Irmiya 13
13
Abin ɗamara na lilin
1Ga abin da Ubangiji ya faɗa mini, “Tafi ka sayo abin ɗamara na lilin ka sha ɗamara da shi, amma kada ka bari yă taɓa ruwa.” 2Saboda haka na sayo abin ɗamara, yadda Ubangiji ya umarce ni, na kuwa sha ɗamara da shi.
3Sai maganar Ubangiji ta zo mini sau na biyu cewa, 4“Ka ɗauki abin ɗamara da ka sayo, wanda ka ɗaura, ka tafi yanzu zuwa Fera#13.4 Ko kuwa mai yiwuwa Yuferites; haka ma a ayoyi 5-7 ka ɓoye shi a cikin kogon dutse.” 5Saboda haka na tafi na ɓoye shi a Fera, yadda Ubangiji ya ce mini.
6Bayan ’yan kwanaki sai Ubangiji ya ce mini, “Tafi yanzu zuwa Fera ka ɗauko abin ɗamara da na ce maka ka ɓoye a can.” 7Sai na tafi Fera da haka na ɗauko abin ɗamara daga wurin da na ɓoye shi, amma abin ɗamara yanzu ya lalace ya zama ba shi da amfani sam.
8Sai maganar Ubangiji ta zo mini cewa, 9“Ga abin da Ubangiji yana cewa, ‘Haka zan lalatar da alfarmar Yahuda da yawan alfarmar Urushalima. 10Waɗannan mugayen mutane, waɗanda suka ƙi saurari maganata, waɗanda suka biye wa taurin zuciyarsu suka bi waɗansu alloli don su bauta su kuma yi musu sujada, za su zama kamar wannan abin ɗamara gaba ɗaya marasa amfani! 11Gama kamar yadda abin ɗamara kan kame gindin mutum tam, haka zan daure dukan gidan Isra’ila da dukan gidan Yahuda gare ni,’ in ji Ubangiji, ‘domin su zama jama’a, da suna, da yabo, da daraja a gare ni, amma sun ƙi ji.’
Salkunan ruwan inabi
12“Faɗa musu cewa, ‘Ga abin da Ubangiji, Allah na Isra’ila, yana cewa a cika kowace salkar ruwan inabi da ruwan inabi.’ In kuwa suka ce maka, ‘Ba mu san cewa ya kamata a cika kowace salkar ruwan inabi da ruwan inabi ba?’ 13Sai ka ce musu, ‘Ga abin da Ubangiji yana cewa, zan cika dukan waɗanda suke zama a ƙasar da buguwa, har ma da sarakunan da suke zama a kursiyin Dawuda, firistoci, annabawa da dukan waɗanda suke zaune a Urushalima. 14Zan fyaɗe su a kan juna, iyaye da ’ya’yansu maza, in ji Ubangiji. Tausayi ko jinƙai, ko juyayi ba zai hana ni hallaka su ba.’ ”
Barazanar kwashewa zuwa zaman bauta
15Ku ji ku kuma saurara,
kada ku yi girman kai,
gama Ubangiji ya yi magana.
16Ku ɗaukaka Ubangiji Allahnku
kafin ya kawo duhu,
kafin ƙafafunku su yi tuntuɓe
a kan tuddai masu duhu.
Za ku sa zuciya ganin haske
amma zai mai da shi duhu mai kauri
ya kuma canja shi zuwa duhu baƙi ƙirin.
17Amma in ba ku saurara ba,
zan yi kuka a ɓoye
saboda girmankanku;
idanuna za su yi kuka mai zafi,
suna zub da hawaye ƙwarai,
domin zan kwashe garken Ubangiji zuwa zaman bauta.
18Ka faɗa wa sarki da kuma mahaifiyar sarauniya cewa,
“Ku sauko daga kursiyinku,
gama rawaninku na ɗaukaka
za su fāɗi daga kawunanku.”
19Za a kulle biranen da suke a Negeb,
kuma babu wanda zai buɗe su.
Za a kwashe dukan Yahuda zuwa zaman bauta,
za a kwashe su tas.
20Ku tā da idanunku ku ga
waɗanda suke zuwa daga arewa.
Ina garken da aka ba ku
tumakin da kuke taƙama a kai?
21Me za ku ce sa’ad da Ubangiji ya naɗa muku
waɗanda ku kanku kuka koya musu a matsayi abokai na musamman?
Ashe, azaba ba za tă auko muku
kamar na mace mai naƙuda ba?
22In kuma kuka tambaye kanku
“Me ya sa wannan ya faru da mu?”
Wannan kuwa saboda yawan zunubanku ne
ya sa fatarinku ya yage
aka kuma wahalshe jikinku.
23Mutumin Habasha#13.23 Da Ibraniyanci Mutumin Kush (mai yiwuwa mutum daga yankin Bisa na Nilu). zai iya canja launin fatar jikinsa
ko damisa ta canja dabbare dabbarenta?
Ba za ku iya yin alheri
ku da kuka saba da yin mugunta ba.
24“Zan watsar da ku kamar yayin
da iskar hamada take hurawa.
25Rabonku ne wannan,
sashen da na auka muku,”
in ji Ubangiji
“domin kun manta da ni
kuka kuma dogara ga allolin ƙarya.
26Zan kware fatarinku sama ya rufe fuskarku
don a iya ga tsiraicinku
27zinace zinacenku da haniniya kamar dawakai,
karuwancinku na bankunya!
Na ga ayyukanku na banƙyama
a kan tuddai da kuma a filaye.
Kaitonki, ya Urushalima!
Har yaushe za ki ci gaba da rashin tsarki?”
Currently Selected:
Irmiya 13: SRK
Highlight
Copy
Compare
Share
Want to have your highlights saved across all your devices? Sign up or sign in
Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™
Neman Rubutaccen Izini © 2009, 2020 ta hannun Biblica, Inc.
An yi amfani da izinin Biblica, Inc. Neman izinin nan ya game dukan Duniya.
Hausa Contemporary Bible™
Copyright © 2009, 2020 by Biblica, Inc.
Used with permission. All rights reserved worldwide.