YouVersion Logo
Search Icon

1Sam 20

20
Abutar Dawuda da Jonatan
1Sa'an nan Dawuda ya gudu daga Nayot ta Rama, ya zo wurin Jonatan, ya ce masa, “Me na yi? Mene ne laifin da na yi wa mahaifinka da yake so ya kashe ne?”
2Jonatan ya ce masa, “Allah ya sawwaƙa, ba za a kashe ka ba, gama babana yakan faɗa mini kome, ƙarami ko babba, kafin ya aikata. To, me zai sa babana ya ɓoye mini wannan? Wannan ba haka yake ba.”
3Amma Dawuda ya rantse masa, ya ce, “Mahaifinka ya hakikance na sami tagomashi a wurinka, domin haka ba zai sanar maka da wannan ba, don kada ya baƙanta maka rai. Na rantse da Ubangiji da kai kuma, mataki ɗaya yake tsakanina da mutuwa!”
4Sai Jonatan ya ce wa Dawuda, “Duk abin da ka ce, zan yi maka.”
5 # L.Ƙid 28.11 Dawuda kuwa ya ce masa, “Ga shi, gobe ce amaryar wata, dole ne in zauna tare da sarki a teburinsa. Ka bar ni in tafi in ɓuya a saura har kwana uku. 6Idan mahaifinka bai gan ni ba, sai ka ce masa, ni na roƙe ka ka bar ni in gaggauta zuwa Baitalami, garinmu, domin akwai ba da sadaka ta shekara saboda dukan gidanmu. 7Idan ka ji ya ce, ‘Da kyau,’ to, baranka zai tsira ke nan, amma idan ya husata, to, sai ka sani yana niyyar kashe ni ke nan, 8kai kuwa ka nuna mini alheri, gama ka yi mini alkawari mai ƙarfi. Amma idan ina da laifi, sai ka kashe ni da kanka. Don me za ka bar mahaifinka ya kashe ni?”
9Jonatan ya masa ya ce, “Allah ya sawwaƙe! Da na sani babana yana da nufi ya yi maka mugunta, ai, da na faɗa maka.”
10Sa'an nan Dawuda ya ce wa Jonatan, “Wane ne zai faɗa mini idan mahaifinka ya amsa maka da fushi?”
11Jonatan kuwa ya ce masa, “Zo mu tafi saura.” Sai su biyu suka tafi saura. 12Sa'an nan Jonatan ya ce wa Dawuda, “Ubangiji Allah na Isra'ila zai zama shaida. Gobe war haka, ko jibi zan tattauna maganar da mahaifina, idan da nufin alheri zuwa gare ka, zan aika, in faɗa maka. 13Amma idan har mahaifina yana da niyyar yi maka mugunta, amma ban sanar da kai ba, to, bari Ubangiji ya hukunta ni. Ubangiji ya kasance tare da kai kamar yadda ya kasance da mahaifina. 14Ba lokacin da nake da rai ne kaɗai za ka nuna mini alherin Ubangiji domin kada in mutu ba. 15#2Sam 9.1 Ko bayan raina kada ka daina nuna wa gidana alheri har abada, lokacin da Ubangiji ya datse maƙiyanka daga fuskar duniya.” 16Jonatan ya yi alkawari da gidan Dawuda. Ubangiji kuwa zai ɗauki fansa a kan maƙiyan Dawuda.
17Sai Jonatan ya sa Dawuda ya yi masa alkawari zai ƙaunace shi, gama shi kansa yana ƙaunar Dawuda ƙwarai kamar yadda yake ƙaunar kansa. 18Sa'an nan Jonatan ya ce wa Dawuda, “Gobe ce amaryar wata, ba kowa a wurin zamanka ke nan da yake ba za ka zo ba. 19A rana ta uku za a gane ba ka nan sosai, to, sai ka tafi, ka ɓuya a wurin da ka ɓuya a waccan rana. Ka zauna kusa da tarin duwatsu. 20Zan harba kibau guda uku kusa da tarin duwatsun, kamar ina harbin wani abu ne. 21Zan aiki yaro ya tafi ya nemo kiban. Idan na ce masa, ‘Duba, ga kiban kusa da kai, ka kawo su,’ To, sai ka fito, ka zo, wato lalle kome lafiya ke nan, ba abin da zai cuce ka. 22Amma idan na ce wa yaron, ‘Duba, kiban suna a gabanka,’ To, ka tafi, gama Ubangiji ya sallame ka, ka tafi. 23A kan alkawarin da muka yi, ni da kai kuwa, Ubangiji shi ne shaida a tsakaninmu har abada.”
