1Sar 22
22
Mikaiya Ya Yi wa Ahab Kashedi
(2Tar 18.1-27)
1Aka yi shekara uku ba a yi yaƙi tsakanin Suriya da Isra'ila ba. 2A shekara ta uku ɗin, sai Yehoshafat, Sarkin Yahuza, ya ziyarci Sarkin Isra'ila.
3Sarkin Isra'ila kuwa ya ce wa fādawansa, “Ko kun sani Ramot-gileyad tamu ce, ga shi kuwa, mun yi shiru, ba mu ƙwace ta daga hannun Sarkin Suriya ba?” 4Ya kuma ce wa Yehoshafat, “Za ka tafi tare da ni zuwa wurin yaƙi a Ramot-gileyad?”
Yehoshafat ya amsa wa Sarkin Isra'ila, “Ni da kai ɗaya ne, mutanena kuma mutanenka ne, dawakaina kuma naka ne.” 5Yehoshafat ya ce wa Sarkin Isra'ila, “Ka nemi faɗar Ubangiji tukuna.”
6Sa'an nan Sarkin Isra'ila ya tara annabawa ɗari huɗu, ya tambaye su, ya ce, “In tafi in yi yaƙi da Ramot-gileyad, ko kuwa kada in tafi?”
Su kuwa suka ce masa, “Ka haura, gama Ubangiji zai ba da ita a hannunka.”
7Amma Yehoshafat ya ce, “Ba wani annabin da za mu tambaya kuma?”
8Sarkin Isra'ila ya ce wa Yehoshafat, “Da sauran mutum ɗaya wanda za mu iya mu tambaya faɗar Ubangiji, shi ne Mikaiya ɗan Imla, amma ina ƙinsa, gama bai taɓa yin wani annabcin alheri a kaina ba, sai dai na masifa.”
Yehoshafat ya ce, “Kada sarki ya faɗi haka.”
9Sa'an nan Sarkin Isra'ila ya kirawo wani bafāde, ya ce masa, “Maza, ka taho da Mikaiya ɗan Imla.”
10Sarkin Isra'ila da Yehoshafat, Sarkin Yahuza, suna zaune a kujerun sarautarsu, saye da tufafinsu a dandalin ƙofar Samariya. Annabawa kuwa suna annabci a gabansu. 11Zadakiya ɗan Kena'ana ya yi ƙahonin ƙarfe, ya ce, “Ubangiji ya ce, ‘Da waɗannan ƙahoni za ka tunkuyi Suriyawa har su hallaka.’ ” 12Dukan annabawan suka yi annabci iri ɗaya, suna cewa, “Ka haura zuwa Ramot, za ka yi nasara, gama Ubangiji zai ba da ita a hannunka.”
13Bafāden da ya tafi kiran Mikaiya ya ce masa, “Ga shi, maganar sauran annabawan iri ɗaya ce, sun yi maganar alheri ga sarki, sai kai ma ka yi magana irin tasu, ka yi maganar alheri ga sarki.”
14Amma Mikaiya ya ce, “Na rantse da Ubangiji, abin da Ubangiji ya faɗa mini, shi ne zan faɗa.”
15Da ya zo gaban sarki, sai sarki ya ce masa, “Mikaiya, mu tafi Ramot don yaƙi, ko kuwa kada mu tafi?”
Ya amsa masa ya ce, “Ka haura, za ka yi nasara, Ubangiji zai ba da ita a hannunka.”
16Sarki Ahab kuwa ya ce masa, “Sau nawa zan roƙe ka kada ka faɗa mini kome sai dai gaskiya ta Ubangiji?”
17 #
L.Ƙid 27.17; Mat 9.36; Mar 6.34 Mikaiya ya ce, “Na ga mutanen Isra'ila duka a warwatse a kan tuddai kamar tumakin da ba su da makiyayi, Ubangiji kuwa ya ce, ‘Waɗannan ba su da shugaba, bari kowa ya koma gidansa lafiya.’ ”
18Sarkin Isra'ila ya ce wa Yehoshafat, “Ban faɗa maka ba, ba zai yi wani annabcin alheri a kaina ba sai dai na masifa?”
19 #
Ayu 1.6; Ish 6.1 Makaiya kuwa ya ce, “Ka ji maganar Ubangiji, gama na ga Ubangiji yana zaune a kursiyinsa. Dukan taron mala'ikun Sama suna tsaye a wajen damansa da na hagunsa. 20Ubangiji kuwa ya ce, ‘Wa zai yaudari Ahab, ya tafi ya fāɗa wa Ramot?’ Sai wannan ya ce abu kaza, wani kuma ya ce abu kaza, 21har da wani ruhu ya fito ya tsaya a gaban Ubangiji ya ce, ‘Ni zan yaudare shi.’ 22Ubangiji ya ce masa, ‘Ta wace hanya?’ Sai ruhun ya ce, ‘Zan tafi in zama ruhun ƙarya a bakin dukan annabawansa.’ Sai Ubangiji ya ce, ‘Ba shakka za ka yaudare shi, za ka yi nasara, sai ka tafi.’ ”
23Mikaiya ya ce, “Ga abin da ya faru, Ubangiji ya bar annabawanka su faɗa maka ƙarya. Amma Ubangiji kansa ya riga ya zartar maka da masifa.”
24Sa'an nan Zadakiya ɗan Kena'ana ya matso kusa ya mari Mikaiya a fuska, ya ce, “Ƙaƙa Ruhun Ubangiji ya bar ni, ya zo ya yi magana da kai?”
