YouVersion Logo
Search Icon

1Tar 6

6
Zuriyar Manyan Firistoci
1'Ya'yan Lawi, maza, su ne Gershon, da Kohat, da Merari.
2'Ya'yan Kohat, maza, su ne Amram, da Izhara, da Hebron, da Uzziyel.
3'Ya'yan Amram kuwa, su ne Haruna, da Musa, da Maryamu.
'Ya'yan Haruna, maza, su ne Nadab, da Abihu, da Ele'azara, da Itamar.
4Zuriyar Ele'azara daga tsara zuwa tsara, su ne Finehas, da Abishuwa, 5da Bukki, da Uzzi, 6da Zarahiya, da Merayot, 7da Amariya, da Ahitub, 8da Zadok, da Ahimawaz, 9da Azariya, da Yohenan, 10da Azariya wanda ya yi hidimar firist a Haikalin da Sulemanu ya gina a Urushalima. 11Ga Amariya kuma da Ahitub, 12da Zakok, da Meshullam, 13da Hilkiya, da Azariya, 14da Seraiya, da Yehozadak. 15Sarki Nebukadnezzar ya kama Yehozadak, ya tafi da shi tare da sauran jama'a zuwa zaman talala, sa'ad da Ubangiji ya ba da su a hannun Nebukadnezzar don su yi zaman talala.
Sauran Zuriyar Lawi
16 # Fit 6.16-19 'Ya'yan Lawi, maza, su ne Gershon, da Kohat, da Merari. 17Waɗannan su ne sunayen 'ya'yan Gershon, maza, Libni da Shimai. 18'Ya'yan Kohat, maza, su ne Amram, da Izhara, da Hebron, da Uzziyel. 19'Ya'yan Merari, maza kuwa, su ne Mali da Mushi. Waɗannan su ne iyalan Lawiyawa bisa ga gidajen kakanninsu.
20Zuriyar Gershon bi da bi, su ne Libni, da Yahat, da Zimma, 21da Yowa, da Iddo, da Zera, da Yewaterai.
22Zuriyar Kohat bi da bi, su ne Izhara, da Kora, da Assir, 23da Elkana, da Ebiyasaf, da Assir, 24da Tahat, da Uriyel, da Azariya, da Shawul.
25'Ya'yan Elkana, maza, su ne Amasai da Ahimot. 26Zuriyar Ahimot bi da bi, su ne Elkana, da Zofai, da Nahat, 27da Eliyab, da Yeroham, da Elkana.
28'Ya'yan Sama'ila, maza, su ne Yowel ɗan farinsa, na biyun shi ne Abaija.
29Zuriyar Merari bi da bi, su ne Mali, da Libni, da Shimai, da Uzza, 30da Shimeya, da Haggiya, da Asaya.
Masu Bushe-bushe a Haikali da Dawuda Ya Zaɓa
31Waɗannan su ne waɗanda Dawuda ya sa su su zama mawaƙa a Haikalin Ubangiji, sa'ad da aka kawo akwatin alkawari a cikin Haikalin. 32Suka yi ta raira waƙoƙi a gaban wurin zama na alfarwa ta taruwa tun kafin Sulemanu ya gina Haikalin Ubangiji a Urushalima. Suka yi hidima bisa ga matsayinsu ta yadda aka tsara. 33Waɗannan su ne waɗanda suka yi ta raira waƙoƙin, su da 'ya'yansu maza.
Daga iyalin Kohat, Heman shi ne shugaban ƙungiyar farko ta mawaƙa, shi ɗan Yowel ne, ɗan Sama'ila, 34ɗan Elkana, ɗan Yeroham, ɗan Eliyab, ɗan Mahat, 35ɗan Zafai, ɗan Elkana, ɗan Mahat, ɗan Amasai, 36ɗan Elkana, ɗan Shawul, ɗan Azariya, ɗan Uriyel, 37ɗan Tahat, ɗan Assir, ɗan Ebiyasaf, ɗan Kora, 38ɗan Izhara, ɗan Kohat, ɗan Lawi, ɗan Isra'ila.
39Asaf kuma shi ne shugaban ƙungiyar mawaƙa ta biyu. Shi ɗan Berikiya ne, ɗan Shimeya, 40ɗan Maikel, ɗan Ba'aseya, ɗan Malkiya, 41ɗan Yewaterai, ɗan Zera, ɗan Iddo, 42ɗan Yowa, ɗan Zimma, ɗan Shimai, 43ɗan Yahat, ɗan Gershon, ɗan Lawi.
44Etan na zuriyar Merari, shi ne shugaban ƙungiyar mawaƙa ta uku, asalinsa shi ɗan Kishi ne, ɗan Abdi, ɗan Malluki, 45ɗan Hashabiya, ɗan Amaziya, ɗan Hilkiya, 46ɗan Amzi, ɗan Bani, ɗan Shemer, 47ɗan Mali, ɗan Mushi, ɗan Merari, ɗan Lawi.
48Aka sa 'yan'uwansu, Lawiyawa, su yi dukan hidimomi a cikin Haikalin Ubangiji.
Zuriyar Haruna
49Amma Haruna da 'ya'yansa maza suka miƙa hadayu a kan bagaden hadaya ta ƙonawa, da kan bagaden ƙona turare, domin dukan aikin Wuri Mafi Tsarki, da kuma yin kafara domin Isra'ila bisa ga dukan abin da Musa, bawan Allah, ya umarta. 50Waɗannan su ne zuriyar Haruna, maza, bi da bi, Ele'azara, da Finehas, da Abishuwa, 51da Bukki, da Uzzi, da Zerahiya, 52da Merayot, da Amariya, da Ahitub, 53da Zadok da Ahimawaz.
