Sai ya ce wa mai ɗaukar masa makamai, “Ka zare takobinka ka sha zarata da shi domin kada marasa kaciyan nan su zo su sha zarata, su yi mini ba'a.” Amma mai ɗaukar masa makamai bai yarda ba, domin ya ji tsoro da yawa. Sai Saul ya zare takobinsa, ya faɗa a kansa. Da mai ɗaukar masa makamai ya ga Saul ya rasu, shi ma ya fāɗa a kan nasa takobi ya mutu tare da Saul.