1Bit 2
2
Rayayyen Dutse da Kabila Tsattsarka
1Saboda haka, sai ku yar da kowace irin ƙeta, da ha'inci, da munafunci, da hassada, da kuma kowane irin kushe. 2Kamar jariri sabon haihuwa, ku yi marmarin shan madara marar gami mai ruhu, domin ku girma da shi, har ya kai ku ga samun ceto, 3#Zab 34.8 in dai kun ɗanɗana alherin Ubangiji.
4Ku zo a gare shi, rayayyen dutsen nan, hakika abin ƙi ne a gun mutane, amma zaɓaɓɓe, ɗaukakakke a gun Allah. 5Ku kuma, kamar rayayyun duwatsu, bari a gina gida mai ruhu da ku, domin ku zama tsattsarkar ƙungiyar firistoci, da nufin ku miƙa hadayu na ruhu, abin karɓa ga Allah, ta wurin Yesu Almasihu, 6#Ish 28.16 Domin a tabbace yake a Nassi cewa,
“Ga shi, na sa mafificin dutsen a gini a Sihiyona, zaɓaɓɓe, ɗaukakakke,
Duk mai gaskatawa da shi kuwa, ba zai kunyata ba.”
7 #
Zab 118.22
A gare ku, ku da kuka ba da gaskiya kuwa, shi ɗaukakakke ne. Amma ga waɗanda suka ƙi gaskatawa, to,
“Dutsen da magina suka ƙi,
Shi ne ya zama mafificin dutsen gini,”
8 #
Ish 8.14,15 Da kuma,
“Dutsen sa tuntuɓe,
Da fā na sa faɗuwa.”
Sun yi tuntuɓe ne da maganar, don sun ƙi biyayya da ita. Haka kuwa aka ƙaddaro musu.
9 #
Fit 19.5,6; Ish 43.20;
Fit 19.5; M.Sh 4.20; 7.6; 14.2; Tit 2.14;
Ish 43.21;
Ish 9.2
Amma ku kabila ce zaɓaɓɓiya, ƙungiyar firistocin babban Sarki, tsattsarkar al'umma, jama'ar mallakar Allah, domin ku sanar da mafifitan al'amuran wannan da ya kirawo ku daga cikin duhu, kuka shiga maɗaukakin haskensa. 10#Yush 2.23 Dā ba jama'a ɗaya kuke ba, amma a yanzu, ku jama'ar Allah ce. Dā ba ku sadu da jinƙansa ba, amma a yanzu kun sadu da shi.
Ku yi Zaman Bayin Allah
11Ya ƙaunatattuna, ina roƙonku don ku baƙi ne, bare kuma, ku guje wa mugayen sha'awace-sha'awace na halin mutuntaka waɗanda suke yaƙi da zuciyarku. 12Ku yi halin yabo a cikin al'ummai, don duk sa'ad da suke kushenku, cewa ku mugaye ne, sai su ga kyawawan ayyukanku, har su ɗaukaka Allah a ran da alheri ya sauko musu.
13Ku yi biyayya ga kowace hukumar mutane saboda Ubangiji, ko ga sarki, domin shi ne shugaba, 14ko kuwa ga mahukunta, domin su ne ya a'aika su hori mugaye, su kuma yabi masu kirki. 15Domin nufin Allah ne ku toshe jahilcin marasa azanci ta yin aiki nagari. 16Ku yi zaman 'yanci, sai dai kada ku fake a bayan 'yancin nan naku, ku yi mugunta. Amma ku yi zaman bayin Allah. 17Ku girmama kowa, ku ƙaunaci 'yan'uwa, ku ji tsoron Allah, ku girmama sarki.
Koyi da Wahalar Almasihu
18Ku barori, ku bi iyayen gidanku da matuƙar ladabi, ba sai na kirki da masu sanyin hali kaɗai ba, har ma da miskilai. 19Ai, abin karɓa ne, in saboda mutum yana sane da nufin Allah, ya jure wa wuyar da yake sha, ba da alhakinsa ba. 20To, ina abin taƙama don kun yi haƙuri in kun sha dūka a kan laifin da kuka yi? Amma, in kun yi aiki nagari kuka sha wuya a kansa, kuka kuma haƙura, to shi ne abin karɓa ga Allah.
21Domin a kan haka ne musamman aka kira ku. Gama Almasihu ma ya sha wuya dominku, ya bar muku gurbi ku bi hanyarsa. 22#Ish 53.9 Bai taɓa yin laifi ba faufau, ba a kuwa taɓa jin yaudara a bakinsa ba. 23#Ish 53.7 Da aka zage shi bai rama ba, da ya sha wuya kuma bai yi kashedi ba, sai dai ya dogara ga mai shari'ar adalci. 24#Ish 53.5,6 Shi kansa ya ɗauke zunubanmu a jikinsa a kan gungume, domin mu yi zamanmu matattu ga zunubi, rayayyu kuma ga adalci. Da raunukansa ne aka warkar da ku. 25A dā kun ɓăce kamar tumaki, amma a yanzu kun dawo ga Makiyayi, wato mai kula da rayukanku.
Currently Selected:
1Bit 2: HAU
Highlight
Share
Copy
Want to have your highlights saved across all your devices? Sign up or sign in
@Bible Society of Nigeria 1979