24Dawuda ya ɓuya a saura. A ranar amaryar wata kuwa sarki ya zauna domin cin abinci. 25Ya zauna inda ya saba zama kusa da bango. Jonatan ya zauna daura da shi, Abner kuwa ya zauna kusa da Saul, amma ba kowa a wurin zaman Dawuda. 26Saul kuwa bai ce kome a wannan rana ba, gama ya zaci wani abu ya sami Dawuda, kila ba shi da tsarki, lalle kam Dawuda ba shi da tsarki. 27Amma kashegari, wato rana ta biyu ta amaryar watan, ba kowa kuma wurin zaman Dawuda, sai Saul ya ce wa Jonatan, ɗansa, “Me ya sa ɗan Yesse bai zo wurin cin abinci ba, jiya da yau?”
28Jonatan ya ce masa, “Dawuda ya roƙe ni da naciya in bar shi ya tafi Baitalami. 29Ya ce mini, ‘In ka yarda ka bar ni in tafi, gama a gidanmu ana ba da sadaka a gari, ɗan'uwana kuwa ya umarce ni in je. Idan na sami tagomashi a wurinka ka bar ni in tafi in ga 'yan'uwana.’ Abin da ya sa bai zo ba ke nan.”
30Sai Saul ya husata da Jonatan, ya ce masa, “Kai yaron banza ne, mai ƙin ji, ai, na sani kana goyon bayan ɗan Yesse don ka wulakantar da kanka da mahaifiyarka. 31Muddin ɗan Yesse na da rai a duniya, ba za ka kahu ba. Sarautarka kuma ba za ta kahu ba. Yanzu sai ka je ka taho mini da shi. Dole kashe shi za a yi.”
32Jonatan ya ce wa mahaifinsa, “Me ya sa za a kashe shi? Me ya yi?”
33Sai Saul ya jefe shi da mashi don ya kashe shi. Sai Jonatan ya gane lalle mahaifinsa ya yi niyya ya kashe Dawuda. 34Sai Jonatan ya tashi da fushi daga wurin cin abinci, bai ci abinci a rana ta biyu ga watan ba, saboda baƙin ciki a kan Dawuda, domin kuma mahaifinsa ya kunyata shi. 35Da safe Jonatan ya tafi saura tare da wani yaro daidai lokacin da ya shirya da Dawuda. 36Sai ya ce wa yaron, “Yi gudu, ka nemo kiban da zan harba.” Sa'ad da yaron ya ruga, sai ya harba kibiya gaba da shi. 37Da yaron ya kai inda Jonatan ya harba kibiyar, sai ya ce masa, “Ba kibiyar tana a gaban ka ba?” 38Ya ce wa yaron ya yi maza, kada ya tsaya. Sai yaron ya kwashe kiban ya kawo masa. 39Amma yaron bai san abin da ake nufi ba. Jonatan da Dawuda kaɗai suka san abin da ake ciki. 40Sa'an nan Jonatan ya ba yaron makamansa, ya ce masa, “Kai su gari.”
41Da yaron ya tafi, sai Dawuda ya tashi daga inda ya ɓuya kusa da tarin duwatsun, ya rusuna har sau uku. Sa'an nan suka sumbaci juna, suka yi kuka, amma Dawuda ya fi yi. 42Jonatan ya ce wa Dawuda, “Sai ka tafi lafiya, tun da yake mun riga mun rantse wa juna da sunan Ubangiji cewa, ‘Ubangiji zai zama shaida tsakanina da kai, da tsakanin zuriyarmu har abada.’ ” Dawuda ya yi tafiyarsa, Jonatan kuwa ya koma gari.

Currently Selected:

1Sam 20: HAU

Highlight

Share

Compare

Copy

None

Want to have your highlights saved across all your devices? Sign up or sign in