25Mikaiya ya ce masa, “A ran nan za ka gani, ka kuma gudu ka shiga har ƙurewar ɗaki don ka ɓuya.”
26Sarki Ahab ya ce, “Ku kama Mikaiya, ku kai shi wurin Amon, shugaban birnin, da wurin Yowash ɗan sarki. 27Ku ce musu su jefa wannan mutum a kurkuku, a riƙa ciyar da shi da abinci kaɗan da ruwan sha kaɗan, har na komo lafiya.”
28Mikaiya kuwa ya ce, “In dai ka komo lafiya, to, Ubangiji bai yi magana da ni ba.” Ya ƙara da cewa, “Kowa ya kasa kunne ga abin da na faɗa.”
Mutuwar Ahab
(2Tar 18.28-34)
29Ahab Sarkin Isra'ila da Sarkin Yahuza suka tafi Ramot-gileyad. 30Sarkin Isra'ila kuwa ya ce wa Sarkin Yahuza, “Zan ɓad da kama in tafi wurin yaƙi, amma kai ka sa tufafinka na sarauta.” Sai Ahab ya ɓad da kama ya tafi wurin yaƙi.
31Sarkin Suriya dai ya riga ya umarci shugabannin karusan yaƙinsa, su talatin da biyu, ya ce, “Kada ku yi yaƙi da kowa, kome matsayinsa, sai dai Ahab kaɗai.”
32Sa'ad da shugabannin karusai suka ga Yehoshafat, sai suka ce, “Lalle shi ne Ahab.” Sai suka juya don su yi yaƙi da shi. Yehoshafat kuwa ya yi ihu. 33Da shugabannin karusan yaƙi suke gane ba Ahab ba ne, sai suka rabu da shi.
34Wani sojan Suriya kuwa ya yi sa'a, ya shilla kibiya kawai, sai ta sami Ahab, ta kafar sulkensa. Saboda haka ya ce wa mai korar karusarsa, “Ka juya, ka fitar da ni daga fagen fama gama an yi mini rauni.”
35A ran nan yaƙi ya yi tsanani. Aka tallafi Ahab a cikin karusarsa a gaban Suriyawa. Da maraice ya mutu. Jinin raunin da aka yi masa ya zuba a cikin karusar. 36A wajen faɗuwar rana aka yi wa sojoji shela aka ce, “Kowa ya koma garinsu da ƙasarsu.”
37Sarki Ahab ya mutu, aka kawo shi Samariya, aka binne shi. 38Suka wanke karusarsa a tafkin Samariya. Karnuka suka lashe jininsa, karuwai kuma suka yi wanka a tafkin kamar yadda Ubangiji ya faɗa.
39Sauran ayyukan Ahab da dukan abin da ya yi, da gidan da ya gina na hauren giwa da garuruwan da ya gina, an rubuta su a littafin tarihin sarakunan Isra'ila. 40Ahab ya rasu kamar kakanninsa. Ɗansa Ahaziya ya gāji sarautarsa.
Sarki Yehoshafat na Yahuza
(2Tar 20.31—21.1)
41Yehoshafat ɗan Asa ya ci sarautar Yahuza a shekara ta huɗu ta sarautar Ahab, Sarkin Isra'ila. 42Yehoshafat yana da shekara talatin da biyar sa'ad da ya ci sarauta. Ya yi shekara ashirin da biyar yana sarauta a Urushalima. Sunan tsohuwarsa Azuba 'yar Shilhi. 43Ya bi halin tsohonsa, Asa, bai karkace ba. Ya yi abin da yake daidai a gaban Ubangiji. Duk da haka ba a rushe wuraren tsafin na tuddai ba. Mutane suka yi ta miƙa hadayu, suka ƙona turare a tuddan. 44Yehoshafat kuma ya ba Sarkin Isra'ila amana.
45Sauran ayyukan Yehoshafat, da ƙarfin da ya nuna, da yadda ya yi yaƙi, an rubuta su a littafin tarihin sarakunan Yahuza. 46Ya kori dukan karuwai mata da maza da suka ragu a ƙasar a zamanin tsohonsa Asa.
47A lokacin babu sarki a Edom sai wakili. 48Yehoshafat ya yi jiragen ruwa a Tarshish don su tafi Ofir su kwaso zinariya, amma jiragen ba su tafi ba, gama jiragen sun farfashe a Eziyon-geber. 49Sa'an nan Ahaziya, ɗan Ahab, ya ce wa Yehoshafat. “Ka bar barorina su tafi tare da naka a cikin jirage.” Amma Yehoshafat bai yarda ba.
50Yehoshafat kuwa ya rasu, aka binne shi a inda aka binne kakanninsa a birnin kakansa Dawuda. Ɗansa Yehoram ya gaji sarautarsa.
Sarki Ahaziya na Isra'ila
51Ahaziya, ɗan Ahab, ya ci sarautar Isra'ila a Samariya a shekara ta goma sha bakwai ta sarautar Yehoshafat, Sarkin Yahuza. Ya yi sarautar Isra'ila shekara biyu. 52Ya yi zunubi a gaban Ubangiji. Ya bi halin tsohonsa da na tsohuwarsa, da na Yerobowam ɗan Nebat, wanda ya sa Isra'ila su yi zunubi. 53Ya bauta wa gunkin nan Ba'al ya yi masa sujada. Ya kuma sa Ubangiji Allah na Isra'ila ya yi fushi, gama ya bi halin tsohonsa.
Currently Selected:
1Sar 22: HAU
Highlight
Share
Compare
Copy
Want to have your highlights saved across all your devices? Sign up or sign in
@Bible Society of Nigeria 1979