YouVersion Logo
Search Icon

1Kor 14

14
Harsuna da Annabci
1Ku nace wa ƙauna, ku kuma himmantu ga neman bayebaye na ruhu, tun ba ma na yin annabci ba. 2Duk wanda yake magana da wani harshe, ba da mutane yake magana ba, da Allah yake yi, ba kuwa wanda yake fahimtarsa, domin asirtattun al'amura yake ambato ta wurin Ruhu. 3Wanda kuwa yake yin annabci, mutane yake yi wa magana domin yă inganta su, ya ƙarfafa su, yă ta'azantar da su. 4Duk wanda yake magana da wani harshe, kansa yake ingantawa. Mai yin annabci kuwa, ikkilisiya yake ingantawa. 5To, ina so dukanku ku yi magana da waɗansu harsuna dabam, amma na fi so ku yi annabci. Wanda yake yin annabci, ya fi mai magana da waɗansu harsuna, sai ko in wani ya yi masa fassara, domin a inganta ikkilisiya.
6To, 'yan'uwa, in na zo muku ina magana da waɗansu harsuna, amfanin me zan yi muku in ban zo muku da wani bayani, ko ilimi, ko annabci, ko koyar da Maganar Allah ba? 7In abubuwan nan marasa rai, kamar su sarewa da molo, muryarsu ba ta fita sosai ba, yaya wani zai san abin da ake busawa ko kaɗawa? 8In ba a busa ƙaho sosai ba, wa zai yi shirin yaƙi? 9Haka ma yake a gare ku. In kun yi magana da wani harshe, wanda ba a fahimta ba, yaya wani zai san abin da ake faɗa? Kun yi magana a banza ke nan! 10Hakika akwai harsuna iri iri a duniya, ba kuwa wanda ba shi da ma'ana. 11In kuwa ba na jin harshen, sai in zama bare ga mai maganar, mai maganar kuma ya zama bare a gare ni. 12Haka ma yake a gare ku. Tun da yake kun ɗokanta da samun bayebaye na Ruhu, sai ku himmantu ku ba da ƙarfinku ga inganta ikkilisiya.
13Saboda haka duk mai magana da wani harshe, sai yă yi addu'a a yi masa baiwar fassara. 14In na yi addu'a da wani harshe, ruhuna ne yake addu'a, amma tunanina bai amfana kowa ba. 15To, ƙaƙa ke nan? Zan yi addu'a da ruhuna, zan kuma yi a game da tunanina. Zan yi waƙar yabon Allah da ruhuna, zan yi a game da tunanina. 16In ba haka ba, in ka gode wa Allah da ruhu kawai, ta yaya wanda yake jahili zai ce, “Amin,” a kan godiyar da kake yi, in bai san abin da kake faɗa ba? 17Ko da yake ka gode wa Allah sosai, ai, ɗan'uwanka bai ƙaru da kome ba. 18Na gode Allah ina magana da waɗansu harsuna fiye da ku duka. 19Duk da haka dai a taron ikkilisiya na gwammace in faɗi kalmomi biyar a game da tunanina, domin in karantar da waɗansu, da in faɗi kalmomi dubu goma da wani harshe.
20Ya ku 'yan'uwa, kada ku yi hankali irin na yara, sai dai a wajen mugunta, ku yi halin jarirai, amma a wajen hankali ku yi dattako. 21#Ish 28.11,12 A rubuce yake a cikin littattafai masu tsarki cewa, “Zan yi magana da jama'an nan ta wurin mutane masu baƙin harsuna, da kuma ta harshen baƙi, duk da haka kuwa ba za su saurare ni ba, in ji Ubangiji.” 22Wato, ashe, harsuna a kan alamu suke, ba ga masu ba da gaskiya ba, sai dai ga marasa ba da gaskiya. Annabci kuwa domin masu ba da gaskiya ne, ba don marasa ba da gaskiya ba. 23Saboda haka, in dukan ikkilisiya ta taru, kowa kuma yana magana da wani harshe dabam, waɗansu jahilai kuma ko marasa ba da gaskiya suka shigo, ashe, ba sai su ce kun ruɗe ba? 24In kuwa kowa yana yin annabci, wani kuma marar ba da gaskiya ko jahili ya shigo, sai maganar kowa ta ratsa shi, ya kamu a ransa ta maganar kowa, 25asiran zuciyarsa kuma su tonu. Ta haka sai ya fāɗi ya yi wa Allah sujada, yana cewa lalle Allah na cikinku.
A Yi Kome yadda Ya Dace, a Shirye
26To, ƙaƙa abin yake ne, 'yan'uwa? Duk sa'ad da kuka taru, wani yakan yi waƙar yabon Allah, wani kuma koyar da Maganar Allah, wani bayani, wani yin magana da wani harshe, wani kuma fassara. Sai dai a yi kome don ingantawa. 27In kuwa waɗansu za su yi magana da wani harshe, kada su fi mutum biyu, matuƙa uku, su ma kuwa bi da bi, wani kuma yă yi fassara. 28In kuwa ba mai fassara, sai kowannensu yă yi shiru a cikin taron Ikkilisiya, yă yi wa Allah magana a zuci. 29Masu yin annabci kuma, sai dai biyu ko uku su yi magana, saura kuwa su auna maganar. 30In kuwa an yi wa wani wanda yake zaune wani bayani, sai na farkon nan mai magana yă yi shiru. 31Dukanku kuna iya yin annabci da ɗaya ɗaya, har kowa yă koya, yă koma sami ƙarfafawa. 32Annabawa suna sarrafa ruhohinsu na annabci, 33domin Allah ba Allahn ruɗu ba ne, na salama ne.
Haka yake kuwa a duk ikilisyoyin tsarkaka. 34Sai mata su yi shiru a cikin taron ikkilisiya, don ba a ba su izinin yin magana ba, sai dai su bi, kamar dai yadda Attaura ma ta ce. 35In akwai wani abin da suke so su sani, to, sai su tambayi mazansu a gida, don abin kunya ne mace ta yi magana a cikin taron ikkilisiya. 36A kanku ne maganar Allah ta fara, ko kuwa a gare ku kaɗai ta isa?
37In wani yana zato shi annabi ne, ko kuwa mai wata baiwa ta ruhu, to, sai yă fahimta, abin nan da nake rubuto muku umarni ne na Ubangiji. 38In kuwa wani ya ƙi kula da wannan, shi ma sai a ƙi kula da shi. 39Saboda haka, 'yan'uwa, sai ku himmantu ga samun baiwar yin annabci, kada kuma ku hana yin magana da waɗansu harsuna. 40Sai dai a yi kome ta hanyar da ta dace, a shirye kuma.

Currently Selected:

1Kor 14: HAU

Highlight

Share

Copy

None

Want to have your highlights saved across all your devices? Sign up or sign in

YouVersion uses cookies to personalize your experience. By using our website, you accept our use of cookies as described in our Privacy Policy