1Sar 21
21
Ahab da Gonar Inabin Nabot
1Nabot Bayezreyele yana da gonar inabi a Yezreyel kusa da fādar Ahab, Sarkin Samariya. 2Sai Ahab ya yi magana da Nabot ya ce, “Ka ba ni gonar inabinka don in mai da ita lambu, gama gonar tana kusa da gidana, ni kuwa zan ba ka wata gonar inabi a maimakonta, idan kuma kana so, sai in ba ka tamanin kuɗinta.”
3Amma Nabot ya ce wa Ahab, “Ubangiji ya sawwaƙa in ba ka gādon kakannina.”
4Ahab ya koma gida da baƙin ciki da rai a ɓace saboda abin da Nabot Bayezreyele ya faɗa masa. Ahab ya kwanta a gadonsa, ya mai da fuskarsa bango ya ƙi cin abinci. 5Yezebel, matarsa kuwa ta zo wurinsa, ta ce masa, “Me ya sa ka damu, ka ruɗe haka, har ka ƙi cin abinci?”
6Ya ce mata, “Domin na yi magana da Nabot Bayezreyele, na ce ya sayar mini da gonar inabinsa, idan kuma yana so, sai in ba shi wata gonar inabi a maimakon tasa, amma ya ce ba zai ba ni gonar inabin ba.”
7Yezebel, matarsa, ta ce masa, “Ba kai ne kake mulkin Isra'ila ba? Tashi, ka ci abinci, ka yi farin ciki, zan ba ka gonar inabin Nabot Bayezreyele.”
8Sa'an nan ta rubuta wasiƙu da sunan Ahab, ta hatimce su da hatiminsa, sa'an nan ta aika da wasiƙun zuwa ga dattawa da fādawan da suke zaune a birnin tare da Nabot. 9Ta rubuta a wasiƙun, “A yi shelar azumi, a sa Nabot a gaban jama'a. 10A kuma sa 'yan iska guda biyu, su yi ta zarginsa, su riƙa cewa, ‘Nabot ya zagi Allah da sarki.’ Sa'an nan ku tafi da shi, ku jajjefe shi da duwatsu har ya mutu.” 11Mutanen birnin kuwa, dattawa da fādawan da suke zaune a birnin suka yi yadda Yezebel ta sa su yi, kamar yadda aka rubuta a wasiƙun da ta aika musu. 12Suka kuwa yi shelar azumi, suka sa Nabot a gaban jama'a. 'Yan iska guda biyu suka zauna kusa da shi, suka yi ta zarginsa a gaban jama'a, suna cewa, “Nabot ya zagi Allah da sarki.” 13Sai suka fitar da shi daga cikin birni, suka jajjefe shi da duwatsu har ya mutu. 14Sa'an nan suka aika wa Yezebel cewa, “An jajjefi Nabot, ya mutu.”
15Nan da nan da Yezebel ta ji an jajjefi Nabot har ya mutu, sai ta ce wa Ahab, “Tashi, ka mallaki gonar inabin Nabot, wadda ya ƙi sayar maka, gama Nabot ba shi da rai, ya mutu.” 16Da Ahab ya ji Nabo ya mutu, sai ya tashi ya gangara zuwa gonar inabin Nabot Bayezreyele don ya mai da ta tasa. 17Sa'an nan Ubangiji ya ce wa Iliya Batishbe, 18“Tashi, ka tafi, ka sadu da Ahab, Sarkin Isra'ila, wanda yake a Samariya, ga shi can a gonar inabin Nabot inda ya tafi don ya mallake ta. 19Ka faɗa masa, ni Ubangiji, na ce, ‘Ka kashe mutum, kana kuma ƙwace abin da ya mallaka?’ Ka faɗa masa ga abin da na faɗa, ‘A wurin da karnuka suka lashe jinin Nabot, a nan ne kuma karnuka za su lashe jininka.’ ”
20Sa'ad da Ahab ya ga Iliya, sai ya ce masa, “Ka tarshe ni ko, maƙiyina?”
Iliya ya amsa ya ce, “I, na tarshe ka, gama ka ba da kanka ga aikata mugunta a gaban Ubangiji. 21Saboda haka Ubangiji ya ce maka, ‘Ga shi, zan kawo maka masifa, in shafe ka, in datse maka kowane ɗa namiji, bawa ko ɗa, a Isra'ila. 22Zan sa gidanka ya zama kamar gidan Yerobowam ɗan Nebat, da gidan Ba'asha ɗan Ahija saboda ka sa ni in yi fushi, ka kuma sa mutanen Isra'ila suka yi zunubi.’ 23#2Sar 9.36 A kan Yezebel kuwa Ubangiji ya ce, ‘Karnuka za su cinye Yezebel a cikin Yezreyel.’ 24Duk wanda yake na Ahab da zai mutu a birni karnuka ne za su cinye shi, wanda kuma ya mutu a waje tsuntsaye ne za su cinye shi.”
25Babu wani kamar Ahab da ya ba da kansa ga aikata mugunta a gaban Ubangiji. Matarsa, Yezebel, ita ce ta zuga shi. 26Ya yi abar banƙyama ƙwarai, ya bi gumaka kamar yadda Amoriyawa suke yi, waɗanda Ubangiji ya kore su a gaban Isra'ilawa.
27Da Ahab ya ji wannan magana, sai ya yage tufafinsa, ya sa na makoki, ya yi azumi, ya kwanta a tsummokin makoki, ya tashi yana tafiya a hankali.
28Ubangiji ya yi magana da Iliya Batishbe ya ce, 29“Ka ga yadda Ahab ya ƙasƙantar da kansa a gabana? Da yake ya ƙasƙantar da kansa a gabana, ba zan kawo masifar a zamaninsa ba, sai a zamanin ɗansa ne, zan kawo masifar a kan gidansa.”
Currently Selected:
1Sar 21: HAU
Highlight
Share
Compare
Copy
Want to have your highlights saved across all your devices? Sign up or sign in
@Bible Society of Nigeria 1979