YouVersion Logo
Search Icon

1Kor 5

5
Hukunci a kan Fasikanci
1 # M.Sh 22.30 Ana ta cewa akwai fasikanci a tsakaninku, irin wanda ba a yi ko a cikin al'ummai, har wani yana zama da matar ubansa. 2A! Har kuwa alfarma kuke yi! Ashe, ba gwamma ku yi baƙin ciki ba, har a fitar da wanda ya yi wannan mugun aiki daga cikin jama'arku?
3Ko da yake a jiki ba na nan, ai, ruhuna yana nan, kamar ma ina nan ne, har ma na riga na yanke wa mutumin da ya yi abin nan hukunci da sunan Ubangijinmu Yesu. 4Sa'ad da kuka hallara, ruhuna kuma yana nan, da kuma ikon Ubangijinmu Yesu, 5sai ku miƙa irin wannan mutum ga Shaiɗan, don yă hallaka jikinsa, ruhunsa kuma ya tsira a ranar Ubangiji Yesu.
6 # Gal 5.9 Fāriyarku ba shi da kyau. Ashe, ba ku sani ba, ɗan yisti kaɗan yake game dukkan curin gurasa? 7#Fit 12.5 Ku fitar da tsohon yistin nan, don ku zama sabon curi, domin hakika an raba ku da yistin, da yake an riga an yanka Ɗan Ragonmu na Idin Ƙetarewa, wato, Almasihu. 8#Fit 13.7; M.Sh 16.3 Saboda haka, sai mu riƙa yin idinmu, ba da gurasa mai tsohon yisti ba, ba kuwa gauraye da yisti na ƙeta da na mugunta ba, sai dai da gurasa marar yisti ta sahihanci da ta gaskiya.
9Na rubuta muku a cikin wasiƙata, cewa kada ku yi cuɗanya da fasikai. 10Ko kusa, ba na nufin fasikai marasa bi, ko makwaɗaita, da mazambata, ko matsafa, don in haka ne, sai yă zama dole ku fita daga duniya. 11Sai dai na rubuta muku ne, don kada ku yi cuɗanya da duk wanda ake kira ɗan'uwa, mai bi, in yana fasikanci, ko makwaɗaici, ko matsafi, ko mai zage-zage, ko mashayi, ko mazambaci, kada ku ko ci abinci da irin waɗannan. 12#M.Sh 13.5; 17.7 Ina ruwana da hukunta waɗanda ba namu ba? Ba waɗanda suke a cikin Ikkilisiya za ku hukunta ba? 13Allah ne yake hukunta waɗanda ba namu ba. Ku kori mugun nan daga cikinku.

Currently Selected:

1Kor 5: HAU

Highlight

Copy

Compare

Share

None

Want to have your highlights saved across all your devices? Sign up or sign in