 9Suka yanke kansa, suka tuɓe makamansa. Suka aika manzannin a ƙasar Filistiyawa da suke kusa don su kai wannan albishir zuwa ga haikalin gumakansu, da mutanensu. 10Suka ajiye makaman Saul cikin haikalin gumakan nan Ashtarot. Suka ɗaure gawarsa a kan garun Bet-sheyan. 11Da mazaunan Yabesh-gileyad suka ji abin da Filistiyawa suka yi wa Saul, 12sai dukan jarumawa suka tashi, suka yi tafiya dukan dare. Suka ɗauko gawar Saul da gawawwakin 'ya'yansa daga kan garun Bet-sheyan. Da suka zo Yabesh sai suka ƙone su a can. 13Suka binne ƙasusuwansu a gindin itacen tsamiya a Yabesh, sa'an nan suka yi azumi kwana bakwai.
Currently Selected:
1Sam 31: HAU
Highlight
Share
Compare
Copy
Want to have your highlights saved across all your devices? Sign up or sign in
@Bible Society of Nigeria 1979