YouVersion Logo
Search Icon

1Sam 21

21
Dawuda Ya Gudu daga wurin Saul
1 # Mat 12.3,4; Mar 2.25,26; Luk 6.3 Sa'an nan Dawuda ya tafi wurin Ahimelek, firist, a Nob. Ahimelek kuwa ya fita da rawar jiki domin ya tarye Dawuda, ya ce masa, “Me ya sa kake kai kaɗai, ba wani tare da kai ba?”
2Dawuda ya ce masa, “Na zo aikin sarki ne, ya kuwa ce kada in sanar wa kowa abin da ya aiko ni in yi. Jama'ata kuwa na riga na shirya inda zan sadu da su. 3Yanzu me kake da shi? Sai ka ba ni abinci malmala biyar ko wani abu da kake da shi a nan.”
4Firist ɗan ya ce wa Dawuda, “Ba ni da abinci don kowa da kowa, sai dai gurasa ta ajiyewa. Zan iya in ba ka muddin dai samarin sun keɓe kansu daga mata.”
5Dawuda ya ce masa, “Lalle ne a keɓe muke daga mata. Mutanena suka keɓe kansu a koyaushe suka tashi 'yar tafiya, balle fa yanzu da muka fito yin wani abu musamman.”
6 # L.Fir 24.5-9 Firist ɗin kuwa ya ba Dawuda tsattsarkan abinci na ajiya, gama ba wani abinci a wurin, sai gurasar ajiyewa kaɗai wadda akan kawar, a sāke sa wata mai ɗumi a ranar da aka kawar da ita.
7A ranar kuwa akwai wani mutum daga cikin barorin Saul, wanda aka tsare a gaban Ubangiji, sunansa Doyeg, mutumin Edom ne. Shi ne shugaban masu kiwon garkunan Saul.
8Dawuda kuwa ya ce wa Ahimelek, “Kana da mashi ko takobi a nan kusa? Gama ban zo da takobina ko wani makami ba, domin ka sani sha'anin sarki na gaggawa ne.”
9 # 1Sam 17.51 Firist ya ce, “Ga takobin Goliyat, Bafiliste wanda ka kashe a kwarin Ila, a naɗe da zane a bayan falmaran. Idan kana so ka ɗauka, sai ka ɗauka, gama banda shi, ba wani takobi a nan.”
Dawuda kuwa ya ce, “Ai, ba wanda ya fi wannan, sai ka ba ni shi.”
10Sai Dawuda ya tashi, yana gudu ke nan daga wurin Saul. Ya tafi wurin Akish, Sarkin Gat. 11#1Sam 18.7; 29.5 Fādawan Akish kuwa suka ce masa, “Ashe, wannan ba shi ne Dawuda, sarkin ƙasar ba? Ba a kansa suka raira waƙa cikin raye-rayensu suna cewa, ‘Saul ya kashe dubbai, Dawuda kuwa ya kashe dubun dubbai’?”
12 # Zab 56 Da Dawuda ya ji waɗannan maganganu, sai ya tsorata ƙwarai da Akish Sarkin Gat. 13#Zab 34 Ya mai da kansa kamar mahaukaci a gabansa. Ya yi zane-zane a ƙyamaren ƙofofin garin. Ya bar yau na bin gemunsa. 14Akish kuwa ya ce wa fādawansa, “Ashe, mutumin mahaukaci ne? Don me kuka kawo shi wurina? 15Na rasa mahaukata ne da za ku kawo mini wannan mutum ya yi ta hauka a gabana? Wannan mutum ne zai shiga gidana?”

Currently Selected:

1Sam 21: HAU

Highlight

Share

Compare

Copy

None

Want to have your highlights saved across all your devices? Sign up or sign in