Irmiya 14
14
Fari, yunwa da takobi
1Ga maganar Ubangiji da ta zo wa Irmiya game da fări cewa,
2“Yahuda tana makoki
biranenta suna fama;
suna kuka saboda ƙasar,
kuka kuma tana tasowa daga Urushalima.
3Manyan mutane suna aika bayinsu su ɗebo ruwa
a maɓulɓulai amma babu ruwa.
Suka dawo da tulunansu haka nan;
da kunya da kuma ƙasƙanci, da kawunansu a rufe.
4Ƙasa ta tsattsage
saboda babu ruwan sama a ƙasar;
manoma sun sha kunya
suka kuma rufe kawunansu.
5Har barewa a kurmi ma
ta gudu ta bar ’ya’yan da ta haihu sababbi
saboda babu ciyawa.
6Jakan jeji suna tsaye a kan tuddai
suna haki kamar diloli;
idanunsu sun kāsa gani
saboda rashin makiyaya.”
7Ko da yake zunubanmu suna ba da shaida a kanmu,
Ya Ubangiji, ka yi wani abu saboda sunanka.
Gama jan bayanmu ya yi yawa;
mun yi maka zunubi.
8Ya kai, Sa Zuciyar Isra’ila,
Mai Cetonsa a lokutan wahala,
me ya sa kake yi kamar baƙo a ƙasar,
kamar matafiyi wanda yake shirya wuri don yă kwana gari ya waye ya wuce?
9Me ya sa kake yi kamar mutumin da aka far masa kwasam ba zato,
kamar jarumi marar ƙarfin ceto?
Kana a cikinmu, ya Ubangiji,
da sunanka ake kiranmu;
kada ka yashe mu!
10Ga abin da Ubangiji ya ce game da wannan mutane,
“Suna son yawace-yawace ƙwarai;
ba sa hana ƙafafunsu yawo.
Saboda haka Ubangiji bai yarda da su ba;
yanzu zai tuna da muguntarsu
zai kuma hukunta su saboda zunubansu.”
11Sa’an nan Ubangiji ya ce mini, “Kada ka yi addu’a domin zaman lafiyar mutanen nan. 12Ko da yake suna azumi, ba zan saurari kukansu ba, ko da yake suna miƙa hadayun ƙonawa da hadayun gari, ba zan yarda da su ba. A maimako zan hallaka su da takobi, yunwa da annoba.”
13Amma na ce, “A, Ubangiji Mai Iko Duka, annabawa sun riƙa ce musu, ‘Ba za ku ga takobi ko ku yi fama da yunwa ba. A maimako, zan ba ku madawwamiyar salama.’ ”
14Sai Ubangiji ya ce mini, “Annabawa suna ta annabcin ƙarya da sunana. Ban aike su ba, ban kuma naɗa su ba, ban yi musu magana ba. Suna muku annabci wahayin ƙarya, suna muku duba marar amfani, suna bautar gumaka suna kuma bayyana tunanin kansu ne. 15Saboda haka, ga abin da Ubangiji ya ce game da annabawan da suke annabci da sunana. Ban aike su ba, duk da haka suna cewa, ‘Babu takobi ko yunwar da zai taɓa wannan ƙasa.’ Waɗannan annabawa takobi da yunwa za su hallaka su. 16Mutanen da suke musu annabcin kuwa za a kore su zuwa titunan Urushalima saboda yunwa da kuma takobi. Babu wanda zai binne su, ko ya binne matansu, ko ’ya’yansu maza da mata. Zan aukar musu da masifar da ya dace da su.
17“Ka yi musu wannan magana,
“ ‘Bari idanuna su yi ta zub da hawaye
dare da rana kada su daina;
saboda ’yata budurwa, mutanena,
sun sha wahalar babban rauni,
an yi musu bugu mai ragargazawa.
18In na shiga cikin ƙasar,
na ga waɗanda takobi ya kashe;
in na shiga cikin birni,
na ga waɗanda suke fama da yunwa.
Da Annabi da firist duk
sun tafi ƙasar da ba su sani ba.’ ”
19Ka ƙi Yahuda ɗungum ke nan?
Kana ƙyamar Sihiyona ne?
Me ya sa ka buge mu
don kada mu warke?
Mun sa zuciya ga salama
babu abin alherin da ya zo,
mun sa rai ga lokacin warkarwa
amma sai ga razana.
20Ya Ubangiji, mun gane da muguntarmu
da kuma laifin kakanninmu;
tabbatacce mun yi maka zunubi.
21Saboda sunanka kada ka ƙi mu;
kada ka ƙasƙantar da kursiyoyinka mai ɗaukaka.
Ka tuna da alkawarinka da mu
kada ka tā da shi.
22Akwai wani daga cikin gumaka marasa amfani na al’ummai da ya kawo ruwan sama?
Sararin sama kansu sukan yi yayyafi?
A’a, kai ne, ya Ubangiji Allahnmu.
Saboda haka sa zuciyarmu tana a kanka,
gama kai ne kake yi wannan duka.
Currently Selected:
Irmiya 14: SRK
Highlight
Copy
Compare
Share
Want to have your highlights saved across all your devices? Sign up or sign in
Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™
Neman Rubutaccen Izini © 2009, 2020 ta hannun Biblica, Inc.
An yi amfani da izinin Biblica, Inc. Neman izinin nan ya game dukan Duniya.
Hausa Contemporary Bible™
Copyright © 2009, 2020 by Biblica, Inc.
Used with permission. All rights reserved worldwide.