1
W.Yah 20:15
Littafi Mai Tsarki
HAU
Duk wanda ba a sami sunansa a rubuce a Littafin Rai ba, sai a jefa shi a tafkin nan na wuta.
Compare
Explore W.Yah 20:15
2
W.Yah 20:12
Sai na ga matattu manya da yara, a tsaitsaye a gaban kursiyin, aka kuma buɗe littattafai. Sai kuma aka buɗe wani littafi, wanda yake shi ne Littafin Rai. Aka kuwa yi wa matattu shari'a bisa ga abin da yake a rubuce a cikin littattafan, gwargwadon aikin da suka yi.
Explore W.Yah 20:12
3
W.Yah 20:13-14
Sai teku ta ba da matattun da suke a cikinta, mutuwa da Hades kuma sun ba da matattun da suke a gare su, aka kuwa yi wa kowa shari'a gwargwadon aikin da ya yi. Sa'an nan aka jefa mutuwa da Hades a tafkin nan na wuta. Wannan ita ce mutuwa ta biyu, wato, tafkin wuta.
Explore W.Yah 20:13-14
4
W.Yah 20:11
Sa'an nan na ga wani babban kursiyi fari, da wanda yake a zaune a kai, sai sama da ƙasa suka guje wa Zatinsa, suka ɓace.
Explore W.Yah 20:11
5
W.Yah 20:7-8
Bayan shekaran nan dubu sun ƙare, sai a saki Shaiɗan daga ɗaurinsa, ya kuma fito ya yaudari al'ummai waɗanda suke kusurwoyin nan huɗu na duniya, wato, Gog da Magog, ya tattara su saboda yaƙi, yawansu kamar yashin teku.
Explore W.Yah 20:7-8