Inda Zuriyar Haruna Suka Zauna
(Josh 21.1-42)
54Ga wuraren da aka ba zuriyar Haruna, na iyalin Kohat. Sun karɓi rabo na farko a ƙasar. 55Rabonsu ya haɗu da Hebron ta yankin ƙasar Yahuza, da makiyayar da suke kewaye da ita. 56Amma an ba Kalibu ɗan Yefunne saurukan birnin, tare da ƙauyukansa. 57Suka ba 'ya'yan Haruna, maza, biranen mafaka, wato Hebron, da Libna tare da makiyayarta, da Yattir, da Eshtemowa tare da makiyayarta, 58da Holon tare da makiyayarta, da Debir tare da makiyayarta, 59da Ayin tare da makiyayarta, da Bet-shemesh tare da makiyayarta. 60Daga kabilar Biliyaminu aka ba su Geba tare da makiyayarta, da Allemet tare da makiyayarta, da Anatot tare da makiyayarta. Dukan biranen iyalansu guda goma sha uku ne.
Inda Sauran Lawiyawa Suka Zauna
61Aka ba sauran 'ya'yan Kohat, maza, garuruwa goma daga na rabin kabilar Manassa, ta hanyar kuri'a. 62Aka kuma ba Gershonawa bisa ga iyalansu, birane goma sha uku daga na kabilar Issaka, da na kabilar Ashiru, da na kabilar Naftali, da na kabilar Manassa da take nan a Bashan. 63Haka kuma aka ba 'ya'yan Merari, maza, bisa ga iyalansu, garuruwa goma sha biyu daga na kabilar Ra'ubainu, da na kabilar Gad, da na kabilar Zabaluna. 64Haka fa, jama'ar Isra'ila suka ba Lawiyawa garuruwa duk da makiyayansu. 65Daga na kabilar Yahuza, da na kabilar Saminu, da na kabilar Biliyaminu kuma aka ba da waɗannan garuruwan da aka ambaci sunayensu ta hanyar kuri'a.
66Waɗansu daga cikin iyalan 'ya'yan Kohat, maza, sun sami garuruwa na yankinsu daga cikin kabilar Ifraimu. 67Sai suka ba su waɗannan biranen mafaka, wato Shekem a ƙasar tudu ta Ifraimu duk da makiyayarta, da Gezer tare da makiyayarta, 68da Yokmeyam duk da makiyayarta, da Bet-horon duk da makiyayarta, 69da Ayalon duk da makiyayarta, da Gatrimmon duk da makiyayarta. 70Daga cikin rabin kabilar Manassa kuma an ba su Ta'anak duk da makiyayarta, da Bileyam duk da makiyayarta. An ba da waɗannan ga sauran iyalai na 'ya'yan Kohat, maza.
71Daga na rabin kabilar Manassa na gabas, an ba 'ya'yan Gershon, maza, Golan ta Bashan tare da makiyayarta, da Ashtarot duk da makiyayarta.
72Daga na kabilar Issaka kuma an ba su Kishiyon duk da makiyayarta, da Daberat duk da makiyayarta, 73da Ramot duk da makiyayarta, da Enganin duk da makiyayarta.
74Daga cikin kabilar Ashiru kuma an ba da Mishal duk da makiyayarta, da Abdon duk da makiyayarta, 75da Helkat duk da makiyayarta, da Rehob duk da makiyayarta.
76Daga na kabilar Naftali kuma an ba da Kedesh ta Galili duk da makiyayarta, da Hammon duk da makiyayarta, da Kartan duk da makiyayarta.
77Daga na kabilar Zabaluna, an ba sauran Lawiyawa, wato 'ya'yan Merari, maza, Rimmon duk da makiyayarta, da Tabor duk da makiyayarta.
78Daga na kabilar Ra'ubainu a hayin Urdun a Yariko, wato gabashin Urdun, an ba da Bezer ta cikin jeji duk da makiyayarta, da Yahaza duk da makiyayarta, 79da Kedemot duk da makiyayarta, da Mefayat duk da makiyayarta.
80Daga na kabilar Gad kuma an ba da Ramot ta Gileyad duk da makiyayarta, da Mahanayim duk da makiyayarta, 81da Heshbon duk da makiyayarta, da Yazar duk da makiyayarta.

Currently Selected:

1Tar 6: HAU

Highlight

Share

Compare

Copy

None

Want to have your highlights saved across all your devices? Sign up or sign in