1Tar 5
5
Zuriyar Ra'ubainu
1 #
Far 35.22; 49.3,4 Ra'ubainu shi ne ɗan farin Isra'ila, amma saboda ya ƙazantar da gadon mahaifinsa aka ba 'ya'yan Yusufu, maza, ɗan Isra'ila, gādonsa na ɗan fari. Don haka ba a lasafta shi a kan matsayin ɗan fari ba. 2#Far 49.8-10 Ko da yake Yahuza ya rinjayi 'yan'uwansa, har daga gare shi aka sami shugaba, duk da haka matsayin ɗan farin na Yusufu ne. 3'Ya'yan Ra'ubainu, maza, wato ɗan farin Isra'ila, su ne Hanok, da Fallu, da Hesruna, da Karmi.
4 #
2Sar 15.29
'Ya'yan Yowel, maza, su ne Shemaiya, da Gog, da Shimai, 5da Mika, da Rewaiya, da Ba'al, 6da Biyera wanda Tiglat-filesar Sarkin Assuriya ya kai bauta. Shi ne shugaban Ra'ubainawa.
7Danginsa bisa ga iyalansu da asalinsu a zamaninsu, su ne sarki Yehiyel, da Zakariya, 8da Bela ɗan Azaz, wato jīkan Shema, ɗan Yowel, wanda ya zauna a Arower har zuwa Nebo da Ba'al-meyon. 9Ya kuma zauna wajen gabas, har zuwa goshin jejin da yake wajen Kogin Yufiretis, saboda shanunsu sun ƙaru a ƙasar Gileyad.
10Zuriyar Ra'ubainu suka yi yaƙi da Hagarawa a kwanakin Saul. Suka ci Hagarawa, saboda haka suka zauna a ƙasar da take gabashin Gileyad.
Zuriyar Gad
11'Ya'yan Gad, maza, suka zauna a ƙasar Bashan, daura da Ra'ubainawa har zuwa Salka. 12Yowel ne sarki, Shafam kuwa shi ne na biyun, da Yanai, da Shafat, su ne tushen Bashan. 13Danginsu bisa ga gidajen kakanninsu, su ne Maikel, da Meshullam, da Sheba, da Yorai, da Jakan, da Ziya, da Eber, su bakwai ke nan. 14Waɗannan su ne 'ya'ya maza na Abihail ɗan Huri. Ga yadda kakanninsu suke, wato Abihail, ɗan Huri ɗan Yarowa, ɗan Gileyad, ɗan Maikel, ɗan Yeshishai, ɗan Yado, ɗan Buz. 15Ahi ɗan Abdiyel, wato jīkan Guni, shi ne shugaban gidan kakanninsu. 16Suka zauna a Gileyad, da Bashan, da garuruwanta, da dukan iyakar makiyayar Sharon. 17(An rubuta waɗannan duka bisa ga asalinsu a zamanin Yotam, Sarkin Yahuza, da Yerobowam Sarkin Isra'ila.)
Tarihin Kabilai Biyu da Rabi
18'Ya'yan Ra'ubainu, maza, da Gadawa, da rabin kabilar Manassa suna da jarumawa masu riƙon garkuwa da takobi, masu harbi kuma da baka. Gwanayen yaƙi ne, su dubu arba'in da huɗu, da ɗari bakwai da sittin ne (44,760). 19Suka yi yaƙi da Hagarawa, da Yetur, da Nafish, da Nodab. 20Aka taimake su yin yaƙi da abokan gābansu, sai aka ba da Hagarawa da duk waɗanda suke tare da su a hannunsu, saboda suka yi roƙo ga Allah a cikin yaƙin, Allah kuwa ya amsa musu roƙonsu saboda sun dogara gare shi. 21Sai suka kwashe dabbobinsu, raƙuma dubu hamsin (50,000), da tumaki dubu ɗari biyu da dubu hamsin (250,000), da jakuna dubu biyu (2,000), da kuma mutane dubu ɗari (100,000). 22Aka karkashe mutane da yawa, domin yaƙin na Allah ne. Sai suka gāje wurin zamansu, har lokacin da aka kai su bauta.
23Mutanen rabin kabilar Manassa suna da yawa, sun zauna a ƙasar, daga Bashan har zuwa Ba'al-harmon, da Senir, da Dutsen Harmon. 24Waɗannan su ne shugabannin gidajen kakanninsu, Efer, da Ishi, da Eliyel, da Azriyel, da Irmiya, da Hodawiya, da Yadiyel. Su jarumawa ne na gaske, masu suna, su ne shugabannin gidajen kakanninsu.
25Amma mutanen suka yi rashin gaskiya ga Allah na kakanninsu, suka bi gumakan mutanen ƙasar, waɗanda Allah ya hallaka a gabansu. 26#2Sar 15.19; 2Sar 15.29; 2Sar 17.6 Don haka Allah na Isra'ila ya zuga Ful, Sarkin Assuriya, wato Tiglat-filesar, ya zo ya kwashe su, ya kai su bauta, wato su Ra'ubainawa, da Gadawa, da rabin kabilar Manassa. Ya kai su Hala, da Habor, da Hara, har zuwa kogin Gozan, can suke har yau.
Currently Selected:
1Tar 5: HAU
Highlight
Share
Compare
Copy
Want to have your highlights saved across all your devices? Sign up or sign in
@Bible Society of Nigeria 1979