Ya ƙaunatattuna, ina roƙonku don ku baƙi ne, bare kuma, ku guje wa mugayen sha'awace-sha'awace na halin mutuntaka waɗanda suke yaƙi da zuciyarku. Ku yi halin yabo a cikin al'ummai, don duk sa'ad da suke kushenku, cewa ku mugaye ne, sai su ga kyawawan ayyukanku, har su ɗaukaka Allah a ran da alheri ya sauko musu.